← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 128

Sashe 100

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta fara magana yake kallonta har ta gama ta ja zip din jakanta ta rufe tana shirin sanya hijabinta yace"Salmah karki yarda ki fita daga gidan nan ban baki izini ba.

Ta girgiza kai cike da takaici tace"bana neman izininki a halin yanzu domin ni tuni na cire ka a zuciyata don haka dole ne in tafi.

Gyada kai yayi yace"ok fine.amma ki sani in har kika tafi bazan taba bikonki ba!

Yana fadin haka ya juya ya fita a tunaninsa in ya fadi hakan zata hkr daga baya a daidaita don yasan tana sonshi.sai dai wnn karon bata saurara ba ta ficewarta.

Nima din dana gama zamana a palon kawai na yanke hukuncin tfy gidanmu don na lura ya salman baya duba irin hkr da nakeyi a gidansa har nema yake ya kuntata min bayan na samu da kyar na rabu da matsalar innah.duk da hakan ma ga adda A'i da sadiya snn ga wnn fitsararriya madiha.ga salmah a gefe snn ya sake dauko min salimah? Ina bazaiyiwu ba.

Ina shirin tattara kayana ya shigo dakin ganina tsaye a gaban wardrobe yasashi karasawa gabana yace"rumaisa ke ma tfyn zakiyi?

Murmushi na sakar masa wanda yafi kuka ciwo snn nace"ina zanje cikin daren nan yayah ? Kai ko gari ya waye ma ai ba inda zanje ni dole in zauna .....

Ido ya zuba min yana son ya karanci wani abu a tattare dani da sauri na juya na kama shirya kaya a wardrobe.

A hankali yace"baby.

Na juyo muka kalli juna hannayena ya kama ya rike snn yace"Rumaisa nasan dama ko kowa zai juyan baya ke bazaki juya min ba snn nasan duk abinda nasa a gaba ke mai iya supporting dinane a kowani hali shiyasa nake dada sonki a cikin zuciyata.Rumaisa ko kadan ba ina son in auri salimah don na kuntata maki bane kawai dai ina tausayin halinda salima take ciki ne tunda tayi aure wahala take sha kuma kinga........

Gabadaya na gama cika fam tsabar haushi da takaici amma na danne zuciya ta nayi murmushi nace"na gane yayah Allah ya bada sa,a.

Na zame hannuna cikin nashi a hankali snn na juya da sauri na shige toilet na kulle.

sai da na tabbatar ya bar dakin snn na fito da sauri na sawa kofata key.

Koda gari ya waye yana tfy daki na tattara da fareeda sai gidan mama. Na sanar da mama dukkan abinda yake faruwa amma sam mama na lura bata damu ba har kokari take in koma gidana.

don haka wata dabara ta fado min airport na tafi nayi booking tfy abuja na kuwa ci sa,a jirgi zai tashi 3:00pm.

ba tareda sanin mama ba muka daga Abuja da farida.mama duk tunaninta gida drivernta ya kaini .

shi kuma yana can wurin aiki be san gidansa ya watse sauran madiha da yan aiki.don munir ma na ce hakim ya kaishi gidan mama kawai.

ba jimawa muka iso Abuja gidan kawu kasim na sauka don alredy na fadawa momy zuwaira ina zuwa .

Bayan munci abinci mun huta anan na fada mata komai.

Cikeda mamaki tace"lallaima salman abinda yake shirin yi knn?saboda rashin hankali kuna zaune lfy shine bai masa ba yake son tada wani fitina?don ni banga dalilinda zai sa ya sake kara aure ba .duk da ma dai nasan ba haramun bane.

nidai kuka na shiga yi tsakani da Allsh nace"momy wlh bazan iya zama da salima ba.ni wlh matsalolin gidan ya salman ya isheni daga wnn sai wnn.

momy tace" wlh banga laifinki ba rumaisa kinmayi kokari kuma kin daure don haka ki kwantar da hankalinki bazan taba barinsa yayi auren nan ba in Allah ya yarda tashi ki hau gado ki kwanciyarki ki bacci abinki shi kuma zaizo ya sameni se munsa kafan wando daya dashi.

Tana gama fadin haka ta dauki farida suka fita.

Da farko kawu kassim ya ce lallai sai in koma inci gaba da hkr amma ina momy ta dage sosai akan bazan koma sai ya salman yazo tukunna.bansan ya tayi ta lallaba kawu har ya yarda na zsuna ba.

Tunda ya fahimci ina Abuja gidan su momy gabadaya hankalinsa ya tashi don yasan tabbas in yazo momy zata masa ba dadi.
Gabadaya ya shiga damuwa ga salmah ta tafi kuma taki dawowa kuma sai zugata akeyi akan ko ya nemeta kar ta dawo ya saketa kawai don haka ta matsa dole sai ya saketa ita ya isheta zama dashi har da ce mishi matsalar rashin haihuwa da batayi ma daga wajansa ne shine yake da problem lol!
Da yake rabon zama tsakaninsu ya kare sai ya biye mata ya saketa din.

Dama innah ma tace kar ya dawo da ita kawai dai ya je yayi kokari ya dawo dani ya lallabani in yi hkr ya kara auren.domin ita har goyon baya take bashi na ya auri saliman.dama can kunsan tana son salimah.

Gabadaya al,amarin ya dagule masa dole ne kawai yayi niyyan zuwa abj don ya dawo dani.

Don haka koda ya sami time tuni ya taho da jirgi gidan ya salim ya fara zuwa.tun a hanyarsu na dawowa gida daga airport ya salim yace masa" salman mu fara zuwa mu gaida su momyn mana.

Yace"kai barni tukun se munje gidanka na gama tunanin yanda zan fuskanci momy in yaso daga baya se muje.

Don wlh jikina yana bani akwai matsala tunda kaga mummy da daddy suka yarda rumaisa ta zauna gunsu ba tareda sunce min ko sannu ba to fa kasan akwai matsala.

Salim yayi dariya yace" to banda abin salman ka hkr mana kawai da maganar auren salima ni fa banga meye dalilinda zaisa kayi wnn auren ba.

Sauke numfashi ya salman yayi yace"hmm kasan meye salim wlh tausayi saliman ta ban ko kasan cewa ita da kanta ta rokeni dana aureta ?

Salim yace"what da kanta ?

Ya salman yace"wlh kuwa tunda Ahmad ya saketa ta buga ta sanar dani snn ta kara da gaya min irin mugayen halin Ahmad don tace yanzu bayan shaye shaye ga neman mata na bala,i har matan aure yake bi.snn ita tsakaninta dashi sai wulakanci har da duka shine kaga a karshe yazo ya saketa snn don rashin adalci irin na familynsu sai suka dinga dora mata laifi.mahaifinta ne kadai take samun sassauci daga wurinsa har yana ce mata in ta gama idda tayi maza ta sami miji ya mata aure ta huta .don baya son azo daga baya ace za,a daidaita su da Ahmad saboda kaga akwai yara uku a tsakaninsu.to fa shine da ta gama iddan take rokona dana aureta don Allah kuma ta min alkawarin zata zauna lfy da rumaisa .kuma kasan dama ita batada problem da inna.

Ya salim ya danyi shiru snn yace"hmm to ni bansan me zance akan wnn maganar ba salman.

Ya salman yace"karka damu kawai ni so nake muje da kai gun momy mu mata bayani yadda zata fahimceni .in yaso ita rumaisan zan san yadda zanyi in lallaba abata kasan batada matsala.

Ya salim yace"ai kuwa wnn karon kam da matsala don daga ganin yanayin rumaisa bazata hkr ba.amma kasan ance tsakanin mata da miji se Allah kai kasan matarka kasan yadda zakayi ka shawo kanta kuma nidai sai dai ince Allah ya bada sa,a.

Har suka iso gidan ya salim suna tattaunawa.

Ruma ta fito ta tarbesu da fara,a cikin jikinta wata hudu har ya dan fita a jikinta.
Ya salman yace"sweety ki bi a hankali fa.

Hade fuska tayi tace"ni mantawa ma nayi darling fushi nakeyi da kai?

Ta fada yayinda ta koma cikin gida ta barsu tsaye ya salman yace" hmm mata knn akan kishiya sun dinga daga hankalinsu alhalin Allah bai haramta ba.

Ya salim yayi dariya yace" hmm kai dai muje ai ka barowa kanka matsala.

Sai da sukayi sallar la,asar suka tafi gidan kawu kassim.

Suna shiga suka ganni a harabar gida ina taya farida wasa muna dariya.

Ni duk tunani ya salim ne kadai yazo har na dauki farida ina cewa muje ga daddy yazo.
Ganin ya salman yasa na hade fuska na juya da sauri na nufi cikin gida.

Aikuwa da saurinsa ya sha gabana tsayawa nayi ba tare da na kalleshi ba .
Ya karbi farida dake masa dariya tunda ta ganshi yace"haba baby me yasa kika min haka.

A daidai lokacinda ya salim ya karaso don haka da sauri na shige palo.

Momy na ganina tace"ya ya me ya faru?

Nace"ya salman ne yazo.

Itama daure fuska tayi a take tace"je ki daki karki yarda ki sakan masa fuska kome zaice miki .

Ina wucewa daki suka shigo da sallama ta amsa ba tare da ta kallesu ba.

Jikin ya salman a mace suka zauna kan kujera ya kalli momy ya dan sosai kai yace"momy ina wuni?

Harara ta watsa masa ta tashi ta barsu a palon
Ya salim yace"hmm kagani koh?

Jikin ya salman yakara yin la,asar don sam momy bata fushi dasu tun suna kanana idan sukayi laifi saidai ta musu fada in ya wuce kuma shikenan.amma da girmansa bai taba gaisheta ta ki amsawa ba se yau don haka ya kalli salim yace"anya danuwa rumaisa ba sharri tazo ta min ba kaga fa momy bata taba yi min haka ba.

Haka suka dauki tsawon lokaci suna zaune shiru momy bata fito ba har sun yanke hukuncin tfy sai gata ta fito don a tunsninta sun jima da tfy.

Suna ganinta ya salman ya tashi da sauri zai karasa gunta ta daga masa hannu hade da fadin"karka yadda kazo inda nake.

Bai saurareta ba ya karasa gabanta da sauri ya durkusa ya rike kafanta yace"please mom kiyi hkr karkiyi fushi dani wlh bazan iya walwala ba momy .momy fushinki babban tashin hankaline a gareni don Allah momy ki min wani hukuncin amma ba irin wnn ba.

Ya juya gun ya salim yace"danuwa baza ka sa baki bane?

Ya salim ya boye dariyarsa yace"gaskia ya kamata insa baki .momy don Allah ki yi hkr kinga fa soja guda durkushe a gabanki.manyan gari mala'ikun duniya masu bada horo .......

Bai karasa fada ba momy ta jefeshi da wata harara don haka mikewa yayi ya fita yana dariya.

Shi dai ya salim har lokacin yana durkushe gabanta yana aikin bada hkr.
Chapter 100 · 0% Book details