← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 128

Sashe 23

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk tunani na ko inna bata dawo ba ashe ta dawo ina ganinta saida zuciyata ta buga. Don tunda ake rikicin nan bamu hadu ba.

Ga mamakina sai naga cikin fara,a tace min rumaisa yanzu kk tafe?

Cike da mamaki nace" eh inna.
Na Dan russuna na gaisheta har da tambayata ya makaranta nace lfy.

Tace"jeki ciki sadiya na nan.

Nace" to.

Na wuce daki a raina ina hamdala an shawo kan inna yanzu kam bamuda matsala.

Na sami sadiya tana ba Abdul nono itama dai ba yabo ba fallasa ta min magana har mun gaisa don a karshe ma tare muka ci abinci.

Ban taba jin dadin weekend a gida irin na wnn karon ba sadiya har kitso ta min dake ta iya irin kitson 'yan kamaru kanana masu kyau.ina rike da Abdul.

Bayan mun gama tace"wnn kitson gaskia yaya yazo biyani?

Nace" kar ki damu zan gaya masa ya biyaki.

Na kwantar da Abdul nace" bari tunda yayi bacci inje in karbi inna.

Tace" to.nima bari inyi shara inzo inyi wanki.

A kitchen na sami inna tace"har kun gama?
Nace " eh wlh munyi sauri ai.nazo in karbeki ne kije huta.

Tace"ai na gama ma yanzu saidai ki debo kwanuka muzo mu kwashe tuwo.

Nace" to.

Tare muka kwashe na kai na Abba na dawo na tattara sauran na share kitchen .

Da safen Monday tuni na shirya tsaf nayi break fast ina shirin fita inna ta fito daga daki ta mika min wani dan roba kamar na Robb tace" ga wnn rumaisa maganin sanyi ne kina shafawa in kinzo kwanciya in Allah ya yarda zaki ji saukin toshewar da kirjinki keyi.

Na karba ta sake mikawa sadiya irinshi tace" ke ma gashi kina shafawa yaron nan sakacinki yasa duk yaro ya kamu da sanyi tun bai kai ko ina ba.Allah dai ya bamu lfy naji suna yabon maganin a garinmu sunce hadine na man kadanya nima zan gwada ko kafafuna zai warke.

Sadiya ta bude ta sa a hanci tace " eh inna man kadanya ne amma anmasa wasu hade hade kamar da tafarnuwa ma.mun gode wlh zamu shafa kwanan nan duk dama mura yakeyi.munsha magani har mun gaji sai dai yayi sauki.

Inna ta ce" ya dai rage naku in kunga dama Ku jefa a jaka kar kuyi amfani da shi ni dai na baku.

Nayi dariya nace" aa inna wlh zamu shafa .mun gode.

Daga nan mukayi sallama naje na sallami Maman sakina ma na fita.

A lokacinda muke exams mama suka dawo jikin Alhaji aminu yayi sauki naje na dubashi amma gaskia ya rame sosai .

Sati daya da komawata makaranta mama ta kirani a waya yanayinda naji muryarta na tabbatar ba lfy bace nace" mama ya jikin Abba ?

Tace" rumaisa abbanku ciwo ya warke baya bukatan komei sai addua.

Dam! Naji zuciyata ya buga na bude baki zan yi magana sai kawai ga hawaye.
Na sauke wayar na dafe kai hawaye na zuba .bansan me yasa ba tun da naje naga jikinsa satin can hankalina yaki kwanciya ban gamsu da saukin da sukace ya samu ba.don yanzu ma shirin tfy gida nake inje in sake dubo shi.

Allah sarki Alhaji Aminu Allah ya jikansa da Rahma yasa aljannace makomarsa don kuwa mutum ne na mutane tsakaninsa da kowa fatan alkhairi duk arzikinda Allah ya bashi baya kyamar mutane talaka da mai kudi duk nasane kuma yayi fice wurin taimakon Alummar annabi.

Karar wayatace ta katseni na duba sai naga ya salman ne na daga masa sallama.

Ya amsa hade da fadin "daga jin muryarki nasan ba lfy waya tabo min ke?

Nace" babu komai yaya saidai yanzu mama ta kirani take sanar dani Abba ya rasu........

Ya tari numfashina da fadin" what!!!! Alhaji aminu ya rasu ? Yaushe?

Na goge hawaye da ya zubo min nace" yanzune tunda kaima bakaji ba.

Yace"naga missed calls na goggo Amina nima sai dai na kira kuma bata dauka ba.Allahu Akbar Allah ya jikansa da Rahma.

Nace "amin.

Daga nan ya min sallama shima jikinsa a mace.

Nima da sauri na saka hijabina na tafi.

Tuni an cika kofar gida da cikin gida makil da jama,a.

Mama kam kam kamin akaishi ma zazzabi ya rufeta ruf ko motsi bata iya yi tsabar tashin hankali.

Yaransa na kusa duk sunzo na nesan ma wasu sunzo.

Aka shiryashi akayi masa sallah aka kaishi gidansa na gaskia

Iyalanshi sun shiga cikin damuwa na rashinshi sai dai ayi masa addua Allah ya jikansa da Rahma.

Sati biyu da rasuwarsa sai a lokacin mutane suka watse .amma har lokacin mama ta na kwance sai dai ta danji sauki .

Mun gama exams don haka na tattara na dawo gidan mama don ba kowa a gunta sai mai aikinta ga takaba.

Dawowata ya dan rage mata damuwa da kewa .

Ranar muna zaune muna hira nace" mama yanzu in kun gama takaban gida zaki koma?

Tace" dole na ai ya zan yi?

Nace" mama yanzu inna ta daina halayenta Mara kyau ai ta tuba.

Dan murmushi mama ta yi sannan tace" hmmm ki dai bi a hankali kar ki saki jiki da ita ni ban yarda da ita ba har yanzu.

Nace" mama kawai ki zauna a sashin daddy tunda ba kullum suke zuwa ba.

Tace" eh shima yayan haka yace sai dai gaskia ni na yanke shawaran dan filina da suka bar min a cikin gidan zan gina nawa zan fi sakewa da kayaiyskina.don ban cika son takura ba.yanzu tuni ma nayiwa ya Mohd maganar kuma na tura kudi a fara aiki.

Nace" to Allah ya taimaka.
Tace "amin
Daganan shiru mukayi.

Ina shirin shiga kitchen sai ga wayar faiza wai gasu nan a kano itada sakina sun fasa tfy Hutu Abuja nan zasuzo mu zauna da mama.

Nan da nan na hau murna na wuce kitchen ina fadin " kai faiza uwar surutu zata zo.

Gaskia hutun ba laifi har muka gama ba wani tashin hankali.mama kam zuwa yanzu tuni sun saba.

Mun dawo makaranta sai dai Sam ban gamsu da yanayina ba.ina yawan jin ciwon mara sannan ciwon kai.

Haka naje asibity aka hada dubani wai ko infection ne aka rubuta min magani na saya na sha amma kamar a banza saima abinda ya karu ciwon mara har da kyar nake iya tfy.

Don haka na yanke hukuncin zuwa gun doctor Hakim tun bayan rabuwarmu yau sai gani a office dinshi cikin fara,a ya karbeni sama sama muka gaisa anan na fara mishi bayani yanayinda nake jin maran da kuma......

Ganin nayi shiru yasa shin fadin" kar ki boye min komai saboda insan irin treatment dinda zakiyi ki daure ki fada min.

Kaina a sunkuye cikin jin nauyinsa da kuma kunya nace" ina yawan jin sha,awa sosai har na kanji wani lokacin kamar na je na nemi........

Na kasa karasawa saboda kunya.

Ya numfasa yana kallona sannan yace" na fahimceki rumaisa kuma in sha Allah zamu shawo kan matsalarki kar ki damu.

Naji dadin maganarsa nace" na gode Doctor

Anan shima ya rubuta min magunguna yace in dawo after 2 weeks

Hakan kuwa akayi bayan sati biyu nakoma yace min yaya meye labari.

Nace"alhamdulillah ciwon Mara yayi sauki sai dai faa wancan har yanzu sai abinda ya karu.

Ya danyi shiru ya zuba min ido can yace"to yanzu kinsan ya za,ayi ki yawaita azumi kawai kuma ki dinga yawaita istigfari a kowani lokaci sannan daga karshe ina mai baki shawaran ki sami miji kiyi aure kar ki jefa rayuwarki a halaka.kina iya tfy.

Na mike a sanyaye gabadaya naji ba dadi don na lura doctor hakim ya fara min kallon 'yer iska don haka na yanke shawaran bazan kuma zuwa asibity ba.

Sai sai kuma na kasa yin azumin hasalima sallar ma yanzu ba son yinta nake ba wasa gaske rayuwata ta sauya gabadaya cikin kankanin lokaci.

Na kasa hkr da yanayinda nake ciki.don haka dolene in samawa kaina mafita.

Wayata na lalubo na kira Ahmad ringing biyu yayi ya daga yace" Queen lfy cikin wnn Daren.

Nace" hmm aina kk naji hayaniya .

Yace" wlh yanzu nazo club.

Nace " to don Allah kazo ka daukeni ina gidan saurayin Maryam da ka taba zuwa ka daukeni dinnan ka gane?

Yace" eh na gane amma me ya kaiki gidan keda ya kamata ace yanzu kina hostel.

Nace " eh wlh tunda muka gama lectures tace na rakata shine faa kaga suka shanyani ......

Ya katseni da fadin ganin nan zuwa

Nace"to
A raina kuwa dadi naji sosai maryam ta kalleni tace" 'yar rainin hankali gara da kika samawa kanki mafita wlh don kinga ni yanzu in baby ya dawo daki zamu wuce sai dai ince miki sai da safe.

Shiru nayi ina dafe da kai
Ahmad koda yazo waya yayi min yace gashi nan da sauri na suri jakata Maryam nace min sai mun hadu a school Queen.

Tuni na fita na sami Ahmad tuni na fada mota nace " king wlh ina cikin wani yanayi na damuwa .

Yace " ai na gani tun jiya ki gaya min menene kina da kamata bai kamata ki shiga damuwa ba Queen .

Nace,wlh nima ban San meye bane kawai in dai kana da maganin damuwa ka bani.

Ya danyi shiru sannan yace" yanzu ki yarda mu tafi night club dinnan kawai zaki ji duk damuwarki ta yaye ki samu kiyi rawa.....

Na katseshi da fadin muje kawai .

Yayi murmushi cikin jin dadi yace,thaz my Queen.

Ya tashi mota.wai yau sai ga RUMAISA a NIGHT CLUB.

Ganin Sam ban saki raina ba yasa shi fadin ina zuwa .ba jimawa ya dawo daukeda kwalba ya zauna hade bude kwalban ya zuba a Kofi ya mika min yace" karbi wnn kisha zaki ji zan zan har ki gode min .

Na yatsuna fuska nace" meye wnn ?

Yace" maganin damuwa ne da hayaniyar duniya kinasha zakijiki cikin nishadi da annashuwa.

Na sa hannu na karba ina kallonsa.

Ya daga min kai hade da fadin " sha zaki ban labari.

Na kai baki na Dan kurba wani dandano ne na tashin hankali naji kan harshena ba shiri na xubar a kasa nace" Ahmad me ye wnn babu dadi.

Dariya yayi yace kin taba jin magani mai dadi?
Chapter 23 · 0% Book details