Sashe 90
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na zauna a kasa na fara gaisheda innah da sauri tace"dakata da gaisuwarki don bashi ya kawoni ba ina dayar mara kunyar kuma take tun dazu nace a kirata shine ta ba banza ajiyarmu.don haka kije ki kirata.
Har ina shirin tashi sai ga salmah na saukowa itama cikin kwalliyarta sai dai fuskarta ba fara,a ta karaso ta yiwa su inna sannu da zuwa .
Inna tace"nemi wuri ki zauna kema.
Salmah ta zauna ba tare da tace komai ba .
Inna ta numfasa tace "to zuwa nayi wurinku don ku bar min gidan dana yau dinnan saboda shi kun gama dashi baya ganin laifinku amma ni baku gama dani ba don haka ko wacce shegiya ta tattara kayanta ta bar gidan nan yanzu don zamanku a gidan nan bai da amfani komai bakuda wani aiki sai dai kuci abinci ku cika masai da kashi.......
Salmah tace subhanallah innah me yai zafi kk fada mana irin wnn kalaman?
Sadiya ta watsa mata harara tace "har ma kinada bakin tambaya keda kk hadani da danuwana ko magana baya min.
Salmah tace"lallai ma sadiya nice ma na hadaki da danuwanki .....
Anan fa sadiya suka shiga sa,insa da salmah suka shiga gaggayawa juna bakaken maganganu innah kam sake baki tayi tana kallon salmah cike da mamaki .
Tace"ashe salmah bakida kunya haka bansani ba ?
Salmah tace"inna ai banice mara kunyarba ga mara kunyar nan data zo har gida na zata ci mun mutunci shikenan kuma sai in kyaleta ?
Inna tace"to yayi kyau sai ku wuce kuje ku tattara kayanku ku bar gidan nan kamin salman ya dawo ya bi kowacce da takardan sakinta.
Salmah tace"tabdi wlh babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan nan gidan mijinane bai koreni ba don haka ba inda zanje ehe!
Gabadaya mamaki ya rufemu ni kam da ido nake binsu gabadaya
Sadiya tace " salmah kinsan da wa kk magana kuwa?
Salmah ta yatsuna fuska tace"da inna nake magana sai me .......
Ji kake tass sadiya ta dauke fuskar salmah da mari itama batai wata wata ba ta rama anan suka shiga kokuwa tashi nayi da sauri ina kokarin janye sadiya ina don Allah ku bari ba amfani kuyi hkr .
Na kwalawa sa,adatu kira nace tazo itama muka shiga raba fada inna kam ta rasa me ma zatayi kawai sai ta fashe da kuka tana cewa sa,adatu kira min salman yanxu yanzun nan yazo yaga irin cin mutuncinda matansa suka mini.
Ta rike hannun sadiya tace "sadiya rabu da ita yau dinnan salman sai ya sallamesu dukansu biyun tunda ba gidan uban su bane gidan dana ne kuma dolene ku barshi a yau.
Ni da naga ba sarki sai Allah tuni na tafi side dina na dauki wayata na kira salman nace yazo yau ma gida ba lfy kuma ni tfy ma zanyi.
Daga nan na katse kiran na jefa wayar cikin jakata na dauki hijabina da key din motana na fita ta kofar baya na figi motata sai gidan mama bansan ya suka kare ba!!!!!!!!!
Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰
*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``
*PAGE* ➡80
***********Salmah zagewa tayi ta rufe ido ta dinga zubawa innah rashin mutunci kuma tace wlh babu inda zata je don nan gidan mijintane.
Inna tace"amma dai banji kince gidan ubanki bane ba koh?to wlh zaki tafi bari salman din yazo yau sai dai ya zaba koni ko ke mara kunya fitsararraiyar banza fitsararriyar wofi .........
Salmah tace"hmmm wlh babu inda zanje aurena da suleyman mutu ka raba bari kiji da kyau.don ni nafi karfin tunaninku ko kin dauka nima shashasha sakarai ce kamar rumaisa ? Duk fa abinda kukeyi ina sane manna muku hauka nayi kawai inga iya gudun ruwanku.idan ba munafurci waye ......
A hasale sadiya tace "wlh ki sawa bakinki limzami ya isheki ciwa mahaifiyarmu mutunci.don na lura bakida tarbiya hala haka uwarki ta koya miki kizo kiyi mana koh?
Salmah tace "sadiya bana gargadeki akan karki kuma sa bakinki ba ?to wlh ku tashi ku fice min daga gida tun kamin na aikata muku abinda ba kwa tunani.
sadiya tace"idan gidan ki ne ba sai ki fitar damu da karfi ba mara mutunci.....
salmah ta gyada kai tace ok jirani ina zuwa.
ta wuce kitchen da sauri tabarya ta dauko cikin store ta fito babu ko tsoro ta nufo sadiya ta daga zata buga mata.
Daga inna har sadiya zaro ido sukayi cike tsoro sadiya tayi bayan inna da sauri.
salmah kuwa a rashin sani tuni ta sauke tabaryar akan innah ji kake tim!!!!!!
Inna ji tayi dif kamar an dauke wutan nepa a hankali jiri ya soma dibanta a take ta yanki jiki ta fadi sadiya tasa ihu a razane hade da fashewa da kuka tana "wayyo Allah na shiga uku ta kashe mana uwa.
Sa,adatu ma a rude ta shiga girgiza innah tana kuka .
Salmah kuwa tuni tayi jifa da tabaryar tayi part dinta a rude jikinta na rawa domin sam ba innah taso bugawa tabarya ba kaddarace dai kawai .....
Nan ta mike cikin gaggawa ta fara neman hijabinta da makullin gidan domin tasan duk inda ya salman yake yanzu ya kusa isa gida in kuma yazo yaga halinda mahaifiyarshi ta shiga to fa kashinta ne zai bushe.
A tare ya salman suka isa gidan da hakim wanda ya dawoda munir daga makaranta .
ko parking mai kyau ya salman bai tsaya yi ba ya fito da sauri ya nufi cikin gida bai ko kula munir da ke masa oyoyo ba hakim ya fahimci ba lfy da sauri ya bishi cikin gidan.
a sume har lokacin ya samu innah su sadiya sai kuka suke tayi .
Salman ba karamin tsorata yayi ba yazo ya daga innah yana"me ya sameta ?
Sadiya tace"Salmah ce ta daketa da tabarya !
what !!! Ya fada cikin yanayin mamaki da sauri ya daga innah ya fita da ita a guje sai cikin motarsa yace da mai gadinsa kar ya kuskura ya bar salmah ta fita daga gida yaja motar da gudu sai asibity gabadaya gani yake kamar inna mutuwa zatayi hankalinshi ya tashi sosai idan nan ya kada yayi jazir yayinda zuciyarsa ke tafarfasa ya na tunani wani irin hukunci zaiwa salmah .
Bai bar asibityn ba saida ya tabbatar innah ta farfado kuma a lokacin abba yazo don haka bai ko sallamesu ba ya bar asibityn ya dawo gida ya iske salmah cikin yanayin tsoro bai tsaya tambayarta komai ba ya zare belt ya shiga dukanta ta koina ihu take tana neman agaji Allah ya sota kofa a bude ta sami ta fita a guje Hakim ne ya bita da sauri ya isketa hanyan get jikinta duk jini abun babu kyaun gani don haka shi ya dauketa a motarsa ya kaita asibity.
Ni kuwa tunda na isa gida mama ta ganni hankali tashe tace"lfy yau kuma me ya faru?
nace"hmm komai ma ya faru mama.
Ba bata lokaci na shiga bata labarin abinda ya faru na karashe maganar da fadin "na barsu bansan ya zasu kare ba ni dai bazan iya zama ya salman ya dawo su doran sharri ba.
Cike da mamaki mama tace"hmm baga irinta ba shatu dai bansan meyake damunta ba.gashi taje taja ma kanta cin mutunci a gurin surukarta Allah dai ya kyauta ni dai banga laifin salmah ba wlh
Nace" mama ban taba tunanin salmah zata maidawa su innah martani ba.
Mama tace"Ai ni ta burgeni irin halin shatu sai hakan..
Muna cikin tattaunawa daddy ya shigo da sallama cike da fara,a mama ta amsa.
Nace"au dama daddy kana gari?
Yace"daxu nazo mamana baki sani ba koh?
Nace"eh.mama bata fada min ba.
Mama ta harareni hade da fadin"saboda banida aikin yi koh?
Na danyi dariya snn na gaisheda da daddy hade da tambayarsa labarin mutanen yola duka yace lfy.
Daga nan ya wuce sashinsa mama tabi bayansa. Ba awani jima sosai ba daddy ya kirani akan maganar da nazo da ita ce min yayi"ihsan a kara hkr duk da dai alhamdulillah ban taba jin kinyi tashin hankali da kowa ba to hakan nakeso kici gaba da hkr har Allah ya kawo karshen abin.snn duk sanda salman yazo ki bishi ku koma kinji tunda kinga yana sonki kuma baison bata miki don haka kema kici gaba da kyautata masa .
Nace insha Allah daddy .
Yace"Allah ya miki albarka.
Ameen nace daga nan na tashi na tafi dakina sai da dan gyaggyara snn na yi wanka na kwanta.duk naji na gaji ko don raba fada da nayi ne oho.
Salman kuwa bayan ya gama da salmah kan sadiya da sa,adatu ya dawo yana tambayarsu yadda akayi yayinda yacewa sadiya" ke ban ma hanaki zuwa gidana ba? Wato bakijin magana koh?
Nan itama ya sauke mata nata rabon ranar tasha belt har ta gigice kuma yace ta fitan masa daga gida kamin ya kakkaryata daga nan fita yayi cikin fushi sai asibity .ya samu innah ta dawo daga hayyacinta daidai .
Fuskarsa a murtuke ya mata sannu bata amsa ba kawai binsa take da kallo .
Salmah kuwa daga asibity da hakim ya kaita gidansu ta koma hankalin iyayenta ya tashi sosai har mahaifiyarta na cewa baga irinta nan ba saida muka hanaki auran wnn sojan kince ke kinji kin gani su fa sojojin nan ba imani ne dasu ba zasu iya kashe mutum ma yanxu dubi yadda ya ji miki ciwo koina wlh bazaki kuma komawa gidansu ba kuma wlh zai fuskanci bacin ran mahaifinku .
Salmah kam na kwance kanta sai ciwo yake.
Hankalina ya tashi ganin har dare ya salman bai zo gurina ba ko abinci na kasa ci na rasa me yake min dadi bacci ma ba sosai na samu nayi ba.
Da safe muna cin abinci a dining kawai na soma ji tashin zuciya na mike da sauri daddy yace"ihisan lfy ?
Nace"amai nake ji.....
Ko kan na rufe baki tuni na shiga kwara amai ba shiri mama ta mike ta rikeni daddy yace"subhanallah Amina dama bata da lfy ne?