← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 128

Sashe 104

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya kuwa duk ni,imar nan da take ciki sam bata jin dadi burinta ta samu dakinta itama don a halin yanzu bata da abokin shawara duk 'yan uwanta suna gidan mazajensu hatta mara kunyar nan madiha ta nitsu a gidan mijinta tun farkon auren da ta fara rashin kunya mijin ya saitata ta nitsu tsaf ta dawo hankalinta.su nabila kam tuni dama suna gidajensu.adda A'i kuma har yanzu bata wani shiga harkarsu.ga raihana da sa,adatu ma ba ruwansu da ita.dama innace mai share mata hawaye da bata kalamai to inna ma yanzu sai a slow ta daina damuwa da halinda sadiyan ke ciki.sha,ani yau da gobe se Allah.don haka komai ya dagulewa sadiya sai addua.

Watarana da mukaje gaida inna har rokon ya salman takeyi wai don Allah ya roki jafar ya maidata gidansa ta zauna da yaranta.

Wani irin kallo ya mata wanda yasa ta nitsu lokaci daya bata kara magana ba ta mike ta shige daki ko shakka banayi nasan kuka zatsyi tuni naji tausayin sadiya na ratsa ni .

Inna tace"hmm ai wnn jafar din da sadiya zata gane da ta rabu dashi don baida mutunci ko kadan amma ta kasa cire shi a ranta kullum kamar zuga ta ake.

Ya salman yace"wai inna ba abba yace min ta sami wani Alhaji hamid ba har yana so ya turo maganar aure?

Inna tace"hmm wai ita bata son mai mata da yawa tsoro takeji don haka ta hanashi turowa .

Ya salman yace" aikuwa tayi babban rashi wlh domin mutumin nan yana da hankali sosai gidansa akwai tarbiyya fiyeda yadda kk zato.bansan meyasa abba ya barta ta koreshi ba.

Inna tace to ya zaiyi da ita tunda tace batayi sadiya ai ba yarinya bace yanzu bare mu mata dole .

Shiru ya salman yayi bai kuma cewa komai ba.

Can inna tace"yawwa ya maganar dawowar shatu nan ne ? Naji sake yin shiru ?

Ya salman yace"inna kinga farida ta riga ta saba da Abuja bazata yarda ta dawo nan ba.snn salim bazaiji dadi ba shida matarsa idan nace farida ta dawo kano tunda kinga tun tana shekara uku take wurinsu .....

Inna ta katseshi da fadin "ai dama nasan zaka fadi hakan yanzu shikenan ni banida jika ko daya a gabana bsnida wanda zasu tayani hira ga rabi nan ko wani hutu sai an kawo yaran sakina da zainab sunsha hutunsu anan.amma ni kiri kiri kana gani raihana bata taba yarda ta kawo min yaranta suyi hutu sai dai wuni shi kuma jafar sai kusa kusan nan ya fara barin Abdul da Amira suna zuwa su gaishemu shima a tsassaye ko ruwa basa tsayawa sha.snn shima khalil baya son zuwa wajena bansan me uwarsa ta fada masa akaina ba gabadaya yabi ya tsaneni ....

Ya salman ya katseta da fadin "ba haka bane inna khalilullah haka nan Allah yayi shi baya sakewa da kowa komu nan ba sosai yake sakewa damu ba .don Allah ki daina daga hankalinki akan wnn.jikoki dai kici gaba da addua Allah zai kawosu suxo su tayaki hira .

A tunaninsa zata saki ranta haba ai kamar ya zugata don cewa tayi"yaushe knn zan tara jikokin tunda naga ai ku kun daina haihuwa gabadaya tunda khalil yanzu har zama saurayi shekara goma.....

Sam na lura bai son maganar don haka yace don Allah inna ki bar wnn maganar kawai kidai ci gaba da addua ke dai.

Daga nan ya tashi ya kalleni yace" rumaisa mu tafi
Tashi nayi jikina a mace muka mata sallama muka tafi a hanyarmu na komawa gida nace"yaya don Allah ka duba lamarin sadiyan nan wlh ta na bani tausayi.

Yace"hmm barta dai tukunna nafi so sai tayi laushi sosai ta gane Allah dayane snn zan shiga lamuranta .

Nace "haba yaya wani laushi kuma shekara nawa tana fama?ai yanzu in ka lura sadiya ta shiryu ta daina shiga tsabgar kowa matsalarta kawai ta samu tayi aure ta huta kamar kowacce mace.don Allah yaya ba dan halinta ba ka taimaka ka duba lamarinta kasa baki.....

Yace"naji zan yi tunani akai baby shikenan.

Murmushi nayi nace"yawwa yayanah ko kaifa?

Bai kuma yin magana ba har muka isa gida mun sami khalil ya dawo islamiyya na kalleshi cike da kulawa nace"daddyna innah tana gaisheka kuma wai tana missing dinka sosai kamata yayi gobe sunday sai kaje ku wuni har lokacin tfyn islamiyya sai ka dawo.

Hade fuska yayi yace"ni momy bana son zuwa gidansu innah ta cika son fada.

Yana fadin haka ya juya ya tafi ciki ya barmu.dagani har ya Salman binsa mukayi da kallo nace"hmm dama ai khalil kam baya son mutane bansan ya zanyi dashi ba.

Shidai baiyi magana amma na lura baiji dadin maganar khalil ba duk da ma yasan matsalar daga wurin innan ce tana son jikoki amma bata iya bi dasu a hankalli ba.kullum adduarsa akan innah yafi yawa saboda halayanta.burinsa bai wuce yaga inna ta daina halayanta marasa kyau dinnan.

ABUJA

Farida kuwa tunda suka fara zuwa secondary itada mimi sun kara wayewa sun zama big girls gashi Allah yayi su da girman jiki musamman ita farida don haka tuni ta fara jan hankalin samari duk inda ta shiga sai ta sami saurayi .tun bata kulasu yau da gobe har ta fara gane meye soyayya don haka tun tana jss 3 ta fara tara samari sabanin ita mimi bata yarda da wasu samari karatunta kawai tasa a gaba kuma tafi farida hankali da nitsuwa nesa ba kusa ba duk da farida ta fita ilmi sosai.

Ruma kam hankalinta ya tashi sosai da irin halayen farida domin a yanayinda ta karanci halin farida da dabiunta duk irin bangarensu innane.(Allah mai iko)da farko taso ta boye min amma daga baya taga babu amfani gara ta sanar dani.
Hankalina ya tashi sosai don nima din naga alamu da tazo wani hutu gabadaya hankalinta na kan charting da samari maganar makaranta kuwa bata kaunar mimi ta kawo mata.kamin su gama hutu su koma sai da na kwace wayarta na kuma cewa ya salim kar ya kuma barinta ta rike waya sam sam.

Na sami mama da maganar na fada mata komai tace"hmm ai dole ne farida ta dauki halayansu sadiya rumaisa jini fa ba wasa bane.ni banga abin damuwa sosai anan ba addua ce kawai zaku rika yi mata hade da maida hankali akan duk wani lamarinta insha Allah babu abinda zai faru da ita su sadiyan ma da kk gansu hakan harda rashin samun tarbiyya ne tun farko shatu ta riga ta batata da mugayen dabiunsu gabadaya kuma danginsu haka suke basa lura da tarbiyan yaransu shiyasa suka tashi a haka.amma ita farida idan har kuka tashi tsaye a kanta da addua in Allah ya yarda zata shiryu tsaf har kiyi mamaki .

Nace"to Allah yasa wlh gabadaya na shiga damuwa mama har bacci bana iyayi sosai.

Tundaga lokacin na zage wajen yiwa farida addua sosai a hankali kuwa sai abin yayi sauki da ikkon Allah domin ruma tace min yanxu ta daina kula samarinkuma ta maida hankali gun karatunta.dadi naji sosai na godewa Allah!

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡91

*******Duk abin nan dake faruwa na matsalar farida ban taba gayawa ya salman ba sanin halinsa har Allah yasa ta daina.Alhamdulillah naji dadin yanda ruma ta gaya min farida ta nitsu sosai har tana zuwa farko a ajinsu dama ililmi kam akwai shi masha Allah.

Dama ya salim ya musu alkawarin suna gama junior waec zasu tafi umrah gsbadayansu.don yanzu ya salim yaransa biyar ne bayan munir da mimi da Salman junior akwai mohd me sunan abban salman snn Ahmad me sunan mahaifin Ruma.gsbadaya zasu tafi har da khalilullah daga can ma london yace zasu wuce don suje su kaiwa su faiza da ya munir ziyara don gabadaya munyi kewarsa nima ba don aiyuka sun ma ya salman yawa ba da mun tafi duka.

bayan sun gama aikin umrah suka tafi london ranar karkuso kuga murna gun faiza da rais da yaransu shidda suma.don haka gabadaya aka hadu aka shiga tadi cikin nishadi da annashuwa har lokacinda munir ya dawo makaranta yana ta dokin son ganin 'yan nigeria don yayi missing dinsu sosai.

yana shiga palon yaran gabadaya suka tashi suka masa oyoyo hade da rumgumeshi .

Dariya yakeyi yace"karfa ku kada ni.

Farida ce ta kalleshi cike da fara,a tace"ya munir munyi missing dinka sosai kaga yanda ka zama babban mutum kuwa gabadaya ka zama kamar uncle hakim .

Shikam murmushi yace"ai gabadaya ni kuma farida girmanki yafi bani mamaki dubi yadda kika zama 'yanmata keda na barki yar kankanuwa.

Nan da nan farida ta zumburo baki ta kama fishi akan munir yace mata yar kankanuwa harda kararsa ta kai gun daddynsu salim.

shikam munir binta yakeyi da kallo duk yanda tayi gabadaya baima san ya shagala da kallon kanwar tashi ba.

Faiza kuwa tuni ta fahimci irin kallon da munir din yakewa farida murmushi tayi hade dan gyaran murya tace"son to baka zo ka gaida su mum dinka ba .

Da sauri munir ya isa gunsu ya salim yana dan sosa keya hade da satan kallon farida wacce bata ma san yanayi ba.sai tsokanar su mimi takeyi dama ita farida gwanar tsokanace ga son fada in dai tana guri babu zaman lfy ta dinga neman magana knn.

Munir ya gaida iyayensa cike da biyaiya don bai cika sakin jikinsa dasu ba.sai ni da ya salman .anan yake tambayarsu labarinmu ya salim yace"suna ta gaisheka sunyi kewarka sosai sai dai kawai daddynku aiki ya masa yawane.

munir yace"ayya daddyna ai to daya bar mummy tazo daku.

Faiza bata san lokacinda tace "tab hmmm ya salman bazai taba bari rumaisah tayi nitsa dashi ba ai.su har yanzu basa tsufa da so........

Harara da ya salim ya sakar mata yasa takama bakinta tana dariya don tama manta yara na nan.

Farida kuwa tayi caraf tace"ai goggo bakisani ba mamana bata son inje hutu saboda indai naje daddy baida lokacinta.......

Ruma tace"kinci gidanku farida waya sako bakinki a cikin wnn zancen?
Chapter 104 · 0% Book details