← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 128

Sashe 121

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

washe gari da yazo ta kama tambayarsa me ya hadashi da nafisa ya korota?

yacewa inna ta tambayi nafisan ta fada da bakinta.
A yayinda nafisa tace ita bata san me ta mashi ba
Abu kamar wasa duk sun saka inna a damuwa salman yaki cewa komai har lokacin abu kusan sati uku knn.

Farida da munir kuwa tuni suka dinke suka shiga gwadawa juna soyayya da kulawa ta musamman gabadaya mun gane hakan nida ya salman don haka ba karamin dadi mukaji ba addua da muka dade munayi ya karbu Allah mun gode maka .yanxu abinda ya rage sai shirye shiryen biki.masha Allah.

Inna kuwa gabadaya abin duniya ya dameta zaman nafisa a gidan ba tare da wani dalili ba ya dameta do gashi tuni nafisa ta sake abinta sai harkokinta take normal salman kuma yaki cewa komai maganar da akeyi har yanxu bata san me ye takamaiman abinda ya hada salman da nafisa ba don kullum ta tambayeshi sai yace nafisa tayi bayani da kanta.nafisa kuma tace bata san me tayi masa ba.don haka sun matukar daurewa inna kai.har taje ta sanar da abba akan yayiwa salman magana .amma shiru ba wani yunkuri da abba yayi.

Inna ta gaji gabadaya ta kira Adda A'i,sadiya,raihana,nabila,madiha,sa,adatu. Tace lallai suxo ga Nafisa a gida kuma bata san me ya hadasu da salman don taki fada shi kuma yace ita zata fada da bakinta.

Ba shiri adda 'Ai ta taho kano a ranar washe gari sai ga madiha ma daga maiduguri haka ma nabila kuma daga yola sai sa,datu daga kaduna.sadiya da raihana kam tuni sun iso.

Kasancewar adda A'i tun jiya tazo tare suka kwana da nafisa tana tambayarta me ya faru?

Nafisa tace kawai don ta fita sun hadu da suraj da yazo ne ranar a hotel take tunanin kila wani munafukin ya gayawa salman din don bayama kasar a ranar ya dawo .

Haushi ya cika adda A'i ba shiri tace"haba yaushe kk zama haka ? Da aurenki zaki fita kina kula wani katon ?ai kema kinsan dolene salman zai sani ko baya kasar domin Allah kadai yasan yawan securities da yake zagaye daku gaskia nafisa kinyi wauta babba.

Nafisa tace"adda fa kawai tattaunawa mukayk sama sama dashi don ya biyo ne kawai zai wuce lagos a ranar muka gaisa.

Adda A'i ta ce"hmm to gashi nan dai kin gani yanxu ni bansan ta wani hanya zan warware wnn matsalar ba ni shatu.

Kwana adda A'i tayi tana sake saken yadda zata bulloma lamarin .

Shine washegari da su ka hadu gabadaya Adda A'i ta kalli inna tace"duk ku kwantar da hankalinku musamman ma goggo don kinga fa kinada hawan jini.nafisa ta gaya min komai akan dalilinda yasa salman ya juya mata baya.

Nan ta gaya musu komai sai dai ta boyemusu suraj saurayin nafisa ne duk da ma madiha da nabila kam sun sani har ma da sa,a .

Inna ta kalli nafisa cike da takaici tace"ke kuwa me ya kaiki aikata wnn kuskure bayan kinsan halin salman sarai yanxu duk duniya ba mai fahimtar dashi ya gane gaskiar maganar ba abinda yake zargi bane .

Gabadaya palon tsit sukayi kowa da abinda yake tunani a ransa sadiya kam sam hankalinta bai kama maganar adda A'i ba

Don haka ta kalli nafisa tace"ke ki dai fadi gaskia ko saurayinki ne domin ke ma fa ba tayar baya bace.....

Madiha ta katse sadiya da fadin"haba sadiya da auren nata zata kula saurayi ?ai ita nafisa ko da can da bata yi aure bama bata kula samari a dalilin hakan ne yasa ska hadata da yaya salman aure don haka me zaisa yanxu ta kula wani saurayi da auranta .

Nabila ta karba "gaskia sadiya bai kamata maganar nan ta fito a bakinki ba.

hmm kunsan sadiya ba hkr nan da nan ta harzuko tace"yo mata nawa suke bin maza da aurensu? Duniyar nan da muke ciki yanxu me ba,ayi a cikinta ku daina daure mata gindi wlh tunda kukaga ya salman ya juya mata baya kunsan dalilinsa babbane.

Raihana ta gyada kai tace"gaskiane nan kuma.mu dai bi maganar a sannu zaifi ni a ganina .

Sai lokacin sa,adatu tayi magana tace"nidai koma meye ne kuyi hkr kawai mu nemi ya salman mu bashi hkr itama kuma nafisan ta bashi hkr ta mishi alkawarin bazata sake ba.

Adda A'i tace"madalla wnn shine mafita ko ya kika gani goggo ?don fa se kinsa baki kan salman ya sauraremu .

Inna tace hakane karku damu na kirashi kuma yace yana nan karasowa.

Nafisa ta bata rai tace"ni wlh ba wani hkr da zan bashi kawai tunda bai yarda dani ba ya sawwake mun.....

Ko kan ta karasa tuni sa,adatu ta make bakin nata.

Kuka nafisa ta saka yayinda ta kifa kanta jikin adda A'i

Nabila da madiha suka watsowa sa,adatu harara yayinda adda A'i tace " duka ba shi zai gyara wnn lamarin ba sa,adatu .

Sadiya tace "ai hakan shine maganinta tunda ita bata da kunya fitsararriyace...

Fadin haka da sadiya tayi yasa gabadaya ta kara kular da su madiha anan suka shiga sa,insa .

Inna kam dafe kai tayi ta rasa me zata ce .

A haka salman ya iske su cikin takunsa na isa da nuna tsantsar jarumtaka fuskar nan a tamke kamar be taba sanin meye dariya ba.gabadaya basu isheshi da kallo ba inna kadai ya gaisar cikin ladabi.yayinda su madiha suka gaisheshi can kasan makoshinsa ya amsa adda A'i kam tabe baki tayi tana kallonsa .

A dry dinsa yacewa inna lfy kika kirani a wnn lokacin.

Inna ta gyara zama tace"akan dai maganarka da nafisa ne shiyasa kaga duk na tara yanuwanta ma domin suyi mata fada nasan tunda ka yanke irin wnn hukuncin to tayi maka laifi babba ne.

Adda A'i ta gyada kai tace"hakane don Allah Salman kayi hkr kasan nafisa yarinya ce har yanxu .gaskia abinda tayi bata kyauta ba ta fada mana komai don haka kayi hkr......

Cije lebensa yayi yana kallon adda A'i snn yace"laifin me ta fada muku tayi min?

Adda Ai tace"akan maganar fitarta ba ka gari ne bayan nan sai haduwarta da .....

Nan adda A'i ta shiga kame kame

Wani irin murmushi yayi mai cikeda takaici ya kallesu daya bayan daya snn ya dagawa adda A'i hannu yace" kiyi shiru kawai na fuskance ki.sai dai ni ba wnn ne kadai laifinda ta aikata min ba.nagode Allah kasancewarku gabadaya anan domin bayan wnn ina tabbatar muku da itace ta daukan min kudadena da na ajiye a dakina masu yawan gaske don........

Gabadaya zuciyoyinsu ya tsinke musamman Nafisa wanda bata taba kawowa a ranta salman zaiyi wnn maganar.

Fashewa tayi da kuka ta sake kifa kanta jikin adda A'i tace"ni ban daukan maka kudi ba .dama ashe ni kk zargi ban sani ba alhalin ni ban ma kwana a dakinka ba a ranar kuma duk gidan ka rasa wacca zaka zarga sai ni?

Shi dai bai kuma cewa komai ba Inna kam salati ta kamayi ta kalli ya salman tana mai neman karin bayani.

Anan ya fada mata komai har ya kara da fadin"a nata wautar ta dauka bazan ganeta ba ta yaya ma za,ayi nafisa ki dauki kudi irin wannan masu yawan gaske snn kiyi tunani kinsha.....

Adda A'i tace"dakata salman wnn wace irin magana kkyi ne haka? Nafisance zata daukan maka kudi ?wlh karya ne kawai ka fito fili kace ka gaji da zama da ita amma ba ka kirkiro wata zancen wai ta daukan maka kudi ba.duk yawan mutane dake gidanka a rasa wanda zai satan ma kudi se nafisa?

Shidai ido ya zuba ma adda A'i har lokacin bai kuma cewa komai ba.

Sadiya kuwa dama irin wnn rana take jira don haka tacewa adda A'i "ki daina goya wa nafisa bayafa don kinsan in har bata aikata ba ba yanda za,ayi yaya ya mata karya...

A fusace adda A'i ta dakawa sadiya tsawa"dan Allah can munafuka na lura da take takenki fa tun dazu wlh kisan me kk fada in ba haka ba.....

Sadiya ta harzuko tace"in ba haka ba sai me? Sai me nace? Ke fa bari kiji nifa ba tsoranki nakeji ba.kuma yanxu lokacin tonon asirinku ne yayi dama kece kike kulla duk wani munafurci har auren nafisa da yaya ke kika dage sai anyi dan ki cimma wani burinki...

Anan sadiya ta rufe ido ta karewa adda A'i tanadi tsaf! Ta kara da fadin "kudin nan kuma nasan ita dince ta dauka kuma dole ku dawo dashi .wlh adda A'i kinji kunya.

Adda A'i kam tuni ido ya fara raina fata amma dake gogaggiyar yar duniyace kawai sai tasa kuka ta kalli innah tace "goggo kinajin abinda sadiya take gaya min koh?

Inna kam jikinta ya mutu sosai a yanxu haka ma su nabila kamar ruwa ya cisu.nafisa kam sosai gabanta yake ta faduwa tun dazu musamman yadda taga salman ya yi shiru bai kuma cewa komai ba.

Inna ta kalli nafisa tace "don Allah nafisa me cece gaskiar wnn maganar?

Nafisa cikin muryar kuka tace"wlh goggo bani na dauka ba ina zan kai kudi masu yawa haka me zanyi dasu?

Madiha tace "nima dai shi na gani .

Nabila ta kalli ya salman tace"yaya a dai bincika dai tukunna .....

Adda A'i tace"wlh tun wuri yaje ya nemi wacca ta satar masa kudi.kuma daga yau salman kasa a ranka aurenka da nafisa ya kare .kuma sharrin da ka mata sai Allah ya saka mata.

Ta karasa fada tana goge kwalla.
Inna kam hankalinta a tashe ta kalli salman tace"Salman don Allah mecece shaidarka na tabbatarda nafisa ce ta daukan ma kudi?

Tashi yayi ya fita ba tareda yace komai ba can ya dawo rike da laptop dinsa ya zauna yana bude laptop din hade da fadin "yanxun zan cire zuciyoyinku daga shakku abinda na fada zaku ganshi zahiri.

Sadiya ta gyda kai tace"da kyau!

Bai jima sosai yana latse latsen computern ba can ya turata gabansu kusada inna.
Chapter 121 · 0% Book details