← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 128

Sashe 57

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihana da tun dazu take zaune shiru tana kallonsu da abun ya isheta fita ta yi don in ta kuskura tasa baki zaginta zasuyi .don inna kwanaki har cewa ta yi zata tsine mata akaina ni da mama kawai dan tana goyan bayan gaskia.

An gama jere kam masha Allah sai Wanda ya gani domin daddy yayi rawar gani gun hado min duk wani kaya na more rayuwa domin duk kayana ma ba anan aka saya ba.

Kayan kichten kuwa har anso ayi rigima akansa domin mama ta ce gabadaya kitchen dina kayanda ta saya min za,a jera su aunty sa,a sukace bazaiyiwu ba ga na daddy ga na dangi ya za,ayi da su sai dai a zauna a rarraba.mama tace ai ta rigada ta fadawa daddy kar kowa ya kawo kayan kitchen har sai da aka kira daddy yace wa aunty sa,a shikenan asa kayan maman kawai nasu kuma a nemi wajan adanawa a ajiyemun.

Aunty sa,a tace " lamido ni wai me ya faru da Amina ne?

Yace " hmm ke dai Hajia bari fushin ne har yanzu taki sakkowa wlh.

Aunty sa,a tace " to gaskia zan mata magana fushin ya isa haka .

Daddy yace " toh inkinyi hakanma kin kyauta kuma kinga dama can 'yar dakinkine ke kk San yadda zaki lallasheta ta sauko.

Tace " to shikenan duk yanda akayi zakaji sai an jima.

Bayan sunyi sallama .anan sukayi yadda mmn keso .

Mu dai sai wajen 03:00 pm muka isa kano jina nake wata iri.

Cikin gida aka kaini gun su inna ko ince dakinta su goggo Ummi suka gaisheta a mutunce snn suka damka mata amanata suna" karki riketa a matsayin suruka ki dauketa tamkar yar cikin ki idan tayi ba dai dai ba kamin mu mu Sani ki dauki mataki ki nuna mata abinda ya dace .

Inna tayi murmushi tace " haba ai babu komai rumaisa ko da can ma ai a dakin nan take kafin mamanta ta dawo gidan nan ni dai banda matsala da ita kawai dai in kun karantar da ita yanda rayuwar aure yake ai shikenan sai muce Allah ya basu zaman lfy.

Gabadaya suka amsa da amin su goggo Ummi suka kara da Godiya .

Anan akayi addua aka shafa snn suka kaini kofar mama itama tayi nata nasihar dagan nan muka wuce gidana .

Wayyo Allah na koda naga na shiga jina nake kamar babu sauran matsala kuma a rayuwa .bayan nayi addua na shiga da kafar dama kamar yadda su goggo Ummi suka ce nayi.

Gaskia gidan kam ya tsaru sosai duk da dai flat din baida wani girma amma masha Allah an tsarashi yadda ya dace da zamani babban Palo ne mai daukeda coridoor uku daya dakina ne da dakin baki sai toilet a kowanne .
Snn daya kuma dining side ne sai kitchen da store .gefe daya kuma side dinsa ne Palo madaidaici da daki da ban daki sai kofar baya. Haka tsarin na ya salim yake.

Komai dai ya zauna yayi kyau masha Allah ga kamshi kota ina.

Muna dakina ni da su ruma da sakina Amarya sai aunty hadiza matar ya awwal muna hira su Sadiya suka shigo anan muka gaisa raihana tace " rumaisa anya bazan zo na tare a gidan nan ba

Mukayi dariya Sadiya kam sai yatsine yatsinen fuska takeyi.daga nan ma fita tayi ta taradda adda A'i a Palo suka shiga gulma da fulatanci wai duk zatonsu ba maiji ko da gangan sukayi don tada fitinane oho.
Sun dai sa goggo karima har ta fusata ta shiga basu amsa daga nan suka shiga sa,ainsa da adda A'i har tana cewa " in ba kaddara bama me salman zaiyi da yarku duk ta zubar da mutunci a titi...

Goggo karima tace " karyane wlh babu abinda ya taba mutuncinta dashi tazo gidan nan.

Adda Ai tayi dariya tace "aikuwa dai kam.tunda kince haka ya akayi sarki yaki auranta ? Bari kiji Hajia babu abinda bamu Sani ba akan yarku kawai ta zauna ta shirya muku karya da gaskia kun hau kun zauna .kaf garin nan waye baisan irin abubuwanda tayi ba na yawon karuwanci da shaye shaye.....

Goggo karima ta katseta da fadin " ya isheki haka ki kama hanyarki ki fita anan ...

Suna cikin haka goggo Ummi da aunty samira suka fito daga kitchen goggo Ummi ta ce " haba karima banso kk tanka musu ba wlh mene ne amfanin biye musun ne kawai ki barsu duk abinda zasu fada ma su fada .

Goggo karima tace " Ummi kina fa jin irin maganganu marasa dadi da suke fada akan Ihsan to me ta musu?

Goggo Ummi ta dafata tace " babu komai ki rabu dasu je kiyi alwala kizo muyi sallah mu wuce gun Amina.

Daga nan ta ja ta suka tafi ciki aunty samira kuwa harara ta bisu dashi ta wuce ciki.

Sadiya tayi dariya tace " kin min dai dai adda A'i.

Adda Ai tace " tukunna ma basunce yarsu budurwa bace to ni kuma wlh sai na basu kunya da ni suke zancan.

Daga nan suka fita.
Su goggo Ummi kam abun ya damesu sosai ba yanda suka iya haka suka kara min magana da insan irin zamanda zanyi dasu.

Washe gari bayan sun gama shiryawa gabadaya suka tafi Abuja.bayan munyi sallama naci kuka sosai aunty samira ma kukan ta tayani.

Sun tafi sun barni ni kadai sai daga bayane ruma da sakina suka shigo suka tattara koina suka share sukayi goge goge .mama da aunty Zuwaira da Maman sakina suka shigo don suga gida haka suka dinga yabawa daga nan fa mama suka ja min kunne kan su Sadiya don babu abinda suke so sai tashin hankali da rigima don haka kar na biye musu.da haka suka barni sakina ma mijinta yazo ya dauketa sun tafi ruma kuma ta wuce side din ta don ya salim sai damunta yake da kira tun dazu.
Zainab aka turo min don ta tayani kwana.

Duk bidirin nan ya salman shiru kakeji ko layinsa ma kashewa yayi. Duk na shiga damuwa sosai wlh .

Aunty samira kuwa sai damuna take da wadan can tarkacen wai sai dai nacigaba da amfani dasu kamin ya dawo bayan ni yanzu gabadaya abun ya min yawa har ciwon mara yake sa min.

Ya salman sai da yayi satinsa biyun nan cif snn ya dawo ba bu Wanda ya Sani sai dai ganinsa kawai akayi gidansu ya fara sauka bayan ya gaggaishesu snn ya shigo gida anan ya salim ya tsare shi da tambaya wai ina zaije ?

Kallonsa yayi cike da mamaki yace " zanje gidana gun amaryata.

Ya salim yayi dariya yace " Malam ko kunya babu.

Ya salman ya harareshi yace " kai sanda kaje gun amaryarka waya sanya maka ido.

Ya salim yace " amma ni ai rakani kukayi don haka kaima ka jira saida daddare mu rakaka kaje a siyi baki.

Tsaki ya salman yayi dole kawai ya juya side din su nada yayi wanka.

Ni dai tunda zainab ta fada min dawowarsa na kasa zaune na kasa tsaye in shiga in fita duk sai naji gabana sai faduwa yake.

Shigowar ruma ne ya taimaka min muka karasa girki bayan munyi isha ta zabo min kaya ta ajiyeni ta tsara min ado na gani na fada .

Adon da ya daukemu tsawon lokaci har suka shigo da ya salim da abokansa shima ango yasha ado cikn sye blue din gezn Wanda yasha guga ya kwanta yana sheki ga hula kuwa an sakashi yadda ya dace kamshin turarensu ya gauraye koina.

Su bakwai suka shigo .

Bayan ruma ta gama shiryani muka fara tunanin fita haka dai muka daure muka fita kaina a sunkuye na kasa dagowa shikam tunda muka fito yake kallona ya kasa dauke idonsa.

Ruma ta kaini har kusa dashi ta zaunar dani murmushi ya sakar mata yace " weldone sweet heart aikinki na kyau.

Murmushi tayi tace " thank you darling.

Snn ta koma kusa da mijinta ta zauna anan abokan ya salman suka shiga zolayarmu aka shiga tadi da dariya ni dai kaina a sunkuye fuskata rufe da gyale .

Ya salman dai tunda suke ta faman zolayarsa baiyi magana ba ganin zasu bata masa lokaci yasa shi fadin " dare fa nayi guys .

Anan suma suka mana nasu nasihar suka rufe da addua snn suka tashi zasu tafi ya salim ya ajiye ledoji a gabana yace " to ga kayan siyan baki Amarya.

Wani daga cikin abokan yaya yace" asha amarci lfy sai mun dawo barka.

Duk kunya ya lullubeni ji nake kamar in nitse kasa.

Ya salman ya tashi ya rakasu ba jimawa ya dawo shi kadai ya rufe kofan palon yasa key snn ya karaso inda nake ya zauna kamshin turarensa ya bugi hancina .

Hannun yasa ya cire gyalen da na rufe fuskata wani irin ajiyar zuciya yayi yace " masha Allah ! Amaryata .

Hade fuska nayi na turo baki alamun fushi .

Da sauri yace " o na manta fushi akeyi dani ban bada hkr ba.

Snn ya danyi murmushi yace" am sorry babyna yau dai abar batun tuna baya tashi muyi alwala muyi sallah tukun mu godewa Allah da ya nuna mana wnn ranar da muka dade muna tsumayensa.

Ya riko hannuna muka tashi a tare....

Karar buga kofa ne ya dakatar dashi ya juya hade da fadin wayene kuma ?

Nikam na tsorata duk da dai karfe sha dayane .

Yana budewa adda A'i ce ta shigo tare da sa,adatu da Sadiya.
Murmushi tayi tace sory mun zo mun matsa maka zaka shiga dakin Amarya ko?

Ta fadi hakan yayinda ta karaso gabana ta kama hannuna tana murmushi tasa min ledan da ta rike tace " to Amarya wnn farin bedsheet ne dazu na bada kudi aka siyo ki shimfida Ku kwanta akai in Allah ya kaimu gobe zan dawo inga result dinda aka samu .

Tana fadan haka ta juya suka fice .

Bai ce musu komai ba ya maida kofa ya rufe.

Ni dai tuni hawaye ya taru a idona koda ya karaso guna kamin yayi magana na juya na tafi daki da kuka..........

Hauly ce👍🏻🥰
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒
Chapter 57 · 0% Book details