← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 128

Sashe 78

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na dada kwantar da kaina a kirjinsa ina wasa da gashin kirjansa nace"yaya idan ina tare da kai mantawa nake da dukkan hayaniyan duniya .kai din na musamman ne.

Ya dago fuskata yana murmushi snn yayi kissing din bakina yace " thank you dear nd kema kinsan your so so so special sonki kullum dada mamaye koina na jikina yake bana iya zama na second daya ni kadai ba tare da na tuna ki ba babyna i love you!

Na dada kwantar da kaina ina murmushi nace " i love you too ......

Da sauri ya soma rikita tunanina da salon soyyayyarsa mai sanyawa zuciya nitsuwa gaskia ya salman daban ne a cikin maza zaiyi wuya mace ta sanshi ta iya rabuwa dashi .don haka nake kara zagewa wurin ganin na toshe duk wata kofa a zuciyarsa kar wata ta shigo don a yadda nakeji a jikina kamar bazan iya sharing dinsa da kowacce mace ba.

Da safe kasancewar ranar sunday ce bacci mukayi sosai har sha biyu muka yi breakfast bayan munyi wanka shikam tuni ya fita yace sai bayan sallar la,asar zai dawo.

Nace" to a dawo lfy.

Bayan fitarsa ne na koma daki na duba wayata wanda naji lokacinda massage ya shiga.

Ina dubawa na fara karantawa kamar haka.

Queen! Pls ina rokonki ki amsa gayyatana ko sau daya ne a guest house dina address dina shine na baki ranar sai na ganki!!!!!!!

Shiru nayi ina maimaita sakonsa a zuciyata mamaki da tsorone ya rufeni a lokaci guda to meye ahmad yake nufi da in amsa gayyatarsa.

Daukar num dinsa nayi da sauri na kirashi ba jimawa ya dauka hade da fadin"queen......

Na katseshi da fadin" Ahmad don Allah don Annabi ka rabu dani na fada ma nayi aure me kk so dani ne?

Cikin wata irin murya yace" queen wlh nima ba,ason raina nake damunki ba na kasa hkr dakene wlh ganinki ranar ya matukar tayar min da hankali sai yanzu na gane saken da nayi a baya pls queen ki daure mu hadu a guest house dina ko sau daya ne nayi miki alkawarin ba wanda zai sani.kuma shikenan zan rabu dake.

Hawayene ya zubo min nace" ahmad ashe har yanzu baka shiryu ba kasan abinda kk shirin cewa mu aikata kuwa ?to nikam ba dani ba kaje can ka nemi shashasha yar iska irinka nikam bazan iya cin amanan aurena ba kuma pls daga yau ina maka gargadi da babbar murya kar ka sake nemana a rayuwa in ba haka ba zan dauki mummunan mataki......

Ya katseni da fadin" queen koma me zaki fada ki fada rabuwa dake bazan iya ba kawai.na baki one week kiyi tunani zan tuntubeki .ba wani abu bane kawai haduwa zamuyi sau daya tak na miki alkawari daga nan bazan kuma nemanki ba ......

Tsabar rakaici katse wayar nayi zuciyata cike da nadaman meyasa na kirashi .kuma nayi alkawarin bazan kuma sauraran shirmensa ba sai dai ya kari maitarsa ya rabu dani !!!!!!

Hauly ce🥰👍🏻
[10/9, 10:36 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

*HAR* *ILA* *YAU* *KUMA* *BAN* *MANTA* *DA* *KU* *BA* ❤

_Masoyana_ _na_ _group_ _din_ *BASMAH* ' *YAR* *LELE* _wnn_ _shafin_ _nakune_ _Allah_ _ya_ _bar_ _zumunci_ _nagode_ _sosai_ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡71

***********Tun daga ranar ban kuma biyo wa ta kan Ahmad ba naci gaba da harkokina.

Ranar wata monday na fito daga wurin aiki sai gashi nan saida gabana ya fadi.

Daure fuskata nayi tamkar ban taba sanin meye dariya ba na wuce da sauri zan shige motata shima din cikin hanzari yasha gabana.

Cike da mamaki nace" Ahmad anya kanka daya kuwa ? Kasan me kk yi kuwa?

Cikin sanyin murya yace"my queen pls ki saurareni dan Allah wlh ko kadan bana son in cutar dake amma......

Na katseshi da fadin " bakada hankali Ahmad Allah wadarai da yawan shekarunda baida amfani wlh gara min rayuwarka ta baya da baka cika shekara 40 dinba.inde haka zaka zama.

Murmushi yayi yace Queen karkiga laifina a shekarun baya ashe shirme nakeyi da nike cewa in na kai shekara 40 zan bar wasu abubuwan dan a ganina zan manyata ne sosai amma kalli dubeni fa sai ma kara jin kaina nake anan na fahimci cewa yanzu ne nake dai dai da cin zamanina.

Tsaki naja hade da fadin " Allah wadaranka wlh ni ka ban hanya na wuce .in yaso kaje can kaci gaba da shashancinka rayuwarkace ai ba tawa ba .

Ina kokarin ratse shi na wuce naji caraf ya rike min hannu .

Na zaro ido cike da tsoro na fara kokarin kwatar hannuna ina waige waige nace"wlh idan baka sakeni ba ihu zan maka in tara ma mutane.

Murmushi yayi ya ce" bani minti daya kamin kiyi ihun.

Nidai sai kokarin kwatar hannuna nake ina don Allah ka sakeni

Wayarsa ya ciro ya bude hade nuna min yace" duba nan kiga.

Na kai kallona ga wayar ai saida gabana yayi mugun faduwa har jakar hannuna ya fadi ganin irin hotunan da mukayi ta dauka dashi a wurin clubs da gidanshi wani muna rumgume da juna wani ma ina kissing dinshi ga watsu arnan kaya da na saka wanda dashi da babu du daya.

Haka yayita nuna minsu yana murmushi snn daga baya yace" kingani ko to akwai vedios ma idan kk bani hadin kai da hannuna zan baki ki goge idan kuma kk ki yanzun nan zan turawa salman snn yanxu haka in zaki duba can bangaren zaki ga ana daukar mu hoto zan sa a wanke in turawa salman har gida.

Ya saki hannuna hade da sakin murmushin yaudara yace" gobe ina jiranki a gidana da yamma in kina so asirinki ya rufu.

Jin ya saki hannuna yasa da sauri na juya yace " ungo jakarki.

Fizgewa nayi na shige motata da sauri na tashi motar Allah ne dai ya kaini gida lfy.

Gabadaya ranar na rasa mai yake man dadi a rayuwar duniya

Ya salman ma har ya fahimci ina cikin damuwa yayita tambayana nace masa babu stress ne ya min yawa .Allah sarki yayana kusan kwana mukayi yana min tausa.da kyar na samu na lallabashi yayi bacci dan haka na samu damar tashi na dhiga kai komo a dakin ina tunani mafita!

A karshe dai yanke shawara nayi bazanje ba sai dai komai ma yafaru.

Washe gari kasancewar ranar sunday ce muna gida ni da yaya bamu je koina ba muna manne a daki muna ta soyewarmu tuni na manta da batun wani Ahamad.

Na dauka ko zai sake turon sako ko ya kiran sai naji shiru ina ta zaman jiran mai zai faru amma har gari ya waye banji komai ba don haka sai naji hankalina ya dan fara kwanciya.

Ya salman ya rigani fita yau don sammako yayi yace min zasuje maiduguri amma may be bazasu kwana ba.nai mishi Allah ya kiyaye hanya.duk naji banson tfyr tasa don gabadaya maiduguri babu zaman lfy sai dai mu tayasu da addua.snn ceto rayukan mutane wajibi ne akansu sojoji koda zasu rasa nasu ran don haka adduace tawa domin tun ina daga hankalina da tfy tfyn ya salman har na saba.

Nima na tafi aiki a motata.ina ta tunani ta inda Ahmad zai bullo min sai addua nike a zuciyata.

Da yamma na fito da niyyar dawowa gida har nasa key zan bude motata kawai sai ji nayi kamar daga sama an fizge jakata da sauri na juya hade da fadin wayyo Allah jakata an kwace!

Kasancewar ba kowa a wurin haka inaji ina ganin wanda ya fizgen jaka ya gudu dashi.

Sa,a na daya wayata da mukullin motata na hannuna abinda ke cikin jakan Atm dinane sai dan canjina da sauran tarkace.......

Hankalina ya tashi kwarai ba yanda na iya haka na wuce gida cikin bakin ciki.ya salim naje na fadawa don ya salman kam tunda ya isa maiduguri daya kirani shikenan yace min ba lallsine in sameshi a waya a kai akai ba don haka sai dai sun dawo kawai.

Kamar da wasa ya salman saida suka shafe 2weeks snn suka dawo gaskia sunsha wuya suma yana bani labarin maiduguri ina kuka tsabar tausayi.

Ganin hankalina ya tashi sosai yasa ya shiga rarrashina yana cewa amma yanxu komai ya lafa Alhamdulillah ki daina damuwa baby su kuma haka tasu kaddarar yazo.

Nace " hakane Allah ya kawo musu agaji .

Yace amin ina son ranar sunday muje abuja nayi missing din muneer wlh.

Murmushi nace "to Allah ya kaimu dazu ma munyi waya da ruman ta tambayeni yaushe zaka dawo ashe kuna hanya.

Yace" baby 2 weeks dinnan kamar shekara biyu naji ina ta missing dinki.

Nayi murmushi nace"nima wlh yaya haka da kyar nike bacci wani lokacin barin yan matsn nan nake a dakina in tafi dakinka in kwana wlh da kyar nake samin bacci yayana amma yau hankalina ya kwanta da naga ka dawo lfy.

Rumgumeni yayi sosai hade sumbatar goshina yace"nima naji dadi da na sameki cikin koshin lfy baby hope ba wanda ya bata miki rai.

Dan dariya nayi nace"wlh ba kowa.

Kusan raba dare mukayi muna hira snn daaga bisani muka yi bacci.

Washe gari kuwa har na tafi yaya na ramuwar baccin gajia.don haka kyaleshi kawai nayi.

Da yamma ina dawowa na fada wanka ina fitowa ya salman ya shigo dakin yanayin fuskarsa dana gani sai da gabana ya fadi.

Ban gama tsorata ba sai da naga jakata da aka kwace a hannunsa.

Ai a take jikina ya kama rawa jinayi kafafuna ya kasa daukana.

Takowa yayi da niyyar ya iso gabana da sauri na ja da baya bansani ba har na jingina da jikin wardrobe .

Ya karaso gabana ya zuban manyan idanunsa da sauya kala zuwa ja yace " aina kk zuwa bayan bana gari?

Girgiza kai na soma yi cikin muryar kuka nace " babu yaya .

Yace " to daga ina wnn jakar ya fito.

Nan ma nace" bansani ba fizgeta akayi a hannuna kuma har na sanar da ya salim.......
Chapter 78 · 0% Book details