← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 128

Sashe 56

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar gaba daya na wuni amsa kiran waya domin duk masoyanmu saida suka kira suka tayamu murna amma shi uban gayya shiru tun bana damuwa har na gaji na gayawa ruma tace kar in damu zai kira ni.

Su daddy kam ana can bikin nadin sarauta har dare suka shigo da aunty samira duk ya gaji gaba daya.

Aunty samira ma sai da ta tayani murna tace " ihisan
ashe duk tsumaki da na dinga yi rabon salman ne ba yayana ba.

Sunkuyar da kai nayi ina murmushi tace " ai shikenan yayi ma kansa Ku kuma Allah ya baku zaman lfy da zuria ta gari.

Nace " Na gode aunty .ai na dauka zaki kwana a gidanku yau kam

Tace " tab bazan iya ba Wa zai kulan min da daddyn naku?

Dariya nayi nace " kai aunty ga nan Momy .

Tace "ke manta Momy ko ran girkinta ma ba wani cikakken kulawa take bashi ba bare.

Ta fada hakan yayinda ta ce " kije daddyn ki na parlour .

Nace " kai aunty ki barshi kawai sai gobe ya huta.

Tace " to ai shikenan.

Da yake a dakinta ta kirani muke tadin nan da nan ta shiga wanka saida ta sheka wankanta mai rai da lfy ta fito ko kunya babu tazauna ta gyre jikinta tsaf tasa kayan baccinta mai kyan gaske turarrurka kuwa ba,a magana don har na ji hancina ya fara toshewa tashi nayi nayi mata sai da safe .

Can dare inata juye juye na kasa bacci tunanin ya salman kawai nake ji nake kamar na kira shi ni din.

Aikuwa kamar ya Sani kawai sai ga kiransa naso naja aji amma na gagara da sauri nayi receiving sallama na yi masa.

Ya amsa can kasar muryarsa kamar bai son magana yace " kina nan qalau koh?

Murmushi nayi nace " lfy yaya yau dai fushin ya kare koh?

Kamar ba zaiyi magana ba yace " fushin me zan yi ? Ai nasan wnn mutumin bazai aureki ba rumaisa.

Nace " meyasa kace haka yaya?

Yace " saboda ni kadai ne mutumin da zan iya auranki a kowani irin hali don sanin kanki ne rumaisa ni ke nake so ba gangar jikinki ba.yanayinda kika tsinci kanki a baya bazaisa naki auranki ba .don haka nake da banbanci da sauran manemanki hope kin fahimceni?

Shiru nayi jikina ya mutu sosai har hawaye ya taru a idona gaskia Innah ta cuceni sai yanzu nake jin zafin abun a raina sosai .wato ya salman har yanzu yana ganina da wnn tunaninsa duk wata mutuncina ya zube koh?

Murmushi nayi lokaci guda nace " Na gode yaya da ka taimakeni ka aureni amma fa ka Sani akwai babban suprise da zan baka Wanda bazaka taba mantawa dashi a rayuwarka ba.

Ba tare da kulawa ba yace " naji kuma ina jira saboda kin matsa min da maganar anyway,dama na kira ki ne in tambayeki ko zaki hkr ki zauna a gidanku in yaso in na gama da ayyukana Na dauki hutu sai nazo na daukeki in yaso 'yan bikin suje suyi jerensu suga gida su watse ko dai kin fiso a kaiki kanon a gama bikin kawai zaki jirani har sai na dawo ? Don gaskia ni bazan dawo ba sai ayyukana sun kare.

Shiru nayi Na lura Sam ya salman bai damu da auran nan ba don baya murna kamar yadda ni nakeyi sai kace ba ango ba wai bazai bar aiki ya dawo ayi bikin ba alhalin nasan zai iya bada excuse a barshi ya taho.

Hawayene shar shar a idona na ce" duk yadda kk so hakan za,ayi .

Ina fadan haka na katse kiran na kifa kaina akan pillow na shiga rusar kuka kamar raina zai fita.

Kukana ya tashi rumasau don mu biyu ne kawai a dakin banda wasu kawaye.

Ta kunna wuta tana subhanallah Ihsan lfy?

Duk ta damu haka na daure nace " ruma kina jin wani irin wulakanci da ya salman yake shirin yayi min sai kace auren bazawara .

Nan na fada mata komai ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kai tace " case dinki da salman baya karewa don Allah ki daina damuwa akan wnn Ihsan yana fa sonki kawai fushi yake don yana ganin kamar kin daina sonsa ne amma ba wani abu bane .

Ganin Sam ban saki raina ba yasa tace " amma zan kira salim in fada msa kwanta ke dai sai da safe!!!!!!

Ayi hkr da rashin post kwana da yawa naje bikine amma yanzu na dawo🥰😘😍

Hauly ce👍🏻🥰
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page ➡51

************ Washegari kuwa ba bata lokaci motocin kaya sun tafi kano da sauran jama,a masu tfyr mota sauran masu bin jirgi kawai.

Anan daddy ya kirani palonsa shida su ya awwal na tarar na gaushesu dukansu suka amsa cike da fara,a.

Anan daddy yace " Ihsan kinga ikon Ubangiji koh dama ance ba mai auren matar wani.don haka ko kadan bana fushi dake bana fushi da Abdallah na dauki abinda ya faru a matsayin kaddara Wanda Allah ya rigada ya rubutashi.snn rukayya ta min bayanin komai akan rayuwarki ta jamia na godewq Allah da ya tsare min ke Ihsan kuma duk Wanda ya miki wnn abun shi yasani da Allah . ko ba haka ba?

Ya juya gun su yaya ya awwal ne yace" hakane daddy tunda komai ya rigada ya wuce.

Daddy yace " to don haka Ihsan ki tsarkake zuciyarki ki zauna da mijinki lfy Salman zabinki ne kina sonshi yana sonki don haka sai Ku zauna lfy.a dinga hkr kuma snn ladabi da biyayya kuma ko kadan karkiyi watsi da ibadarki ki rike addininki hannun bibbiyu shi zai taimakeki duk abinda ya sameki mai kyau ko mara kyau( ba fata ba) sha,anin rayuwane ki tattara lamarinki ki mikawa ubangijinki shi zai miki maganin komai .kar ki yadda ki dauki kudinki kije gaban wani kato da sunan kin kai masa matsalarki ya magance miki bazan taba yafe miki ba har in kinyi hakan.snn kima iyayensa biyayya da 'yanuwansa ki yi koyi da halin mahaifiyarki domin biyayyarta yasa ta shiga ran kowa a familyn galadima har gobe in an tashi ana bada misali da ita don haka nake son kema ki zamo hakan Mamana .banda bin zugin kawaye duk da ma naga ke baki damu da kawayen ba. A karshe ina muku fatan Allah ya baku zaman lfy da zuria ta gari.

Tunda daddy ya fara magana jikina ya fara sanyi hawaye ya fara zubo min na goge da mayafina ba tare da na dago ba nace " insha Allah daddy zan yi duk abinda kace nayi Wanda ka hana kuma zan kiyaye .na gode da irin kulawar da kake bani Allah ya saka maka da gidan aljannatul firdaus.

Cikin jin dadi yace " amin Mamana Allah ya muku albarka.

Snn ya kalli su yaya yace " idan akwai abinda na manta ban fada ba sai Ku fada mata .

Anan ya awwal ma yayi nasa nasihan ya samir ya karba yayi snn ya Hafiz daga karshe har da ce mun yay " in kuma anki asha bulala.

Hararsa nayi daddy yayi dariya yace " to meye na bulala kuma ana zaune qalau.

Yace" daddy ai Ihsan ta rainani ne da yawa bansan me yasa kuka gaya mata tsakaninmu ba nisa ba.

Dariya sukayi gabadaya nikam muna hada ido na masa gwalo.

Yace " au dama kukan na munafurci ne don kar ace bakiyi ba koh?

Da sauri na sunkuyar da kaina daddy yace kaga je ka kira min su rukayya da goggonka suzo suyi su tafi gidan galadima kar lokaci ya kure musu.

Anan ya kira su suka zo suma suka min nasu nasihar daganan fa mukayi sallama da daddy don daga gidan galadima sai airport su Maman sakina suna can gidan galadima don sune 'yan daukan amaryq daga dangin ango itada aunty zuwaira .Ruma ma tace ita ma dangin ango take.

Gaskia naji ba dadi rabuwa da daddyna da yanuwana a dan zaman da nayi a yola mun shaku sosai.lallai aure wani babban al,amari ne a rayuwar 'ya mace!

*******A kano kuwa su inna tuni an fara shirin tarbar Amarya harda girki na musamman don ma wnn karon 'yanuwanta na kamaru basu zo sun cika gida ba.

Kasancewar daurin auren yazo a kurarren lokaci bata samu ta yi gayya ba daga ita sai adda A'i raihana Sadiya da sa,adatu itama 'yar yayan innace wacce take gaban adda A'i da zama don tun auren ya salman da sukhaina da sukazo aka fasa basu koma ba suna nan .dama ita adda A'i a Lagos ma take aure .in baku manta ba ita a gaban inna ta girma tun haihuwar ya salman aka baiwa inna ita .kuma su Abba sun sata makaranta ta yi har secondary inda samari suka mata caa! Kunsan kanawa da farar mace lol! Nan ta zabi wani hamshakin dan kasuwa Alhaji Shamsu aka musu aure yanzu suna Lagos da zama da yaransu shidda duk sun girma.

Sadiya kam ta kasa zaune ta kasa tsaye .tunda motar kaya ta iso kano da 'yan Jere sai shiga da fita takeyi a yayinda matan baffanayena suka sanya mata ido don sunga shiga da ficen nata yayi yawa.

Hankalinta ya kasa kwanciya sai da taje ta sami su inna tace" Inna kinga kaya ?Subhanallahi wani abun ma ban taba gani ba .da kyar wasu abubuwan in ba su koma da kayansu ba don gidan zai musu kadan.

Inna ta tabe baki tace" hmm ai gara hakan kinga yanzu da gidan sarki aka kaita zasuyi ta rigima son ransu .ai dama su 'yan yola 'yan son girmane zasuji haushi sosai kasancewar yarsu a nan don ba haka suka so ba.

Sadiya tace " wlh kuwa hmm ai zasu ga wulakanci na musu tanadinsa buhu buhu .

Adda A'i ta yi dariya tace " kai Sadiya ba mutunci .

Snn ta kalli inna ta ce " goggo ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa ni da Sadiya mun ishesu.
Chapter 56 · 0% Book details