Sashe 45
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lamido palace muka fara zuwa muka shiga fada muka gaida lamido a fada sosai ya nuna murnarsa a fili ya taya daddy murna.
Munje gidansa mun gaida matansa duk sun tsufa harshi mai martaba.
Kamin mu bar gidan mai martaba ma mun kai awa biyu daga nan muka fita sai family house gidan galadima.
Tabdi ranar naga jama,a dama haka nake da gata amma nake shan gori gunsu inna.
Dangina na nesa dana kusa sunzo 'yan kalilan ne da suke kasashen waje basu zo ba .
Da kunga yanda aka cika gidan nan zaku dauka biki akeyi gagarumi.
Sashi sashi muka shiga na gidan kamin muka isa gunsu Haj rumaisa.
Allah sarki duk sun tsufa sai dai dake akwai kudi basu lalace ba da kwarinsu.
Haj rumaisa da Haj Zubaida kam rumgumeni sukayi sai kuka suna ta sambatu
Haj rumaisa sai fadi take "Allahu Akbar Allah mai iko Allah mun gode maka da ka dawo mana da ihisan cikinmu.
Ta kalleni tace" rumaisa tuni muka cire ran gsninku amma kinga ikon Rabbi yau sai gaki rabon mu dake tin kina 'yar shekara biyu.
Ta dada fashewa da kuka .
Goggo Ummi da goggo karima Suma sun shigo haka suka rumgumeni suna kuka nima na shiga tayasu.
Daddy ma hawayen ke zuba yana gogewa da hankacif.
Haka akayita shigowa ana min sannu da zuwa yayinda umma da Haj Zubaida suka dinga gabatar min da kowa.
Kai masha Allah dangina kaf ban sami matsala da kowa ba sun karbeni hannu bibbiyu.
A ranar wasu suka koma ciki har da goggo Ummi da karima.
Har Karfe tara na dare snn aka gama watsewa sai ' yan gida.
Anan ya awwal ma da matarsa hadiza har dansu daya me sunan daddy .suka mn sallama suka tafi.
Daddy ya kallisu aunty samira yace" to muma sai mu tafi ko?
Anan ummah tace"lamido a bar mana ihisan ta kwana......
Ya Hafiz ya tari numfashinta da fadin " bazata kwana ba bamu gaji da kallonta ba kinjiki da wata magana 'yaruwarkice?
Harararsa tayi ta ce " ja,iri to sai ta kwana ko ba 'yaruwataba.
Haj Zubaida tayi dariya tace" mai gidan nawa kk masa haka?
Ya samir yace wa umma kinga tsohuwa ihisan fa ba lfy ne da itaba ga gajia ga bacci don haka tana bukatar hutu sosai.
Daddy dai baisa baki ba haka ya samir ya dinga lallabasu har suka yadda muka tafi
Bayan mun isa gidanmu daddy ya kalli aunty rukayya yace "rukayya ihisan kuje ta kwana a dakinki kamin a gyara mata daki.
Aunty samira tace" Alhaji ai tuni nasa an gyara mata daki.
Daddy yace" ai so nike asa mata komai sabo fil a dakinta.
Aunty rukayya tayi murmushi tace" gaskia ne alhaji .to ihisan muje mu kwanta.
Ya samir yace " akwai maganinta da alluranta guda daya bari muje na mata inyaso sai tayi baccin.
Daddy yace " to ba matsala.
Ya kalleni yace " Mamana ina fatan baki da wata matsala ?
Na sunkuyar da kai nace " eh sai dai ina son inyi magana da Mamana.
Yace " eh gaskia kam ya kamata kuyi magana amma kiyi hkr zuwa gobe insha Allah zamu San yadda zamuyi mu nemota kiyi hkr kinji?
Nace " babu komai daddy na gode.
Anan ya mun saida safe.
A dakin aunty rukayya bayan ya samir ya bani magunguna nasha ya zuba min ido yace " ihisan me ya faru nake jin numfashinki sama sama ?
Nace " sanyin nan da akeyi ne.
Yace " kina da asma ko?
Na daga mishi kai yace" da kinyi magana da wuri na kawo miki magani ai ina inhaler dinki?
Nace " yana cikin jakata da aka sace.
Da sauri yace" to fa gaskia bazan barki ki kwana haka ba ina zuwa.
Ya tashi da sauri ya fita kan ya dawo ma nayi bacci.
Da kyar aunty rukayya ta tasheni nayi sallar asuba na idar nayi azkar ina shirin komawa bacci daddy ya shigo dakin na gaisheshi cike da fara,a ya amsa hade da fadin ihisan Allah ya maki albarka.
Nace "amin
Yace " dama nazo in dubaki ne ina fatan dai ba wani abu koh?
Nace" eh daddy ba komai.
Yace " to shikenan yanzu kiyi bacci lfy.
Daga nan ya fita aunty samira ma ta shigo muka gaisa snn aunty rukayya ta kawo min tea tace " Ihsan kisamu kisha tea samir zai zo ya baki maganinki kamin ki koma bacci.
Haka dai suka dinga dawainiya dani ba,a bari ko tsinke in daga ni dai aikina daga bacci sai cin abinci sai wanka.
Daddy ya kawo min wayarsa yace" ihisan har na fita sai naga an turo maki sako ta wayata.
Ya mika min na karba ina dubawa naga ya salman ne ya turo min tex kamar haka
*Ga* *num* *din* *Goggo* *Amina*
Murmushi nayi na duba naga num din ta nada ne inaga tayi wlcm back ne.
Na kalli daddy nace " ya salman ne ya turo min num din Mamana tayi wlcm back.
Murmushi yayi yace OK kema ya kamata ki samu kiyi ai.
Yanzu kirata sai kuyi magana .
Nace to
Nan nayi dialing num din mama ba jimawa ta daga hade da sallama.
Na amsa hade da fadin mama nice
Tace" rumaisa fatan dai komai lfy hankali na duk a tashe salman ne yace min kin isa lfy ba komai hakane?
Murmushi nayi nace hakane mama kuma na sami kowa lfy kuma kowa ya karbeni cikin farin ciki.
Tace " Alhamdulillah Allah mun gode maka yanzu sai na sami lokaci in kiraki insha labaru. Sai dai layinki duk basa tfy meyasa?
Nace" mama wayar ya batane amma zan yi wlcm back sai muyi magana .
Tace " to ba matsala ina mahaifinku ?
Murmushi nayi na kalli daddy nace " gashina nan ko na bashi.......
Kamin na karasa ta katse.
Daddy kuwa tuni mika hannu yana murmushi yaji ina cewa in bashi.
Jikina a mace nace " ta katse.
Ya karbi wayar sa yace " ihisan karki damu komi ze wuce insha Allah kinji?
Kai kawai na daga masa.
Sati Na daya a gidanmu sai lokacin mutane suka rage zuwa ganina.
Yanzu na saba kullum ina tare da yayyuna da daddy muna hira gaskia naga gata. A yanzu in kunga wayar hannuna ma se kun rike baki ga kyau ga tsada kuma furniture din dakina ma kawo photuna akayi in zaba na zabi komai pink .
Bayan Na samu an zaga dani koina dangi 'yanuwa da abokan arziki.
Watarana daddy ya tafi dani gidansu gunsu ummah bayan mun gaisa dake ranar Haj Zubaida bats nan.
Anan na kwashe labarina kaf Na gayawa daddy da ummah da irin wahalar da mama tasha dani kaina.
Ummah kam kuka sosai a yayinda daddy ma idanunsa sunyi jazir tsabar tashin hankali.
Yace" ihisan duk abun nan ya faru a rashin sani .Jamila itace tayi sanadiyar rabuwarmu duk da bana son tuna abunda ta yi tunda tana kwance a kabarinta yanzu.
Bayan tfyrku da mahaifiyarki ban sake gane inda hankalina yake ba komai sai abinda Jamila tace ko nan gidan na daina zuwa gaida umma saida suka shiga yi mun addua sosai .an dauki tsawon lokaci kamin nan Allah ya kawo karshen abun a in da Jamila ta fara rashin lfy wasa wasa har ta kwanta mun je asibitoci ansha yi mata aiki amma ina abun ya gagara haka muna ji muna gani cancern jikinta yayi chronic .
Jamila ta tabbatar ciwonta bana tashi ba shine fa ta fadi dukkan abinda ta aikata kuma ta nemi gafara a in da tace don Allah ko bayan ranta in nemo amina don ta yafe mata da zaluncinda ta mata.
Bayan rasuwar Jamila Ihsan hankalina yayi matukar tashi musamman in na tuna yanda na rabu da mamanki.
Na tafi Kaduna da kyar na gane gidansu amina saboda anguwan ta kara cika da gine gine amma abin mamaki gidan nan na yayyun mamanki na samu ya kone sakamakon wutan NEPA da aka kawo da karfi.
Nan mutanen anguwan suka tabbatar min da kowa na gidan babu Wanda ya fita da rai.
Hankalina yayi mummunar tashi Wanda tun a lokacin na kamu da hawan jini nasha jinya sosai Wanda ya dauki tsawon lokaci kamin na warke amma zuciyata ta kasa hakuri sai da na kuma dawowa Kaduna da photon mamanki ina nemanta anan ne na fahimci ba Ku ne a gidan lokacin da akayi gobara ba don da nayi bincike sosai na tabbatar 'yan hayane ma a gidan .
Amma abun mamaki kowa na nuna Wa photon mamanki sai suce basu Santa ba.da yake Allah baiyi zamu hadu ba har kanon ma naja don ta taba bani labarin cewa su kanawa ne.
Dole na sawa raina dangana na shiga adduan Allah ya bayyana mun Ku.
Bayan rasuwar Jamila da shekara biyar ne na auri rukayya mutumiyar kirki tana da hankali da biyayya sai dai Allah bai bani haihuwa da ita ba
Bayan shekaru kadan shine maimartaba yabani auran 'yarsa Sameera .
Ya numfasa ya kalleni yace ' ihisan kinji irin abubuwa da suka faru bayan barinku garin nan da mamanki.
Ni da ummah duk kuka muke.
Anan na share hawayena na shiga baiwa ummah hkr ina nunan mata komai ya wuce yanzu kam.
Anan daddy ya barni ya tafi. Kwanan biyu a gidan snn driver ya maidani gidanmu.
Nan na tarar tuni an gyara min dakina tsaf komai sabo dal kuma komai pink ne da white har toilet .
Gaskia naji dadi ba kadan ba naje nayiwa daddy Godiya .
Murmushi yayi yace" Mamana banda wani buri a rayuwa da ya wuce in faranta miki rai karki damu wnn kadan ne daga cikin abinda na miki tanadi.ihisan duk abinda kk so kizo ki sanar dani inshaa Allah zan miki
Nace " nagode daddy Allah ya saka maka da gidan aljannah.
Yace "ameen Mamana yanzu abinda nake so dake shine ki tayani addua sosai domin ina son in dawoda mahaifiyarki sai dai kinsan ba karamin aiki bane ta yarda dole sai mun dage da addua.
Cikin jin dadi nace " insha Allah zata amince daddy .
Yace "Allah yasa.
Nace " ameen daddy .
Yace "akwai hotunan motoci a wurin hafiz ya nuna miki ki zabi wacca kk so.