← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 128

Sashe 63

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********Tuni innah ta kira Sadiya tayi mata albishir .

Sadiya tace" amma inna kinfa San Goggo Amina ba a zaune take ba in kin lura duk abinda muke mata baya ko girgizata ita.

Inna tace" hmm aini tunda naci nasara akan rumaisa to banda wata matsala .kuma wnn karon abun yafi na kullum wlh suka kuskura suka ce ta koma gidanta ina mai tabbatar miki haukacewa zatayi gabadaya yanzu abinda nake jira knn kuma nasan za,ayi haka kwanan nan.

Sadiya tace" hauka inna?

Inna tace" sosai kuwa kuma bazata taba warkwwa ba har sai an tone wadannan layu da aka binne a gidan.

Sadiya tayi dariya tace" tab Ashe zamusha kallo knn kwanan nan.

Haka inna da Sadiya suka dinga hirarsu cike da nishadi.

Da daddare ina kwance a dakin mama duk najini wata iri a cikin satin nan kasala sosai nakeji.

Sa,a ce ta shigo da sallama na amsa bayan ta gaisheni tace " aunty rumaisa yaya na kira .

Nace "yana ina?

Tace" yana motarsa a waje.

Nace " to ina zuwa .

Bayan ta fita na tashi na kintsa sosai snn na sallami mama na fita.

Yana cikin motar na shiga na sameshi yana sanye da kananan kaya wando 3 Quarter na sojoji da farin Riga sun matukar karbarsa.

Kallonshi nake ina murmushi nace " monin sir!

Fuska daure yace" me yasa tuni nake kiran wayarki baki dauka ba?

Nace " wayar na silent ne yi hkr yaya.

Shiru yayi tsawon wasu lokuta snn ya juyo muna fuskantar juna yace" yakamata zuwa yanzu kam ki dawo gida domin gaskia na gaji da zamanki a gun Goggo amina kina shiga hakkina dauriya na ya kare.

Kaina na sunkuyar hankalina tashe don bana kaunar ace in koma gidana .nan da nan na fara zubar da hawaye.

Cike da mamaki yace" don Allah meye abun kuka kuma anan yanzu.

Aikuwa sai na fashe da kukan nace" yaya wlh bana son komawa gidan can tsoro nakeji.

Yace" amma ai na fada miki ba komai koh?

Shiru na masa naci gaba da kukana.

Jikinsa ne yayi sanyi ya jawoni sosai ya rumgumeni hade da goge min hawaye yace" shikenan kiyi hkr ki bar kukan bazan tirsasa miki ki dawo ba amma don Allah nima a tausaya min hkr na ya kare.

Ya fadi hakan yayinda ya shiga shashshafani yana sauke numfashi da kyar ya lumshe idonsa da suka fara canza launi

Ni kuma uwar sonjiki dada lafewa nayi a kirjinsa idona lumshe nace " yaya mota ne fa.

Dago fuskata yayi cikin wata kasalalliyar murya yace " hmm baby nayi missing dinki sosaine bazan iya hkr ba gaskia.

Yana fadin haka ya hade bakinmu gu daya ya shiga sarrafani son ransa.

Ganin yana kokarin zarcewa yasani fadin" yaya ka bari motane fa za,a ganmu.

Da kyar ya sakeni idonsa tuni ya kada yayi jaxir ba tare da yace mun komai ba ya tashi mortar muka bar kofan gida.

Nima jikina a mace ban kuma ce mishi komiba.

Mun danyi tfy kawai sai gamu a wata hadaddiyar hotel mai ktau da tsarin gaske.

Bayan mun gama parking muka sauka yana rike da hannuna muka tafi yaje ya biya kudin kwana .

Muna zuwa dakin bai tsaya sauraran komai ba yayi kan gado dani ni dai ranar ina ganin ikon ubangiji.

Yau ma naji jiki da kyar ya saurara min sai lokacin hankalinsa ya komo jikinsa dai dai .

Bayan munyi wanka ne muka kwanta amma duk wani motsi sai ya kawai ya sake jawoni kwana mukayi muna abu daya.saida mukayi sallar asuba muka fara rama bacci.

Sai sha daya muka tashi mukayi wanka nikam komawa nayi na kwanta kasala nakeji sosai .na lumshe ido sanyin AC na ratsani.

Kallona yayi fuska sake yace " baby me zakici ?

Na danyi juyi nace " yaya black tea kawai zansha.

Zama yayi kusa dani yace" haba baby tun jiya da daddare bakici komai ba fa me yasa baki son cin abinci to?

Kwanciya nayi a jikinsa nace" yayana wlh bana son cin komai ne.

Yace" pls ki daure ko kadan ne kici kinji?

Na daga mishi kai.

Bayan mun gama karyawa muna shirun dawowa kawai na fara jun tashin zuciya sai amai ya biyo baya nayita kwarawa anan ya salman ya dinga min sannu Wanda daga bisani asibity ya kai ni a in da aka tabbatar mishi da ina da shigar ciki na wata daya .

Wai karkuso kuga murna kamar yayi yaya da ransa ko motsi kwakkwara ya hana inyi haka ya dinga dawainiya dani har muka dawo gida ba kunya ya fadawa mama komai.

Don haka minti minti yana kofar mama har ta gaji tace " maza in tattara in bishi ita ta gaji da ganin rashin kunyarmu.

Ba don raina yaso ba na bishi gabana sai faduwa yake .

Aikuwa na gudu ban tsira ba don muna isa gidan bakina yaki budewa inyi addua gabadaya naji tsigar jikina ya tashi na fara jin gidan gabadaya yana girgiza dani anan na yanki jiki na fadi sumammiya .

Ya salman kam ya gama rukicewa rumgune yayi yana kiran sunana .

Ni dai vankuma sanin ina kaina yakeba sai .........

Hauly ce🥰👍🏻
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡58

************Saida na shafe sati guda ba tare da nasan ina nake ba .

Babu ci babu sha babu magana ba bacci kuma da ido kawai nake bin kowa ko an kira sunana ban amsawa ban ma San dani ake magana.

Tun ranarda abun ya faru asibity aka kaini amma basu gane komai ba suma in banda drip ba abinda suke sa min.

Hankalin ya salman da mama ya tashi matuka mama ta kasa daurewa sai kuka take yi ba dare ba rana addua kuwa bata fasa ba.

Daddyna da aka sanar mishi yace kawai a fita dani kasashen waje mama tace masa wnn ba case din asibity ba addu a kawai shine mafita .

Anan daddy ya ware kudi masu yawan gaske akayita saukan Qur,ani dare da rana ba fashi ana kuma sadaka .

Duk wani masoyina in yayi Sallah sai ya min addua.ya Salman har ya rame ya rasa me ke masa dadi a duniya ko abinci bai iya ci gashi ya koma bakin aikinsa don hutunda ya dauka ya kare.

Tuni aka sallameni na dawo gida anan ake ta dawainiyar saka min drip.

Mama kullum tana gefena tana zubar da hawaye .ta yaya ma zata iya wani aure a yanzu ta tafi ta barni wa zai kula dani ? Da ta fara shawaran amincewa ta koma gidanmu amma ganin har yanzu rayuwata tana cikin matsala yasa ta fara tunanin ta hkr da komai zata zauna kusa dani domin ta bani kulawa.

Tana cikin wnn tunani sa,adatu ta shigo ta gaisheta hade da fadin Goggo ya jikin aunty Rumaisa.

Mama ta dan goge hawaye tace" da sauki sa,adatu.

Zama tayi shiru na tsawon wasu lokuta snn tace " Goggo in Allah ya yarda aunty rumaisa zata sami lfy domin yau na tone wnn asirin da aka mata Wanda ni aka baiwa naje na binne da hannuna a cikin gidan can...

Sakin baki mama ta yi tana kallon sa,a cike da mamaki duk da tasan komai ma zasu iyayi.

Mama tace" yanzu sa,a kina nufin kinsan abinda ke faruwa da rumaisa ko ince da hadin kanki aka mata ? Meye tai muku ne don Allah me yasa kuka cutar min da ita ki fada min ?

Sa,adatu ta girgiza kai tace " Goggo ni ma bansani ba su innah ne suka bani wani fai fai zagaye da layu adda Ai ne ta kawo daga kamaru lokacin da su aunty rumaisa suka tafi yola shine innah ta bani tace inje in binne maganin tsarin gidane na karba na binne amma wlh ba don nasan na miye bane duk abubuwanda ke faruwa da aunty rumaisa hankalina bai zo kan layun nan ba amma tun shekaranjiya nake mafarki akan wnn abu dana binne shine yake da alaka da rashin lfyn aunty rumaisa to shine ban yi shawara da kowa ba na je na tone sai na boye a bayan flowers anjima zan kawo maki ki gani.

Mama ta share hawaye tace" nagode sa,a tabbas kin cika 'yar halal bansan da wasu kalmomi zan yi amfani dasu wurin gode miki ba.

Sa,a tace " ba komai Goggo sai dai Dan Allah ki rufan asiri karki bari su inna su Sani ko yaya ma ban son yaji don Allah Goggo wlh idan suka Sani zan shiga damuwa.

Mama tayi murmushi tace " bazan fada musu ba sa,a suje su da Allah kuma salman ma bazan bari ya Sani ba sai lokaci yayi da kansa zai gane komai ni dai fatana samun lfy rumaisa.

Sa,a tace " inshaa Allah Goggo bari in tafi kar inna ta nemeni.

Mama ta gyada mata kai tace " shikenan sa,a na gode.

Da daddare sa,a ta tafi ta dauko wnn faifan me zagaye da layu ta kawowa mama cikeda tsoro mama take bin faifan da kallo a ranta kuwa tana fadin" anya shatu na tsoron ubangijinta? Kai amma jahilci baiyi ba a rayuwa .Tabbas addua bata faduwa kasa banza Allah ne ya karbi adduoinda aka dinga yin min.

Tare da sa,a suka zagaya dashi bayan dakunanta suka zuba masa kero suka kyasta ashana amma abin mamaki har keron ya kare layun nan ko gezau gara ma faifan ya kurmushe don haka mama ta yanke shawaran gobe zata je ta jefa a ruwa.

Ikon Allah knn a Daren hankalina ya soma dawowa Jikina lokacin na fara tuna abinda ya faru dani sanda muka koma gida da ya salman amma banda wnn ba abinda na iya tunawa kuma sai kuma ganin mama da nayi yanzu tana sallah na duba agogo karfe biyun dare ne.

A hankali na tashi zaune sai lokacin na lura da drip da aka samin nabi ruwan da kallo cike da mamaki.

Mama kuwa tana sallama ta mike da sauri ta karaso inda nake rumgumeni ta yi ta fara hawaye tana Alhamdulillah.

Jikina a mace nace" mama mene ne ya sameni?
Chapter 63 · 0% Book details