← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 128

Sashe 116

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kawai ga wayar sadiya ranar ta kirani kamar kar na dauka amma haka nan na daure na dauka muka gaisa anan ta fara gaya min bukatanta hade da rokona akan insa baki ya salman ya bata jari itama tana son ta fara business.nace mata insha Allah zan rokan mata.

Amma koda na tuntubi ya salman da maganar kin saurarata yayi a karshema ce min yayi in daina kula sadiya bayason sadiya ta kuma shiga rayuwata.

Nidai banji dadin hakan ba don haka a cikin kudin da ya bani kwanaki na dauki milliyon biyu na bata wai karkuso kuga murna ranar taje ta gaya wa innah.innah tace"hmm ai ta rigada ta gama mallakeshi duk abinda tace mishi baya ko bata lokaci yakeyi .

Sadiya tace"hmm Inna ni dai tunda na samu ai shikenan.

Inna kam haushi ne taji sosai saidai bata kuma cewa komai ba.

Su nafisa kuwa tuni kasuwanci ta kamkama Allah ya basu sa,a sun fara da kafar dama don haka komai na tfyn musu yadda suka tsara.adda A'i burinta ya fara cika yanxu kam .

Yayinda sadiya ta shiga sanya ido a lamarinsu a hankali domin tana son gane me sukeci saboda ziciyarta ya shiga zarginsu........

Hmm Allah ya kyauta

Hauly ce🥰🙏🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡98

*******Alokacinda yaran nan suka sami hutun december muka tafi yola muka bar yaya a gida da nafisarsa.

Gidan galadima muka fara sauka Allah sarki rayuwa gabadaya tsoffina nan babu su a yanxu dai dai suka dinga tfy har suka kare.sai adduar Allah ya rahamcesu a koda yaushe nazo yola gidan galadima sai na zubda hawayen tunawa da haj rumaisa da hajiya zubaida mutanen kiriki Allah ya jikansu.

Mun jima agidan don saida muka shiga kowane sashi a karshe gidan mai martaba muka tafi kasancewar ba lokacin fada bane mun samu ganinsa mun gaisheshi cike da girmamswa.sarki Abdallah girma ya fara zuwa gaskia.

Muna nan gidan lamido har isha snn muka wuce mafiyas quaters gidanmu.sosai kannena suka shiga murnar ganinmu haka ma su aunty samira bayan munci abinci muka baje a palon daddy muka shiga hirar duniya yayinda su farida suke ta tsokanar daddy nan ma ina taka musu birki sosai.

Karfe goma kowa ya kwanta nikam ina tareda aunty samira a dakinta hiranmu yaki karewa hmm dama kunsanmu indai mun hadu to kwana muke muna hira ko itace da girki bata zuwa dakin daddy a ranar.

Nan ta fara tambayata tace"ihsan ya kike jin zama da wnn yar mitsisiyar yarinya da surukina ya aura?nasan kina ta ganin iyayi iri iri.

Dariya nayi nace"hmm babu sam aunty nima da farko na dauka hakanne amma sam nafisa babu ruwanta bata ma shiga tsabgar komai na gidan bata maida hankalinta akan komai.

Aunty samira ta tabe baki tace"to Allah yasa ta dore gaskia na miki murna.kinsan kwanaki da bakida lfy sosai daddynku ya dage akan gaskia sai salman ya sawwaka miki saboda wahalar da kk sha tinda kukayi aure da kyar aunty amina ta lallabashi.

murmushi nayi nace"hmm aunty bazan iya rabuwa da yayanah ba wlh.kinsan ko ni a lokacin da yake na dan fusata sai na yanke shawaran barin masa gidan kamin akai ga hakan nazo na kama rashin lfy wlh aunty irin kulawarda yaya ya dinga bani sai naji kawai bazan iya barinsa ba dan gabadays ya manta da wata amaryarsa hankalinsa gabadaya akaina yake har saida na warke.kuma kinga aunty duk abubuwan nan dake faruwa dani a rayuwa yayana bai taba juyan baya ba yana sona sosai kuma ya yarda dani hundred percent snn baya wulakantani.aunty wnn shine dalilinda yasa ko su inna sun min wani abun nake hkr bana nuna fushina ko damuwata tunda wanda nake zamansa bai taba juyan baya ba.

murmushi aunty samira tayi tace"hakane ihsan Allah ya kara muku hkr da son juna wlh ihsan rayuwarki da salman tana birge kowa.

dariya nayi nace"amin aunty.

Snn na sake cewa aunty kamin na koma gyara nake so a min na musamman ina son in koma amaryace nima.

dariya tayi tace "babbar magana kice kuma kara,i ya tashi.to banda abinki ihsan cikin nan fa.

na dan bata fuska nace"ai bazai hana ba aunty.

Tace"tab to wlh badani ba.kinga ki bari sai Allah ya raba lfy yawwa sai mu aika har nijar sokkoto maiduguri kayan kamshi duka .amma yanxun zaki danyi sama sama kawai .

murmushi nayi nace"yawwa aunty dama ina son farida in fara dan kinsata kamin nan kinga munir dawowarsa saura wata daya yanzu kuma ya salman yace yana dawowa da wata biyu za,ayi bikinsu.kinga har sun gama komai har gininsa na kano.

Aunty samira tace da kyau Allah ya nuna mana.kuma gaskia gara mun fara tsumata .to ya batun asibitynda za,a bude kuma?

nace"ai kinsan aikin asibity yanada bukatan nitsuwa don haka ana nan ana shirye shirye a kanshi
Tace "masha Allahu.Allah ya nuna mana .

Nace amin ya rabb
Har karfe biyu snn muka kwanta bacci.

Washe gari muka shirya sai gidan ya awwal yini mukayi snn muka dawo.

Snn washe garin kuma gidan ya samir.haka dai muka dinga zaga dangi.su farida ba karamin alkhairi aka musu ba yayinda samarin yola sukayiwa farida caa wai sonta suke.

Satinmu biyu muka shirya dawowa ba don mun gaji ba sai don matsin ya salman .

ranar jumma kuwa muka taso jirginmu na safe sai gamu kanon dabo.

tinda muka sauko na hango ya salman na saki murmushi shima ya maida min.ganinsa nayi ya koma saurayi dan shekara talatin domin kanan nan kaya ne a jikinsa snn ya toshe ido da bakin glss hannunsa daure da agogon azurfa sai daukan ido yake yayinda fuskar nan tasha gyara hmm yaya gayu.

Muna karasawa yaran nan suka rumgumeshi cikeda murna yana mana sannu da hanya.

farida ta kalleshi tace"daddy wlh da kyar na ganeka.

khalil yace "koni daddy.gabadaya ka zama wani dan saurayi.

Murmushi yayi yace"dama ni tsoho ne?

Suka sa dariya yayinda farida ta rike hannunsa ta kamo nawa ta hada da nashi tana murmushi tace"wlh mama da daddy kunyi kyau sosai yau dinnan kamar wasu sabbin couples

Ta kalli khalil tace "ibrahim daukesu hoto.

khalil yace yanxu kuwa.

nan ya fitar da iphone dinsa ya shiga daukarmu hoto ya salman don tsabar daurewa karya gindi har wani canza style yake mana .
Bayan sun gama gabadaya haduwa mukayi farida tayi mana selfie.

daga nan muka kama hanyar gidansu innah don mu gaishesu.khalil turo baki yayi yace"ni wlh dama gida muka fara zuwa ba gidansu innah ba.

Nace" kai dai daddyna baka son mutane haka nan hutunda mukayi a yola duk kabi ka ishemu da mu dawo.

farida tace"shi ai yafi son zama waje daya kana da aiki ai.

Ya salman dai baice mana komai ba.

Mun iso gidansu inna tuni su farida suka shiga suka barmu nan ya kamo hannuna ya rike yayinda ya cire sun glss na idonsa ya min wani irin kallo da naji gabadaya tsigar jikina ya mike matso da fuskarsa yay dab da tawa har muna exchanging numfashi ya sassauta murya yace"baby nasha wahala sosai two weeks dinnan da ba kya kusa dani ji nayi tamkar two years ne.

ya fada yayinda ya kashe min ido daya hade da daga min gira daya yayinda ya ke murza hannuna a hakali cikin nashi snn yace "gaskia you are very special ke din ta musammance my dear.

ganin yana kokarin shagalantar dani yasa nayi saurin fadin"yaya mu shiga ciki don Allah kar wani ya fito ya samemu muji kunya.

Yace"naji amma ki fada min irin tanadi da tsaraba da kk yo min daga yola.

murmushi nayi nace"kai yaya kaida kk da amarya kamar nafisa.

nan da nan yanayin fuskarsa ta sauya tabe baki yayi ya saki hannu na ya shige gaba ni kuma na bishi a baya cikin rashin jin dadin yadda fuskarsa ta canza.

A palon inna muka iske su farida tana ta zolayar inna tana dariya .

nan muka xube hade da gaisheta ta amsa fuskar nan a tamke tunda muka shigo su farida tashi sukayi suka tafi dakin mmn sakina.

Nafisa ce ta fito daga bedroom din innah tana mana sannu da xuwa ni kadai na amsa shi kam ko kallo bata isheshi ba nace"ashe kinzo kina nan?

sunkuyar da kai tayi tace,"eh.

daga nan shiru mukayi gabadaya nafisa ce taje ta kawo mana ruwa da lemo inna sai harararta takeyi.

bamu jima ba mukayk musu sallama muka tafi na dauka nafisa zata bimu amma shiru.

mun iske gida kowa lfy sojojin sai kamewa suke suna gaida oga shikam ko a jikinsa.

mun tarar gida fes koina kamshi anan yaran nan kowanne ya wuce room dinsa nima ina kokarin wucewa side dina kawai naji anyi cak dani da sauri nace"wayyo yaya so nike na danje nayi wanka da ruwa mai dimi tukun ko naji dadin jikina.

baice komai ba ya nufi side dinshi dani a hanni kamar wata karamar yarinya muna ziwa ya saukeni kan gadonsa ya koma yasawa kofa key snn ya wuce toilet ya hadomin ruwan wanka ya fito da kansa ya shiga hidimar cire min kaya hade da fadin"banji lfy babyna ba ma.

Ya soma shada cikina wanda ya dan fara tasowa don yanzu ina wata na biyar.

Saida yayi mai isarshi snn ya sake daukata sai toilet wanka yayi min shima yayi daga nan muka dawo daki ina goge jikina na juya na kalleshi nace"yanxu idan matar gidannan ta shigo ta kamamu fa munji kunya gaskia

daure fuska yayi yace"saboda haramci muke aikatawa?

Da sauri nace"Allah ya huci ranka yayanah ba haka nake nufi ba.

na karasa gabanshi ina rike kunnena kamoni yayi mukayi kan gado.hmm dsga nan fa labari yasha banbam nan muka shiga gwadawa juna so ya salman ya kamkameni tamkar zai maidani cikinsa sai sakin numfashi yake nima din hakane duk mun kasa cewa komai.

da kyar mukayi sallar azahar ya sake janyoni muka koma gado kai ya salman baya gajia ni tuni nayi laushi jikina ya fara ciwo.

sai la,asar ya rabu dani.

Kwanan mu biyu da dawowa shiru banga nafisa ta dawo ba ina son tambayarsa ina jin tsoron fushinsa.
Chapter 116 · 0% Book details