← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 128

Sashe 77

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kuwa akayi washe gari tare muka shiga dashi wurin innah bayan mun gaggaisa yace" inna wnn akwatin ko na sadiya kk canza baki sani ba aka kaiwa rumaisa don kaysn babys ne kawai a ciki.

Inna tayi murmushi tace"ina sane sarai rumaisan na kawowa ko dai bata da cikine?

Sunkuyar da kai nayi ya salman ma shiru yayi.

Tace " ikon Allah kamar na sani Allah to ya raba lfy na kosa inga yaranka salman

Da sauri ya salman yace" inna rumaisa fa bata da ciki sai dai muna fatan......

Zaro ido tayi tace"har yanzu? To ko batada lfy ne ? Kai gaskia akwai abin dubawa a wnn lamarin kamata kuje asibity a dubaaku don asan daga ina matsalar take .

Yace"innah ai haihuwa daga Allah ne kuma ni a ganina ba wata matsala tunda ta taba bari har sau biyu kuma kinga aurenmu ko shekara baiyi ba.......

Ta katseshi da fadin" salman ai auren yanzu ba kai shekara ake haihuwa ko baka ganin 'yanuwankane faiza da sakina duka suna da ciki ga matar salim ma ko yau ko gobe amma kai shiru gaskia akwai abin dubawa.

Sai lokacin adda A'i tayi farat tace " kamata yayi dai kuje ku bincika don watakila rumaisa tana da problem tunda kaga tayi bari har sau biyu gashi daga lokacin shiru har yanzu.ba zama zakuyi hakan nan ba ku dai je a duba se a bata magani.

Inna ta karba " wnn shine abinda yafi dacewa kuyi don ni na kosa inga yaranku koda naje hajj ma nayita muku addua.

Shiru kawai mukai ni da ya salman don ranshi ya matukar baci daga bisani mikewa yayi ya kalleni yace" ke tashi mu tafi.

Haka na tashi jiki ba kwari har zan fita sadiya tace" kin manta kayan naki fa.

Inna tace"aikuwa dai kizo ki dauka kije ki adana mai kyau har ki haihu .

Na dawo na dauki akwatin hade da yi mata godiya na fita.

Ya salman tuni ya fita banma ganshi ba.

Ina zuwa gida daki na wuce na dora akwatin kan wardrobe snn na koma kan gado na kwanta kukanda nake kokarin hana kaina ya gagara haka na shiga kuka sosai na rasa me yake min dadi a duniya.

Har ya salman ya shigo jikinsa a mace ya karaso ya zauna yayinda ya dagoni ya kwantar da ni a jikinsa yana shafa kaina.

A hankali ya fara magana " baby kiyi hkr don Allah nasan dolene maganganunsu inna ya dameki nima kaina banji dadi ba amma zan sami inna in mata magana kinsan wani abun duk su Adda A'i ke ingizata.

Nidai bance masa komai ba kukana kawai naci gaba dayi yayinda shi kuma yaci gaba da rarrashina .

A kwanakin sosai na shiga damuwa akan maganar haihuwa.don kullum na shiga gun inna kusan maganarta knn .

Ya salman tuni ya koma lagos ya barni a lokacin mun fara sevice dinmu inda nake dan samun sauki knn in na fita don bana zama gida sam sam.

Bayan dawowarsu inna haj da sati biyu ne fa,iza da sakina suka haihu tsakaninsu 2 weeks ne faiza ta sami fatima zahra sakina kuma ta sami da namiji Abduljabbar.

A lokacin ni kadai a gida sai 'yan matan nan sa,a da zainab.

Bayan sunan babyn sakina da kwana biyu ne ruma ma ta saukea masha Allah an sami baby boy murna a gun ya salman har yafi na ya salim abun har mamaki ya ban.

Suprise kawai ranar na dawo gida na sameshi bai gaya min zaizo ba.

Nace"yaya shine ko ka fada nmin na shirya tarbanka?

Zuba min ido yayi yana kallon kayan jikina.har na dan fara tsarguwa.

Nace"yaya lfy?

Ce min yayi" ke yanzu haka kk fita kamar wata arniya?

Na dubi kayan jikina riga ne da wando kayan copers sai dan karamin hijabi snn na kalleshi nace" yaya hijabi fa nasa kuma kaga da motata nake zuwa na ......

Ya tari numfashina da fadin" matukar kina son kici gaba da service dinnan to dole ne ki dinga suturta jikinki duka .wnn hijabin da kk takama dashi ki bari sai kinje can ki saka amma ki tabbatar da kin dauki babban hijabi kin saka kamin ki fita daga gidan nan haka ma in kin tashi dawowa karkiga wai don a motarki kk dawowa.

Jikina a sanyaye nace" to yaya zanyi yanda kace .

Ya gyada min kai snn ya fita.

Ni kuma na wuce ciki don cire kayan jikina .
Ko wanka ban tsaya yi ba na wuce kitchen da sauri na shiga shirya mishi girki.
Ana kiran sallar magriba na gama na shirya dining snn na wuce daki na fada toilet nayi wanka hade da alwala .

Sai da na idar har sallar isha snn na tashi na fara shiryawa.ado nayi na musamman na saka doguwar riga na material mai combination nayi kyau sosai.

A lokacinda na fita palo suma suka shigo da ya salim nayi musu sannu hade da fadin " mu isa dining .

Ya salim yace "aiko bakice ba .

Dariya nayi nace" yaya angon karni ashe ka dawo ya kabar maman baby da babyn?

Yana murmushi yace lfynsu lau suna gaidaki wai yaushe zakizo.

Na kalli ya salman shima ni yake kallo amma baice komai ba don haka nace" ai zanjene kar ta damu.

Muka wuce dining na musu serving nima nayi na zauna muka soma cin abinci muna dan taba hira ni da ya salim shi dai bai sa mana baki ba har saida ya salim yace masa " yaushe zakaje kayiwa dan naka huduba?

Kai tsaye yace gobe insha Allah.

Da sauri nace "yaya nima zanje don Allah.

Yace"aikin naki fa.

Nace"ba damuwa.

Hade fuska yayi yace in kk je gobe bazaki je suna ba zabi ya rage naki.

Ya salim yace" kaifa salman bakada kirki wani lokacin to meye a ciki don taje sau biyu?

Shiru yayi ya salim ya kalleni yace " rumaisa ki shirya dake zamu tafi goben in Allah ya yarda.

Murmushi nayi nace " to yaya nagode.

Shidai bai kuma cewa komai ba na luro yau 'yan halin nasa sun murdo gaban goshine.ni dai inda sabo na saba don haka ban damu ba.

Ya salim kam muna gamawa ya fita ya barmu.

Na kalleshi cikin kwantar da murya nace" yayana don Allah waya bata maka rai ne ?

Shiru ya min na sake cewa "inde akan maganar sutura ne kayi hkr daga yau na daina kwata kwata banson bacin ranka yayana.

Ba tare da yace min komai ba ya wuce side dinshi binshi nayi da sauri na iskeshi yana kokarin cire kayanshi da sauri na karasa gabansa na soma tayashi.

Snn nace" yaya don......

Ya katseni da fadin" banson yawan surutu pls na gaji ina son in hutane.

Jikina a mace nace " to yaya .

Ya wuce toilet ya barni nima fita nayi na tafi dakina rai ba dadi.

Da safe kuwa tunda na gama komai daki na koma nayi kwanciyata.

Jin shiru shiru ban fito ba yasa shi shigowa cikin shirin tfy Abuja?

Ya kalleni cike da mamaki yace"baki tafi aikin ba?

Nace"eh.

Yace " to meya faru?

Tabe baki nayi nace" ni na hkr da aikin bautar kasarne zaman aurena yafi min komai muhimmanci don haka bazan so na dinga bata maka rai ba yaya.

Ya karaso bakin gadon hade da fadin " wayace miki fushi nakeyi?

Hawayene ya cicciko idona nace" ba gashi nan ba tun jiya sai baka hkr nikeyi .

Ya zauna hade da jawoni jikinsa yace" shikenan na hkr karkiyi kuka pls.

Ya dago fuskata yana share min hawaye snn yace in tashi na shirya mu tafi Abujan suna jirana.

Muhammad kassim shine sunanda ya salman ya zabawa babyn .

Bayan mun gama shagalin suna a tunanina yaya zai wuce lagos amma shiru koda na tambayeshi ce min ya dawo kano ne.

Don haka wasu lokutan shi yake kaini wurin aiki.

Ranar kawai yana saukeni ya tafi sai ga wata mota baka da tintet tayi parking a gefena ban kula ba nayi wucewata

" *Queen* "
Kamar a mafarki naji muryar *Ahmad*

Da sauri na juyo shi din ne kuwa na gani ya sauko daga motar yana murmushi Ahmad ya kara kyau da jiki ga haske gaskia.

Ya karaso gabana fuskata na yabo ba fallasa nace" Ahmad dama kana duniyar nan.

Dariya yayi yace" gani kina ganina queen ya dai ya kwana da yawa ya share wa?

Nace"hmm Ahmad knn bakaji labarin nayi aure ba?

Yace " naji kunyi aure da salman mana.

Nace "ok ina salima ta haihu ne?

Yayi murmushi yace" eh mun samu baby boy umar farouq.

Sai lokacin nayi murmushi nace " Allah ya raya bari in shiga ciki sauri nike.

Yayi murmushi snn yace" ai na gani amma dan bani minti daya pls.

Ya tafi motarsa da sauri ba jimawa ya dawo ya mika min wani card na kalleshi nace"wnn din na meye ?

Yace" karba ki duba?

Na karba murmushi yayi yace" thank you sai na jiki.

Binshi nayi da kallo har ya shiga mota ya tafi ban biyo ta kan card dinba na jefa a jaka.

Bayan kwana biyu da faruwar haka kawai ranar aka kirani da boyayyiyar number ina dagawa naji muryar ahmad ce mun yayi " queen shiru shiru har yanxu baki amsa gayyata na ba.

Jin motsin shigowar ya salman yasa na kashe da sauri kuma cikeda tsoro da fargaba.

Ya karaso kusa dani yace " keda waye a waya kuma a wnn daren?

Nace"nima ban sani an boye numberne an kirani .

Yace"to karki kuma dagawa.
Da ssuri nace masa to

A jiye wayar nayi nace"bari yaya na kawo ma fruit salad dinka

Da sauri ya kamoni yace" ki barshi kawai yau dinnan ke kadai nake bukata baby.

Murmushi nayi nace" yaya dare fa yayi sosai is time for sleeping.

Ya rumgumeni hade da lumshe ido yace" no bazan iya bacci ba baby weather din yau bana bacci bane .

Ya karasa fada yayinda ya soma shashshafani nima lumshe ido nayi na fara karbar sakonninsa a shagwabe nace" yayana.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya snn yace" babyna!
Chapter 77 · 0% Book details