← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 128

Sashe 11

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan nayi wanka zama nayi na bata lokaci wurin tsara ado.dogon rigana saka na atamfa green Wanda yasha stone work na dage na daura dankwali gashina yasha parking har gadon baya na dauko akwatin sarkana don in zaba sai naji sallamar ya salim anan naji su inna na musu sannu da hanya nayi maza na gama sakawa har zan fita kiran fa,iza ya shigo wayata kamar bazan dauka ba na daure na daga nace " hello sis ya kk?

Tace" qalau 'yar uwa don Allah rumaisa ki kulan min da Sojana naji suna kano dazu ya salim ke shaida min wai zasuyi bikin abokinsu don Allah kar ki bari waccar banzar taje kusa dashi.

Jikina ne ya mutu nace" hmm faiza kema kinsan ban isa in hana Salima zuwa kusa da yaya salman ba.

Tace O my God wlh rumaisa wannan karon muna samun Hutu kano zanzo shawararki zanbi kawai in cire kunya in fadawa kawu ko ya kk gani? Tunda shi har yanzu ko kallo ban ishe shi ba.
Gabadaya naji maganar ta gundureni na dai daure nace"eh hakan zaifi ai sis akan ki ta zama kina wahalar da kanki kullum ai gwara ayita ta kare.

Tace" shikenan sis hakan za,ayi kawai.na gode da shawarwarinki gareni.

Nace" babu komai sis.bari inzo I will call you back.

Ban saurareta ba na katse wayar .

Dafe kai nayi nace wayyoni rumaisa gaskia gara in koya Wa zuciyata hkr da son ya salman data fara domin fa,iza ta fini sonsa gefe guda kuma ga Salima .

Dan tsaki nayi a dai dai lokacin da naji inna na kwalan kira na tashi da sauri ina amsawa na fito tace" ana ta kira ni na dauka bacci kk.to yi maza ki kai musu makulli ke suke jira.

Da sauri na koma daki na dauko key da gyalena na fita tuni har sun shiga suna jirana a coridoor su ukune tare da wani da ban sanshi ba.

Tundaga nesa suke kallona nikam duk na tsargu na dai karaso kaina a sunkuye nace" barkanku da zuwa.

Ya salim ne da mutumin suka amsa.na rasa Wa zan baiwa key din kawai na wuce na bude musu kofa.

Nace" bismillah.

Ya salim yace "yawwa mun gode 'yar uwa.

Murmushi nayi .ina tsaye suka wuce ciki ya salman kamin ya shiga ya kalleni yayi kasa kasa da murya yace" tafi kije ki sanyo hijabi sai yawo kk tsirara a cikin mutane kefa ' yar kauyece.

Haushi naji shikam tuni ya wuce.wai har yanzu bazai bar ce min ' yar kauye bane?

Da sauri na bar gidan na dawo ai ko minti biyar banyi ba ya Kira ni wai nazo nayi serving nasu.

Haka na tashi na saka hijabi na sake komawa .

Na tarar tuni ya salim da abokin shi sun fara cin abinci shi kam ya salman yana wanka.

Anan na zauna na gaishesu ya salim yana zolayata yace" rumaisa kinga Ra'is sai santi yake ni na masa waigi.

Sunkuyar da kai nayi ina murmushi .

Murmushi yayi yace" hakane girkin yayi dadi kwarai da gaske kanwata.

Nima murmushi nayi nace" nagode sosai.

Ya salim yace " rumaisa wannan shine abokinmu Ra'is ko kina jin sunansa gun faiza shekararsa biyu a Malaysia sai cikin satin nan ya dawo.

Nace " Ayya da fatan ka dawo lfy.

Yace lfy lau kanwata ya karatu?

Nace Alhamdulillah muna fama

Yace " Allah ya taimaka.

Nace " amin.

Anan ya salman ya fito sanye da 3 quarter da rigan shan iska.

Ya zauna kan kujera yace " sai yanzu naji normal.

Ya salim yace" kai dai ka saba da sanyin Lagos in ba haka ba aini dai dai nakeji ba wani zafi.

Ya salman yace" kai dama can ai bajin zafi kk ba.

Ya kalleni tace " a min serving yanzu na shirya.

Nace "to

Nan na mishi serving tuwon semo miyar kubewa na cika masa kunu a cup na kawo masa ruwan wanke hannu.

Nan suka shiga zolayarsa wai shi dan gargajiya ne.

Baima kulasu ba.ni dai ya hanani tfy sai da ya gama Na tattara na gyre wurin tsaf sannan ya barni na tafi duk na gaji.

Da sassafe kuwa na tashi na shirya tfy makaranta don muna da lectures karfe 7:00.

Lokacin da na fita na sameshi a waje shikadai sanyeda kayan motsa jiki.

Na Dan rage tsawo" yaya ina kwana?

Ya dago da alamun yanzu ya ganni yace" lfy .

Daga nan na wuce don ko na kara bazai amsa ba.

Kamin na isa kan titi sai gashi nan da mota ya sauke glass yace min " zagayo

Ba musu na zagaya na bude na shiga snn na rufe baice min komai ba yaja muka tafi har muka isa sannan yace min" yaushe zaku taso.

Na danyi shiru sannan nace " karfe biyar.

Yace " zanzo in daukeki mu koma gida.

"To" kawai naçe masa.

Daga nan na sauka na tafi har na danyi nitsa na juya sai naga har lokacin bai tafi ba ko me yasa oho.

Da yamma kuwa mun tashi banje hostel ba ina jiran shi nida Maryam ne muna cikin hira sai ka wata bakar mota ta yi parking a gabanmu kyan motar ya dauki hankalinmu sosai ni da Maryam.

Mun shagala da kallo har mai motar ya fito wani saurayi ne Dan gayu dogo kyakkyawa ya fito sanyeda 3 quarter da t shirt kansa kuwa ya tara gashi Wanda yasha gyara idonsa sanye da bakar glass.

Lokaci daya muka kalli juna da Maryam sannan muka kalleshi murmushi naga ya sakar min hade da daga gira yayinda ya cire glass ya karaso gabanmu .

Ban taba tunanin sallama a bakinsa sai kuwa naji ya mana cikakken sallama .

Maryam ce ta amsa nikam kauda kai nayi.ina jinsu suna gaisawa sannan yace" kawar taki bata magana ne?

Maryam tace " tanayi mn.

Yace" ni ai gabadaya wurinta nazo amma kuma sai ta juya min baya.

Maryam tace" to ko na baku waje ne.

Ta fada yayinda ta mike nace" don Allah kiyi zamanki ba inda zaki

Tace" ke dai bari na dan baku waje.

Da sauri na mike nima nace" muje kawai.

Shima yazo gabana da sauri yace" haba baby bai kamata ki min haka ba wlh saboda ke na shigo BUK a irin wnn lokacin pls ko bazakice komi ba ki dan bani lokaci da zamu hadu da kuma contact dinki.

Maryam dai tuni ta yi gaba.

Kallonshi nayi cikin jin haushi nace" malam ban sanka baka sanni ba bamu taba haduwa in dau number ta in baka? To kaga nifa ba irin ' yan matan da kk tunani bane don haka ka kama gabanka.

Murmushi ya yi yace" na Sani ke nitsassiya ce mai tarbiya da kamun kai shiyasa ma nazo gareki domin in Isar da sakon zuciyata.ni sunana AHMAD mahaifina Alhaji Umar Affan ma,ana GOV kano state.pls ki daure.....

Na katseshi da fadin " naji kuma na gode amma ni bazan fada maka wacece ni ba.

Ya sake fadada murmushi yace" nop ba sai kin fada ba na Sani.sunanki RUMAISA IBRAHIM.

Kallonshi nayi da mamaki ya daga min gira yana murmushi na kauda kai kamin nace wani abu wayata ya soma ringing da sauri na ciro ta a jaka ina dubawa naga ya salman ne sai da zuciyata ta tsinke .a tsorace na dauka kamin nayi magana yace " gani nan ina jiranki.

Ya kashe ina juyawa gefe naga motarsa can yana tsaye ya harde hannayensa a kan kirji yana hangomu.

Ai da sauri na wuce na bar wnn sarkin nacin a gurin .

Ya salman hade fuska ya yi sosai idonsa har ya sauya yana kallona rai bace yace"waye wancan dan iskan da kk tsaye dashi?

Aikuwa hanjin cikina har rawa suke don tsoro nace" nima yau na ganshi ......

Ya katseni da tsawa " zaki fada min gaskia ko sai naje na sameshi naci ubanshi tukun?

Jikina har rawa yake nace " wlh wlh wlh yaya yau na fara ganinshi nima.

Ya daka min tsawa" shiga mota mu tafi.

Da sauri na zagaya na shiga tuni hawaye ya fara bin kumatuna don bana son fada a rayuwata.

Yana tsaye har Ahmad yazo ya wuce da motarsa sannan ya shigo mota ya kalleni yace " bari na miki first and last warning idan na kara ganinki da wannan dan iskan kai ko labari aka bani wlh na lahira sai yafi ki jin dadi kinaji na ai?

Na daga nasa kai a tsorace .ya tashi motar rai a bace ya fizgeta da gudu nikam da sauri naja belt na daura.

Kamin mu isa gida ya zagi mutane sunfi goma a hanya alhali kuwa shi yake tukin ganganci kana ganin fuskarsa kasan yanaji da bala,i don ma anci sa,a ba Wanda ya tanka masa da sunsha Mari waya Sani ma ko alluransa ne suka motsa.

Allah dai ya dawo mu gida lfy da sauri na fita ina hamdala a raina na wuce cikin gida ana na sami inna da mmn sakina suna ma sadiya fada ita kam said kuka take har zan tambaya me ya faru sai ga ya salman ya shigo fuskar na a murtuke don haka shiru nayi

Ya na ganin sadiya yace" ke kuma me aka miki kk kuka?

Inna ta karba me za a mata kuwa ? Dadine ya isheta wai jafar yace bazai dauko mata mai aiki ba sai ma ya turo kanwarsa tazo ta zauna da ita.don haka ba zata iya zama da yarinyar ba ta dawo .

"Ta dawo? Ya fada cike da mamaki.

Ya kalli Sadiya yace" ke tashi ki tafi

Ta kara fashewa da kuka tace"yaya wlh son yarinyar yake cin amanata suke ni bazan zauna da jafar ba...

Ya katseta da fadin rufe min baki dan Allah dama bakisan Dan iska bane kk aura ko hauka zaki manna mana? Run muna shiri da juna ki tashi ki bar gidan nan.

Ta kara turbunewa tace" ni wlh ba Inda zan je sai dai in ta bar gidan .
Yace " OK taurin kai zaki min ?

Ya fara kunce belt a kugunsa ido na zaro nayi ciki da gudu kar ya hada dani .
Chapter 11 · 0% Book details