← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 128

Sashe 128

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Adda A,i kam jinyar mijinta gabadaya ya karar da duk wata arzikinsu a yanxu basuda komai sai dai da taimakon yan uwa da abokan arziki yayi jinya mai tsawo kafin Allah ya dauki ransa.gaskia fadan tashin hankali gun adda A,i ba,a magana duk ta rame tayi baki kamar ba adda A'i ba duk wanda ya ganta a yanxu sai ya tausaya mata.

Bayan ta gama takaba ta dawo gidan Inna ba don innah taso ba sai don abba ne yasa baki akan ta dawo ta zauna ba yanda inna ta iya.hakama ya salman baiso hakan ba.

Amma cikin ikon Allah kuma babu wata hayaniya tunda ta dawo ta nitsu tsaf kamar ba ita ba .yaranta kuma suna bata kulawa dai dai gwargwado.yayinda take ci gaba da kasuwancinta a hankali don yanxu fa babu harka kamar da sai dai ana manage kawai.

Nima tsakanina da ita yanxu mutunci ta daina saka kanta a lamuranmu kamar da.

_Rayuwa_ _knn_

***A karshe wnn shekaran mukaje Abuja bikin mimi da fadyl din sakina gaskia munsha hidima sosai kasancewar suma auren dangi ne.
A lokacin farida kuma take ta fama da laulayin ciki da ya hanata sukuni duk yadda taso ayi hidimar bikin mimi da ita abin ya gagara .tana kwance kawai ko ruwa tasha amai.munir duk ya shiga damuwa minti minti sai ya shigo ya duba ta .
Anan ruma ta kama yi masa fada wai baida kunya ya bari mana sai sun koma gidansu.

Bayan ta gama yi masa fada ya fita yana bata hkr na kalleta nace"gaskia ruma bsnji dadi abinda kk ma munir ba meye laifinsa anan don yazo ya duba lfyr matarsa kinsanfa shi likita ne.snn tun farko ya ma fada mana farida bazata iya zuwa bikin nan ba don bata da cikakkiyar lfy kika matsa sai tazo gashi kinxo kina ta masa fada da wanne......

Ta katseni da fadin "rabu dashi baida kunyane tun dazu yaketa shigowa ko kunyan mutane baiji sai kace akansa za,a fara haihuwa.laulayin cikin kowa yasan yanda yake ya rabu da ita mana sai sun koma gidansu suje yaci gaba da rashin kunyarsa can inda suka saba.

Dariya nayi nace"nidai banga abin tsanani anan ba kema fa in baki manta haka kuka tayi da ya salim sanda kk da cikin munir din ke kam ma bakida wani laulayi amma sai tarairayarki ya salim yake .don haka yadda kikaci naki zamani suma ki barsu suci zamaninsu.....

Fitowar farida daga toilet ne ya katseni na kalleta duk ta rame ko magana bata iyayi.

Ruma ta kamota ta kwantar da ita jikinta tana shafa kanta tace"sannu kinji ? Kiyita hkr insha Allah daga zaran cikin yayi kwari zaki daina duk wani laulayi nasan yanda kikeji sorry my dear.in an gama bikin nan kiyi zamanki anan har ki sami lfy kinji?

Kai kawai farida ta daga mata ni dai kallonsu kawai nake.

Muna shirin fita wurin walima ya salim ya shigo dakin ruma ya samemu fada ya shiga yi mana wai don me muka ce sai farida tazo bikin mimi alhalin bata da lfy.don haka ta tashi maza munir na jiranta a mota su koma kano .ai sai da lfy ake kome.

Ba don ruma taso ba haka ta kyale munir ya tattara matarsa suka bar Abuja .

Ruma ta gama cika fam tace zai dawo ya sameta ne.

Nidai sai dariya nake mata ina mamakin irin wnn karfin halin nata.

Da haka mukaci gaba da hidimar biki har aka kare lfy amarya ta tare a zariya su sakina an zama suruka.

Mun dawo kano gida ni kadai sai sojoji da masu aiki don ya salman daga Abuja ya wuce lagos amma yace min kwana biyu kawai zaiyi ya dawo.

Ban wani huta ba na daiyi wanka na shirya da kaina nayi driving gidan munir naje tukun .

Na samesu a palo farida sai zuba mishi shagwaba take son ranta ganina baisa sun fasa abinda suke ba don ni dama sun saba yi a gabana kuma ban taba nuna damuwa kamar ruma ba.

Bayan mun gaisa farida ta kalleni tace"mama yaushe kk dawo Abuja?

Nace"daxun bai jima ba.

Tace'daddy fa?

Nace"ya wuce lagos.

Snn na tambayeta ya jikin tace da sauki.

Munir kuwa ya shiga hidimar kawo min drinks da abinci

Murmushi nayi nace"sannu da hidima wnn duk aikinka ne na sani tunda ku ba kwa yarda da yan aiki.

Murmushi yayi yace"mama yan aikin ne kazamai.

Nace"hmm kai dai ka cika kyama.amma yanxu tunda na dawo karka kuma shiga kitchen kana wahalar da kanka zan na turo muku abinci har Allah ya bata lfy.

Da haka na tashi munir yace"mama baki ci komai ba fa.

Dariya nayi nace "ni a koshe nake kuma sauri nake gidan mama zanje in dubasu snn in wuce gidansu Innah suma na gaishesu.

Farida tace ai kuwa jiya inna tazo muka sata yini dole.

Dariya nayi nace"zaku aikata.

Daga nan muka fita suka rakani har bakin mota munir yace"mama me yasa baki dauki driver ba bayan kinsan dad baya so kina driving?

Na danyi shiru snn nace"yau kwadayin driving da kaina nake kuma kaga ai ba wani nitsa zanyi ba.

Mukayi sallama na motata sai gidan mama daddy ma yana gari don haka hira muka shiga yi sosai har yamma na tafi gidansu inna ina isa ana kiran sallar magrib don haka sai da muka idar da sallah muka samu damar gaisawa inna tace"rumaisa ashe kun dawo?

Nace"eh inna na dawo tun dazu amma ya salman ya wuce lagos.

Tace"ayya A'i ma dazu ta tafi lagos din nusaibarta ta haihu.

Murmushi nayi nace"o nusaiba dai ta cika gida da yara Allah ya raya .

Tace "ameen jiya naje na duba shatu ma anata fama da laulayi amma ja'ira haka suka sakoni a gaba wai sai na kwana a gidansu nace wlh bazan iya kwana a gidan ba ina ganin irin rashin kunya da sukeyi a gabana.

Dariya nayi nace"hmm Allah ya kyauta dai.
Tace"ameen bari a kawo miki abinci kici kamin ki tafi.

Haka kuwa akayi sai da naci abinci na yi sallar isha har ina shirin dawowa amma hiranmu da inna taki karewa a karshe ma ce mintayi kawai mu kwana tunda ya salman baya gari kuma ba kowa a gidan namu sai masu aiki da sojoji.

Don haka nan na kwana mukayita hira kamar uwa da yarta.don gado daya muka kwanta har gari ya waye.

Muna breakfast sai ga ya salman ya shigo da sallama inna ta amsa yayinda nikam gabana ne ya fadi don ko gaya masa akan na zo gidansu inna banyi ba don bamuyi dashi zai dawo yau ba.

Aikuwq hararata yayi yace"ke kuma da iznin waye kika zo kika kwana anan?

Inna ta karba "nice nan nace ta kwana ko laifine don ta kwana anan?

Yace"inna nifa bamuyi da ita zata zo nan ba.

Inna tace to zuwa nan din laifine knn?

Shiru yayi yayinda ya zauna ya fara gaisheta.ko da na gaisheshi kin amsawa yayi.inna tasa aka kawo masa breakfast ni dai tashi nayi na barsu na koma dakin inna nan na fara gyara dakin.

Ina cikin gyarawa ya shigo ya sameni banji shigowarsa ba kawai saiji nayi an rumgumeni ta baya kamshin turarensa ne ya bugi hancina.

Kokarin kwace kaina nakeyi ina fadin yaya don Allah ka bari kar inna tazo ta samemu muji kunya.

Cewa yayi wlh se dai ta shigo din wayace kixo nan ki kwana?

Tureni yayi nafada gado ya bini shima ya min rumfa zaro ido nayi da kyar na iya fadin"yaya akan gadon innah don Allah ka bari wlh zata iya shigowa......

Shhhhiiiii yasa hannunsa a baki snn ya fara kissing dina ta koina ni dai naki biye masa duk a tsorace nake don kar inna ta shigo ta samemu akan gadonta kai namiji baida kunya lol!

Da kyar ya rabu dani yana sauke ajiyar zuciya ya kalleni da idanunsa ta suka canza nan danan yace"kiyi sauri kizo mu tafi ina jiranki a mota karki bata min lokaci.

Ya fita yana gyara rigarsa.

Nikam dole na sake gyara gadon snn na dauki hijabina da jakata na fita bansami inna a palo ba sai mai aiki dake ta moping tace min inna na side din abba.

Don haka na fita na sallami mmn sakina snn na leka palon abba na sallami su inna daga nan na fita na sameshi yana jirana tunda yaga fitowata ya zuba min ido kamar yau ya fara ganina har na karasa na shiga motar bai ce komai ba yaja motar muka tafi.

Muna isa gida ko kunya baiji ba ya dagani cak daga cikin motar sojojinsa sai kame masa sukeyi shi dai ko kallonsu baiyi ba yayi cikin gida dani nidai yau na gama shan kunya don shikam ko ajikinsa yau 'yan barikin ne suka tashi.

Bai direni koina ba sai kan gado a dakinsa kokarin cire min ......yakeyi nace"wayyo yaya don Allah ka bari wlh na koshi sosai amai zanyi.

Shafa cikina yayi yace"so nake in samowa twins kannene ba wani abu ba.

Nace"yaya ni fa na gama haihuwa tunda farida ta fara....

Ya katseni da fadin inji wa?
Bai barni na amsa ba ya hade bakinmu wuri daya yana juya ni san ransa.

****Bayan waasu watanni farida Allah yayi ta sauka lfy ta haifo katuwar baby girl mai kama da ubanta ba abinda ta bar masa
Hmm farinciki a gun munir ba,a magana .muma hakane.

Ranar suna baby taci suna RUMAISA(intisar) Allahu Akbar nida ruma mun zama kaka lol!

Abuja ta koma wankan gida don ruma ta dage sosai ni dai ban damu ba don ko ta dawo wajena bazata wani samun kulawa har can ba.tunda ya salman kullum kwanan duniya kara manne min yake baya taba yarda nayi nitsa dashi abin har yana bani mamaki ni a tunani na tunda yanxu mun tsufa abubuwan zasu ragu amma ina sai ma abinda ya karu .gashi gida dagani sai shi su hanifa sai dai akawosu weekend.

Haka rayuwa taci gaba da tfy cikin jin dadi sai dan abinda ba,a rasawa....!
Nida ya salman zamanmu lfy lau sai dai muce *_ALHAMDULILLAH_* 🔚🥰🥰😭

*_Anan na kawo karshen_* *_wnn_* *_labarin_* *_na_* *_RUMAISA_* *_SALMAN_* .Godiya ta tabbata ga *ALLAH* Subhanahu wata ala da ya kawo ni wnn lokaci *ALHAMDULILLAH*🙏🏻 snn ina salati ga fiyayyen halitta Annabi *MUHAMMAD* ( *SAW* )🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Da fatan zamuyi koyi da duk wani abu mai kyau daga cikin labarin.Sannan muyi watsi da marasa kyan.Allah sa mu dace(ameen)🙏🏻🙏🏻 Sannan ina rokon Allah kuskuren da nayi a cikin wannan labarin ya gafarta min(ameen)🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*_GODIYA MAI TARIN YAWA A GAREKU FANS DIN RUMAISA SALMAN A DUK INDA KUKE.NAGODE SOSAI DA IRIN COMMENTS DINKU DA NA KE GANI AKAN WNN _LITTAFIN_ _ALLAH_ _YA_ _BAR_ _ZUMUNCI_ _DA_ *_KAUNA_* 🥰🥰🥰🙏🏻
_Maman khausar bazan taba mantawa da ku ba soyayyarku🥰 daban ne a cikin zuciyata❤😁😁😁😁👍🏻_❤❤❤❤❤
_Ina yinku sosai da sosai.😉🥰❤_

*Tammat* *bihamdillah* ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻🔚🔚🔚🔚
Chapter 128 · 0% Book details