← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 128

Sashe 85

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka koda na idar dining muka wuce don cin abinci sa,a ta kawo mana fruits ko da ya lura na kasa cin abinci don haka ya daddage ya dinga bani a baki har saida na koshi yace"yawwa baby ko ke fa.

Nace hmm yaya ka daina kirana da babyn nan kar amaryarka ta rainani ta dauka babynce.

Dan dariya yayi yace"babyn ce mana tunda bata wuce a bata abinci a baki ba .

Bayan munyi wanka muka sake komawa duty aikin knn ranar ko baccin kirki ya salman ya hana muyi sai na dan fara bacci ya sake lalubata har asuba duk nayi tsami wlh.a cewarsa na bankwana ne.

Haka kuwa akayi washe gari na gama komai a ranar jirginmu ya daga ina cike da kewar ya salman.

Tunda na sauka kasa mai tsarki gabadaya na manta da dukkan damuwa na shiga ibada sosai yayinda nake kaiwa Allah kukana musamman akan maganar haihuwan nan .

A kano kuwa ana nan sai shan biki akeyi duk da ma su inna sunso ace ina nan don su cusan bakin ciki amma Allah bai nufa ba.amma mama kam tasha bakar magana gun innah sai dai sam bata kulata ba har amarya salmah ta tare .

Ya salman bai wani marmarinta ba da farko ko dan bazawarace oho amma a daren amarcinsu yaji dadinta sosai domin tayi mishi tanadi na musamman gashi dama bazawarace ba wsni kunya dagewa tayi sosai don ta birgeshi aikuwa ta rikitqshi da nata salon .A ranar kasa fita yayi suna manne.

Gaskia sun sake sunci amarcinsu yadda ya kamata .

Sa,adatu kam komawa makaranta tayi yayinda munir har lokacin yana gidan mama .sai da suka yi 2weeks suna cin amarcinsu kafin suka fara fita sunje gidan mama daga nan sai gidansu innah

Inna sai washe baki take duk ta rasa inda zata saka su don murna abin ya matukar bawa ya salman mamaki.

Su innah har da nasiha tana cewa salmah kar ta dauketa suruka ta dauketa kamar uwa don ita uwace a gareta yayinda ta jawa ya salman kunne akan wlh in ya sake ya batawa salmah rai sai ta saba mishi .

Salmah taji dadin yanda aka karbeta a familyn mijinta sosai.sadiya kam bata sati bata je gidan ya salman ba tuni ta kwashe labarina ta gayawa salmah har tana cewa tayi taka tsan tsan dani don ni ba mutumiyar arziki bace hmm duk karyar duniya da sharri ba wacce sadiya bata fada a kaina ba sai da ta tabbatar ta bakantani a gun salmah har ta fara shiri akaina.don a tunaninta in bata mike tsaye ba in na dawo zan iya rabata da mijinta.

Ina can kasa mai tsarki ban ma san wace wainar ake toyawa ba nikam ban kuma taba kawo komai a raina ba tunda ya salman na kirana kullum har sau biyu a rana.

A haka muka gama ibadarmu lfy lau ba wani matsala yanzu har muna shirin dawowa!!!!!!!

Haulyce🥰👍🏻
[10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡77

***************Tun daga airport haka kawai na tsinci kaina cikin faduwar gaba ko don bansan me zanje in tarar ba a gida.

Haka dai na dinga yiwa kowa fara,a Ruma tace"ihsan kinganki kuwa masha Allah kinyi looking fresh wlh.kamar kece ma amaryar

Murmushi nayi yayinda nace" hmm na isa?

Raihana tace min a hankali "ke kin ma fi amaryar kyau 'yar uwa wlh .

Sukayi dariya da sakina nace"Allah ya shiryeku to ni duk banga yayana ba kuma shine ya kamata na fara gani anan?

Ruma tace"baya gari yayi tfy bakuyi magana ba koh?

Nace"eh na nemi layinsa shiru ma.

Raihana tace"kwantar da hankalinki zai dawo kuxo mu tafi.

A motar ruma muka dawo gida tunda muka shigo nakejin wani iri .

Munir ne ya taho da gudu yana momy oyoyo shida sa,a da zainab suka rumgumeni.

Daga munir nayi sama duk da girmansa ina dariya nace"oyoyo good boy nayi missing dinka sosai dear.

Na sumbaci goshinshi ina murmushi daga nan muka wuce ciki zuwa part dina da su zainab suka gyara min shi fess dama kuma kan na tafi ya salman yace zai sake min funitures har ina ce masa ai komai sabone ya bari kawai.sai gashi na tarar da komai sabbi dal ga kayayyakin sawa an dinka su tirim daga kan atamfa laces material da shadda gaskia naji dadi sosai har naji sanyi a raina.

Su ruma kuma sun shishshirya min girki na musamman komai da komai masha Allah.

sai zuwa ake yi min barka da dawowa 'yan uwa da abokan arziki amma abin mamaki har lokacin banga matar gidan ba.kuma ban tambaya ba.

Ya salman ma ya kirani cike da murna yace"hajia barka da dawowa .

Murmushi nayi nace"yawwa yaya duk na kosa na dawo na ganka nayi missing inka sosai yayana.

Sautin murmushinsa na jiyo yace"nima babya inata missing dinki aiyukan ne suka mini yawa amma zan dawo karki damu ya gajia to?

Na kwantar da murya nace "Alhamdulillah.

Yace"Masha Allah saidai fa naji muryartaki bata fita sosai.......

Bai rufe bakinsa na fara tari
yace"subhanallah baby mura koh?

Na dan gyara murya nace"bari kawai yaya ina fama da mura kirjina sai toshewa yake.

Na fada yayinda na lalubo inhaler na.

Yace"sorry baby Allah ya baki lfy zance salim ya kaiki asibity ko na kira doctor james azo a dubaki.

Nace"ba komai yaya sai ka dawo Allah ya kawoka lfy.

Yace "ameen ki kula da kanki sosai ina raihana?

Nace"gata nan

Yace"bata wayar.

Na mikawa raihana wayar ta karba fita tayi waje .

Ruma tace min "to ki dan kwanta mana ihsan .

Sakina tace"ai naga kamar bacci ma kk ji.

Murmushi nayi nace" ai bazan iya bacci ba sai zuwa anjima saboda baki da suke zuwa.

Raihana ta shigo tana mika mun waya tanacewa don Allah kuji min munafurcin mata?

Sakienah tace"wacce?

Ta zauna hade da jan tsaki tace"Salmah mana.

Ruma tace"wai me?

Raihana tace"wai tace ma yaya bamu fada mata dawowar rumaisa ba alhalin tana gidan nan duk wani zirga zirga da muke tana sane tun dazu baki sai zuwa suke ta sani sarai amma kinji wai munki mu sanar da ita ai bama sonta ne bama kula da ita sadiya kadai da innah suke sonta harda wani guntun kukanta.

Dariya mukayi sakina tace"yayan ke fada miki hakan?

Raihana tace"eh man sai kinji ma uban tsawa da yake min kamar ya fasa wayar ya shigo ya sameni.

Sakina tace"lallai yaya ma dai daga an kwashi karya da gaskia an sanar dashi sai ya hau kai ya zauna?

Raihana tace"bari kedai naji haushin matan nan sosai yanzu yaya wai muje dake mu sanar da ita kuma mu kawota ta gaida rumaisa.

Sakinah tace"tab ni wlh bazanje ba irin kallon banza data ke ma mutane duk sadiya tabi ta bakanta mu a wurinta.

Ruma tace"to ya zakuyi hkr kawai zakuyi tunda amaryarkuce.amma dai nima nazo gidan nan tun jiya mun gaisa har na fada mata ihisan zata dawo yau ko ta manta ne?

Sakinah tace"iskanci dai kawai.

Murmushi nayi nace "don Allah kuje ku sanar da ita kar ku kara laifi ni dai ace daga dawowata har an fara samun matsala.

Raihana ta tashi hade da fadin gaskia kam don ba mamaki sadiya taje ta hadamu da inna ma.

Sakina ta tashi suka fita.na kalli ruma nace"'yar uwa bani labarin amarya don Allah.
Ruma tace"hmmm amarya kam se kinyi taka tsan tsan yar uwa domin sadiya ta rigada ta sanar da ita komai karya da gaskia kuma kinga innah naji da ita don haka dolene kisan irin zaman da zakuyi .

Jikina a mace nace"to Allah shi kyauta .

Tace"amin hmm.

Kusan minti goma da tfyrsu sakinah sai gasu nan duk da amaryar tasu da sadiya .

Ba laifi Salmah kyakkyawace doguwa tana da dan haske kuma ta dan fini jiki kadan.taci kwalliyarta cikin shadda riga da skirt tasha daurinn dankwali ta zuba sarkoki se kamshi ke ta faman tashi tunda ta shigo.gashi tasha lalle kuna ganinta kunga amarya.

Fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso nikam murmushi nayi mata hade da yi mata sannu da shigowa.

Ta zauna kan stool nikam ji nake gabana na faduwa wani irin kishinta nakeji sosai tabdi ashe haka mata keji in an musu kishiya? To sai dai ince Allah ya bamu hkr ya sanyaya zuciyoyinmu.

Nan muka fara gaisawa tace"ashe kin dawo ai na dauka sai koh gobe .

Murmushi nayi nace "aa yau din ne dama.....

Sadiya ta karba "to rumaisa ga amarya aunty salmah nasan yau ne haduwarku ta farko koh?

Nace"hakane yau ne .

Tace"fatan zaki bata hadin kai domin bata da matsala ko kadan tana da saukin kai kuma tana mutunta kowa don haka pls ki bata hadin kai ku zauna lfy.

Murmushi nayi nace"to sadiya naji karkiji komai Allah ya hada kanmu.

Raihana tace da sadiya"to da kika gabatar da ita a gun rumaisan ai ita ma kamata yayi ki gabatar da ita gun amaryar ko? in dai duniya da adalci .

Bata saurari abinda sadiya zata ce ba ta kalli salmah tace"to ni bari in gabatar miki da rumaisa ko ince uwar gida kan gida kin ganta nan ko kadan bata da matsala hkr ne da ita sosai snn tana da kirki da sanin ya kamata don haka ki zauna da ita lfy .

Murmushi tayi tace" babu matsala ai raihana dama suleyman ya fada min komai kuma insha Allah lfy lau zamu zauna

Ta kalleni tana murmushi tace"to me za,a dafa miki yanzu zan shiga kitchen dama.

Nima murmushi nayi nace"in dai dan nine ki huta wlh ga abinci kam nan mama ta turo min raihana ma ta kawo snn mmn sakina ma ta turo no need se kinyi girki se dei ko naki .

Tace" ok dama ke dince zan girkawa.don suleyman ya turo cefane yace a maki girki tun tuni bansan kin dawo ba .

Nace "babu komai wlh na gode da kulawarku gareni.

Ta mike hade da fadin ba komai bari na danje na kwanta na huta.

Nace"to ba laifi a tashi lfy.
Chapter 85 · 0% Book details