← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 128

Sashe 38

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa tuni ta fita daki ta nufa ranar ko bacci batayi ba ta kulla wnn ta keance har dare ya raba biyu.

Gari bai gama wayewa ba ta fita kamar mai tfy mkranta kawai ta wuce tasha motar Adamawa ta biya kudi ta shiga.

Mota na cika su ka daga sai yola.

Tana ganin wlcm to yola tace a sauketa dama ta gaya wa Ibrahim zata zo amma Sam ta lura bai yarda ba.

Ta na sauka ta kirashi tace gata nan a wlcm to yola.

Sam bai yarda ba saida tayita ransewa snn ya amince aikuwa yana zuwa da ya ganta da katuwar jaka ya zuba mata ido hankalinsa tashe!!!!!

Haulyce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡33

********"Amina lfy na ganki haka?

Hawayene ya fara zubo mata tace"Ib ba lfy gudowa nayi daga gidanmu saboda yayyuna suna shirin yi mun auren dole ni kuma bana so.

Ib ya dafe kai hade da fadin " ya Salam!

Amina kam kuka ta fara yi sosai tace" don Allah Ib ka taimaki rayuwata banda kowa a yanzu sai Allah sai kuma kai masoyina.

Ib kam hankalinsa ya tashi matuka yace " kinga meenah zo mu shiga mota muyi magana kar a ganmu kinga nan kan hanyane.

Suka shiga mota Ib ya cire hularsa ya goge gumi sannan ya juyo yana fuskantar Amina sosai yace" meenah akwai matsala ni dinnan Dan babban family ne domin danginmu suna da yawa sosai so kankanin abu zai iya jawo min matsala ni yanzu idan nace zan taimakeki ina zan kaiki?

Amina ta zuba mishi ido cike da mamaki tace " Ib anya kana sona?

Yace " haba meenah ina sonki mana amma ina jiye mana tsoron abinda zai biyo baya ne.don haka ni dai shawarata kizo muje na kai ki gidan abokina in Allah ya kaimu gobe sai in kaiki tasha ki koma gida zanzo KD din muyi setling na komai a hankali kingane.

Amina tace " haba Ib ina maka maganar saura sati daya a daura min aure da Farouq kana in koma KD in jiraka?

Shiru Ib yayi duk kansa ya dau zafi ya rasa me zaiyi.

Amina ta ci gaba da kuka tace " shikenan Ib na gane ba sona kake ba dama yaudarace .domin da,ace son gaskia kake min da zaka iya komai akaina kamar yadda na bar gida na zabi in zauna da kai akan 'yan,uwana.Ib kasa a ranka mun rabu rabuwa ta har abada.don in nakoma Kaduna ba abinda zai hana ayi aurena da Farouq.

Ta na gama fadin haka ta fita daga motar tana kuka tace " bude ka ban jakata zan juya daga nan.

Tausayinta ne ya rufe shi a gefe guda kuma yana tunanin mafita ganin yadda taketa kuka yasa ba shiri ya fita yace" kinga ki daina kuka zo mu shiga mota nasan me zanyi.

Bayan sun shiga mota yace " Amina ina sonki so na Allah da annabi don haka bazan cutar dake ba don haka zan kaiki gidanmu kuma zan yi magana da mahaifiyata sai dai ina bukatar ki nitsu kiji me zan fada miki domin fa dagani har ke zamu iya shiga damuwa dan haka dole ne mu fara neman mafita kamin mu tinkari Ummahta.

Anan ya dinga mata bayani sosai ta gamsu.da haka suka tafi yola family house na galadima Wanda yake kusa da gidan maimartaba lamidon Adamawa .

Babban gidane sashi sashi.sai dai Alhaji Ahmad galadima wato mahaifin Ib ya jima da rasuwa.so gidan yanuwansa maza da mata cike da iyalansu.sai kuma matansa biyu Hajia Zubaida da Hajia rumaisa 'ya'yansa kuwa ashirin da uku hajiya Zubaida nada goma sha uku don itace uwargida.Hajia rumaisa kuma goma ciki harda IB domin shine danta na tara sai 'yar auta Ummi wacce bata wuce sa ar Amina ba

Sai dai wani ikon Allah familyn galadima basu cika samun haihuwa yara mata ba domin gaba daya family in zaka duba babu Wanda ya sami yara mata sai kalilan cikinsu domin ko su Ib yara mata biyu ne kawai karima 'yar hajiya Zubaida sai kuma Ummi kanwar Ib .
Don haka familyn suna matukar balain son 'ya'ya mata.don haka duk sanda aka yi haihuwa a familyn in akaci sa,a an sami 'ya mace to akwai kyaututtuka na mussaman daga kan kaya gwalagwalai ,motar ,kujeran hajj,fili da dai sauransu.

Amina tunda take bata taba shiga babban gida irin wnn ba domin In kai bakone zaka bata a gidan

Sashinsu hajiya rumaisa suka shiga.

Suna palon da hajiya Zubaida kamar kullum suna hirarsu kamar ba kushiyoyi.

Cike da girmamawa Ib ya gaishesu cikin harshen fulatanci.

Anan amina ma ta gaishesu da Hausa ga mamakinta da hausan suka amsa mata don batayi tunanin sunaji ba.

Suka danyi shiru Ib ya daure ya kalli mahaifiyarsa yace " Ummah wnn itace Amina da nake baki labarinta .

Haj rumaisa tace " o ayya yanzu daga Kaduna tazo gunka ko dai tanada wasu dangi a garin nan?

Jikin ib a sanyaye yace" aa ummah wani babban al,amari ne ke tafe damu.

Anan ya gyara zama cikin ladabi ya shiga yi musu bayani bai boye musu komai ba.

Ran umma ya matukar baci sosai bata San ta juya harshe da Hausa ta kalli amina tace" yanzu wnn har ya kai dalili da za ki bar gida saboda shi? 'Yan uwanki sun zaba miki miji Wanda suke ganin zai rikeki amma kikasa kafa kika bar gidanku don tsabar rashin tarbiyya ko? Shi lbrahim din da kika zo gunsa kina da tabbacin idan ya aureki zai soki.......

Haj Zubaida ta tari numfashinta da fadin " Haj rumaisa hkr zakiyi mu bi abin a sannu kinsan fa halin dan yau.

Ib kam sai hkr yake ta baiwa ummah yayinda Amina kuma take kuka don sai yanzu ta gane tayi babbar wauta.

Umma tace " kunga Ku tashi Ku bar gidan nan tun kafin kowa yasan wnn maganar.

Ta kalli Ibrahim tace " kaga lamido ka rabu da wnn yarinyar ka nemo wata .ke kuma ki koma garinku kije kiyi hkr ki auri Wanda yayyunki suka zaban miki.

Ib yace" don Allah ummah kiyi hkr ina son Amina wlh ummah amina tana hankali .yayyunta so suke su zalunceta sunga iyayensu basa raye.

A fusace Umma ta Mike ta tafi ciki
Amina kam jikinta yayi sanyi yanzu tunsninta ina zata je ? Dole ta koma gida ta hkr da zabinda aka mata.

Haj Zubaida kam ta lura da gaske Ib da Amina son juna suke don haka ta yi niyyar shawo kan Haj rumaisa sai dai bata San ya zatayi da bappanan su ib da yayyunsa ba.

Ta kalli Ibrahim tace " kaga lamido kwantar da hankalinka in Allah ya yarda Amina matarka ce kaji yanzu abinda za,ayi kai ta dakinsu karima ina zuwa.

Ib cike da farin ciki yace " nagode mama Allah ya kara miki tsawon rai.

Daga nan yayiwa Amina jagora zuwa dakin su karima da Ummi.duk suna nan sun dawo daga mkrnt.

Ya kallesu yace " ga ban bakuwa Na kawo muku sunsnta Amina don Allah karima ta samu tayi wanka taci abinci.

Cike da fara,a suka karbi amina.har ta danji sanyi don dama tana son irin wnn gida mutane cike gwanin sha,awa.

Ib dai daga nan ya wuce masallaci don ankira sallar magrub.

Haj Zubaida kuwa da kyar ta shawo kan Haj rumaisa ta amince da zamsn amina a gidan amma dole ne a kira family meeting domin aji ta bskin kowa .

Amina da Ib ranar kamar hadin baki basuyi bacci ba kwana sukayi suna nafila hadi da rokon Allah ya dorasu kan iyayen nasu.

Wnn shine karo na farko a rayuwar Amina da ta hana kanta bacci ta mikawa Allah kukanta.don ta sa a ranta daga yau zata zama mai kula da ibadarta domin duk matsalolin da ta shiga sakacin ta da ibada ya jawo.

Da safe kuwa duk family sun hadu a babbar palonsu na meeting. Ciki harda ibarahim.

Da yawa daga cikinsu sunki amincewa yayinda wasu kuma basu damu ba .tunda shi zai zauna da ita.

Haj Zubaida ganin yanda lamarin yaki daidaituwa yasa ta tafi gidan maimartaba lamidon Adamawa domin aminin marigayi Alhaji Ahmad galadimane amuntar tasu har ta koma kamar 'yanuwan juna don haka ne ma Ibrahim yaci sunan maimartaba shiyasa ake kiransa lamido maimartaba yana son Ibrahim sosai domin shi yake debe masa kewar marigayi Amininsa.

Aikuwa koda Haj Zubaida taje da wnn batu kuma ta hada da fadin ranka ya dade yaran nan suna son juna idan an rabasu bamusan me zasuje suyi ba kasan halin Dan yau don haka ni anawa tunanin ranka ya dade a barsu suyi auren idan yaso in an natsu sai aje a baiwa yayyunta hkr a masu bayani kuma akan illar auren dole.don yana jefa rayuwar 'ya'ya mata cikin mummunar yanayi .Allah ya ja zamaninka.

Maimartaba ya gamsu matuka da maganar Haj Zubaida.

Don haka Allah ya amshi adduar Amina da Ib sunci nasara a karshe don haka saura daurin aure.

Haj rumaisa duk da hakan bata saki ranta ba don haka ta hana ib ganawa da amina tace ya bari sai sunyi auren tukunnna.

Don haka ib ko yazo gidan bata bari ya hadu da Amina.

Amina ma bata damu ba ibadarta kawai tasa a gaba.

Amina ta shaku da Ummi da karima sosai don sunji dadin zama da ita haka itama taji dadin zama da su.

Abinka da family house tuni akaje aka gayawa Jamila matar ib labarin Amina.

Ta kasa hkr sai da tazo taga Amina aikuwa hankalinta ya matukar tashi domin amina ta fita da komai .

To anan fa aka bazama gidan bokaye 'yan tsubbu amma abu ya gagara.

Zuwa yanzu Amina ta samu karbuwa a zuciyar kowa domin kowa ya fahimci halayenta nagari ne.kasancewar ta bahaushiya ta iya zama da mutane sosai cikin hikima da dabara take bin kowa a yanda halinsa yake.

Haj rumaisa sai godewa Allah take da ib ya sami mace kamar Amina domin gabadaya hkr yake da Jamila saboda bakin hali ga rashin kunya ga kuma girman kan tsiya.
Chapter 38 · 0% Book details