← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 128

Sashe 46

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro ido nayi nace " duk ni kadai daddy?

Murmushi yayi yace"kwarai da gaske Mamana ai komai na miki ban fadi ba yanzu lokaci ne da zaki ji dadi sosai a rayuwa kema.

Godiya na dinga zuba masa.

Anan aunty samira ta shigo ta samemu tace " ihisan dinkunanki sun dawo muje ki gwada duk Wanda bai miki ba sai a mayar.

Ni dai yanzu kam na ma rasa mai zance sai dai Alhamdulillah Allah.

Hotuna na dunga yi ina turawa mama dasu faiza don ina waya dasu sosai .

Hutunmu ya kusa karewa yanzu kam gaskia ba don mkranta da mama ba banga abinda zai maidani kano ba.

Naci kwalliyata mai rai da lfy ina kwance kan makeken gado na ina ta hira da faiza da sakina a watsapp don group muka bude mu uku kawai muna zuba iya shege son ranmu.

Ya samir ne ya shigo da sallama .

Na dago ina murmushi nace "yaya har ka dawo?

Yace" ban tafi ba sai anjima yanzu dai ki aje wayarki ki tashi kizo muje kiga wani surprise .

Murmushi nayi na tashi hade da fadin " ni dai dadi zai kashe ni yaya bayan jiya ma kabani surprise din motata data karaso.

Hannuna ya kama hade da fadin " zo muje ke dai.

Muka fita da sauri a harabar gida ya min nuni yace " kinsan waye wancan?

Na kalli inda ya min nuni rass naji gabana ya fadi anan na fara murza idona don in tabbatar da abinda nake gani.

Har yanzu shi nake gani da sauri na juya da nufin inyiwa ya samir magana amma sai naga wayam babushi.

Wayyo to ko mafarki nakeyi?

Ina tsaye kamar gumki har ya karaso gabana.

Da kyar na iya budan baki nace " yaya Kaine?

Ba zato ba sammani naga ya sakar min murmushi hade da gyada kai yace " kwarai kuwa nine rumaisa.

Mamaki ne ya cika ni sosai wai ya salman ne a gidanmu to waya nuna masa kuma mai ya kawo shi?

Ban Sani ba a fili na fadi maganar.

A hankali ya amsa min da fadin " rumaisa meye tunaninki ? Kina ganin zan iya rayuwa ba tare da ke bane?

Ya danyi shiru snn yace " rumaisa bazan taba iya rabuwa da ke ba so duk India kk shiga a fadin duniya sai na nemoki .

Ni dai tsabar mamaki ban iya cewa komai ba .......

Hauly ce👍🏻🥰
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡40

*********Ganin shirun yayi yawa yasa shi isa dab dani yace" Rumaisa kinyi farin ciki da ganina?

Murmushi nayi nace " kwarai da gaske kuma na yarda da abinda kace yaya .

Ya danyi murmushi yace " to baki min sannu da zuwa ba.

Russunawa nayi na karbi jakar da ya rataya ina murmushi nace" yaya barka da zuwa.

Na fada yayinda na rataya jakar nace " mu isa ciki......

Ban gama rufe bakina ba naga mai gadi ya bude kofa motar daddy ne ya shigo.

Da sauri na kalli ya salman nace" kaga ma ga daddy ya dawo.

Ya juya ya kalli motar ba tare da yace komai ba.

Bayan driver ya gama parking ya sauko da sauri ya budewa daddy kofa.

A yayinda muka karasa nida ya salman .

Murmushi nayi nace " daddy sannu da dawowa.

Shima murmushi ya sakar min yace yawwa mama na .

Ya salman ya Dan russuna ya fara gaida daddy.

Ya amsa fuska sake nace " daddy yaya salman ne .........

Cikin fara,a daddy yace" Masha Allah dana sannu da zuwa.

Ya fadi hakan ne yayinda ya rumgume ya salman yace" naji dadin zuwanka kwarai dana.

Snn ya kalleni yace" mamana yanzu ne zuwansa.

Nace" eh.

Yace OK to muje ciki ai ya kwaso gajia.

Suka wuce yana rike da hannun ya salman kamar wani yaro karami.

Ina biye dasu a baya dariya nake musu kasa kasa don na lura ya salman nauyin daddy yake ji sosai baisan daddy kan ba ruwansa ba .

Har palonsa muka shiga yace " ihisan kira min Sameera .....au gata nan ma.

Aunty samira ne ta shigo taci kwalliya cikin less mai tsadan gaske tana zuba kamshi .

Ta karaso wajanmu tana murmushi tace." Sannu da dawowa ranka ya Dade.

Daddy yace " yawwa gimbiyar mata.

Ta sake fadada murmushi snn ta kalli ya salman tace" sannu da zuwa bako mukayi?

Daddy yace " babba ma kuwa .wnn da kk gani surukinkine .

Aunty samira ta kalleni da alamun neman Karin bayani gyada mata kai nayi nace " ya salman ne aunty.

Murmushi ta yi tace" da kyau 'yata.

Anan suka gaisa daddy yace "kindai shirya dining koh ?

Aunty samira ta ce " sosai ma alhaji

Yace " to kira rukayya tazo ta gaisa da surukinta kafin muci abinci.

Tace " to"

Ta fita da sauri ni dai Sai murmushi nske tayi tun dazu domin naji dadin zuwan ya salman kwarai .Allah sarki so duk abin nan da ya faru a baya amma gashi lokaci guda na manta.

Bayan an gaggaisa daddy yace " inje da ya salman dining yaci abinci kamin nan shi zaije ciki.

Duk sun watse suka barmu mu .

Ya salman yace " Rumaisa gaskia na tayaki murna haduwa da mahaifinki da 'yan uwanki.mahaifinki mutumin kirki ne hakama 'yan uwanki Masha Allah!

Murmushi nayi nace " yaya na gode ya kabar mutan gida ina su kawu ya Mamana?

Yace " duk suna lfy Sai dai ban fadawa kowa nan zanzo ba so ba Wanda yasan nazo gunki.

Nace " to waya baka address din gidan nan?

Yace" tuntuni goggo Amina ta sanar dani .

Nace " ikon Allah yaya naji dadin ganinka kwarai da gaske .domin ko kadan bana jin dadin fushi da kakeyi dani duk naji kano ya fitan min a rai.

Na karasa fada kaina a sunkuye shiru yayi baice komai ba .

Jikina a mace nace" yaya don Allah ka yi hkr nasan abinda nayi bai dace ba kuma ya kauce amma wlh yaya nima bansan me ya faru dani a wancan lokacin ba har........

Hannu ya daga min tuni yanayin fuskarsa ta sauya yace,don Allah ki bar wancan maganar ya wuce a wurina kuma ni ba na fushi dake kawai ina bakin cikin abinda ya samekine.amma komai ya wuce insha Allah gani na dawo gareki da soyayyata zan Dora daga inda na tsaya.

Sunkuyar da kai nayi cikin jin kunya sosai nasa hannuna na rufe fuskata.

Dan murmushi yayi ya taso ya isa gabana ya dan rankwafo a hankali yace " baby tsantsar so nake miki zallah bazan taba iya rabuwa da ke ba .abinda ya faru baya kaddarace baki isa ki tsallaka ba amma ina son ki Sani ni salman ke nake so ba Gangar jikinki ba !!!

Maganarsa ta karshe ta matukar girgizani har na dago ba shiri na kalleshi dama zarginda ya salman ke min knn?

Ganin fuskata ta sauya yasa shi fadin " no kar ki damu abinda Na gaya miki gaskia ne har cikin raina.

Murmushi na sakar masa nace " yaya Na gode tabbas ka cika masoyi na gaske .ni kuma duk randa ka aureni zan baka babban *SURPRISE*

Na karasa fada ina murmushi shima fuska sake yace " Allah ya nuna mana rai da lfy *IHISAN* 'yar gatan daddy

Dariya nayi nace " kai yaya .to muje kaci abinci ka samu ka huta.

Yace " ai ba gajia tunda jirgine Abuja to yola ba nitsa.

Muka isa dining na gyara mishi wurin zama ya zauna hade da fadin " thank you.

Ruwa mai sanyi na dauko a fridge na zuba masa a cup snn na mika masa ya karba .

Nace " to yanzu me za,a zubo maka tuwon semo miyar kuka ko jallof da peppe chicken ko dai pepe soup na rago zan zubo maka akwai kuma snacks.

Tunda na fara magana ya zuban ido har na gama baice komai ba sai kallona kawai yakeyi.

Da sauri nace "au afwan yayana nasan kafi son tuwo musamman semo da miyar kuka ko kubewa.

Ya saki fuska yace " ai na dauka ko kin manta abubuwanda nafi so ne?

Na ce " tab na isa ?

Na fada ina murmushi na dauko plet na masa serving tuwon semo miyar kuka da yasha naman rago ga daddawa da man shanu .gaskia mutanen yola sun cira tuta wajan dafa miyar kuka .

Ya salman yaci sosai don ya yaba miyar sosai har yace min " gaskia girkin nan yayi ki koya sosai ina so.

Nayi murmushi nace to.

A yayinda yake wanke hannunsa na mika masa tissue nace " amma yaya bakaci da yawa ba fa in kara maka mana.

Yace" what! A gidan surukai fa nake kuma ma am OK nagode sosai.

Nace " to muje ka huta ya samir Na jiranka in yaso da yamma Sai muje gidan galadima.

Muka fita Na kaishi gun ya samir don ya samu ya huta.

Ni. Kuma na dawo dakina Na fada gado zuciyata cike da farinciki nan na fara tunanin me zanyiwa ya salman in Dada burgeshi domin ina matukar ji da *SOJAN* nan nawa.

Aunty samira ce ta shigo ta sameni.

Bayan ta zauna kusa dani ta kalleni tana murmushi tace" ihisan yau dai naga ya salman dinnan da kk damunmu da sunanshi motsi kadan yayana yayana yayana!!!

Dariya mukayi lokaci guda nace " aunty to ya kk ga yayan nawa.

Tace " eh na ganshi kyakkyawa ga cikar kamala ga kuma kwarjini ga natsuwa amma fa yayan baki yanada matsala daya.

Fuskata tuni ta sauya nace" meye matsalar aunty gimbiya?

Tace" yayan naki baya dariya Sam kuma baya magana sosai me yasa?

Dariya nayi nace " aunty yayana haka halittarsa yake amma fa a hankali in ya saba da mutum to zakuyi hira kuma zaiyi miki fara,a kuma kinga sojane a bariki ba,a San wani dariya ba...

Dariya mukayi lokaci guda kamar kawaye .

Aunty rukayya ma ta shigo tana cewa" daryar mi akeyi?

Aunty samira tace " tadin surukina muke.
Chapter 46 · 0% Book details