← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 128

Sashe 91

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace"hmm gatanan dai ni tunda tazo jiya ban gamsu da yanayinta ba amma tace babu abinda ke damunta.

Nan daddy ya rikice yace"to maza kuje ta shirya mu tafi asibity.

Mama ta kalleni tace"sannu kin gama ne?

Kai na daga mata tace"to jeki ki wanke jikinki kisa kaya kizo muje asibity.

Nan na tashi daddy yace" Amina ki riketa mana karta fadi.

Ganin yadda daddy ya damu yasani fadin "zan iya tfy daddy .

Daga nan na fita mama kuwa ta shiga gyara gurin bayan ta gama ta dawo palo gun daddy tace"lamido ka kwantar da hankalinka inaga ihsan kamar fa cikine.

Nan da nan daddy ya saki fuska yace"Allah yasa hakan ne Amina .

Tace"amin bari naje na dubota.

Mama ta sameni ina kwance ruf da ciki idona lumshe tace" ki daure ki tashi muje asibity rumaisah.

Haka na daure muka tafi asibity.bayan sunyi gwaje gwajensu nan suka tabbatar da ina daukeda *CIKI* tsawon wata guda........

Haulyce👍🏻🥰
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡81

**********Farin ciki a gun mama da daddy ba,a magana don sun kasa boyewa nima sosai na godewa Allah hade da rokonsa wnn karon yasa rabonmu ne .

Anan doctor da ya dubani yace ya bani bedrest kuma a kula dani sosai.

Da farin ciki muka dawo gida daddy ko motsi kwakkwara baiso nayi haka mama ta rike min hannu har zuwa dakina kamar wata karamar yarinya tace" to kindaiji abinda doctor yace saboda haka ki kiyaye duk abinda kk bukata ki fada min ko lami .

Nace"to mama zan kiyaye.

tace"yanzun me kk sha,awan ci a dafa miki?

Na dan yatsuna fuska nace "a bani black tea kadai nasha yanzun bana sha,awar komai.

tace"aa bazaiyiwu ba black tea kadai me zai maki ?ke da tun breakfast da kk yi ba ki kara cin komi ba .to shi dinma ai duk kin amayar.

nace"to mama a bani kunun tsamiya in yaso anjima sai naci wani abu tunda zansha maganin amai yanzun ko naci amai zanyi.

Tace to Allah dai ya raba lfy.

Daga nan ta fita nan na lalubo wayata na fara neman uban gayyan sau biyu ina kiransa bai daga ba don haka na rabu dashi.ina ta tunanin a wane hali yake.can sai ga message dinshi ya shigo ce min yayi nayi hkr yana busy ne zai zo daga baya .kuma ya tambayeni lfyta .na masa rply da cewa lfyta qalau kuma ba matsala sai yazo din da haka muka rabu.

Allah sarki yayanah yana can yana fama da case din innah da Salmah.don saida abba ya shiga maganar sosai aka samu aka daidaita domin har gidansu salmah sukaje shida daddyn su ya salim akan maganar don mahaifinta ranshi ya baci matuka da irin dukan da ya salman ya ma 'yarsa .amma koda yaji nata laifin sai ya sassauto aka daidaita ya salman ya amince ta dawo kuma itama ta yarda zata dawo don a cewarta bazata iya rabuwa da ya salman ba.takaici kamar zai kashe uwarta.don haka sukace sai ta warware zata dawo.

Inna kuwa tana asibity tana fama da kaddarar da ya fado mata gashi abba yazo ya dada sauke mata kwandon bala,i yayi mata wankin babban bargo a asibityn yace kuma idan ta sake shiga lamarin gidan salman zai saketa!

saida daddynsu ya salim ya dinga ba abba hkr.sadiya kuwa bayan tasha dukan ya salman abba ma kara mata yayi taji jiki sosai abin gwanin tausayi .

Inna kuwa tun ba,aje koina ba nadama ne ya shigeta sosai da kuma da na sani tabbas a yanzu ta gane kuskurenta kuma tasan alhakina ne ya kamata don haka daga wnn lokacin ta sama zuciyarta salama!(dama hausawa sukace jiki magayi Allah ya kyauta)

Ni sa,adatu ce ma tazo ta bamu karashen labarin ni da mama lol!ranar mama yini tayi tana juyayin wnn lamarin hade da fadin Allah ya kyauta .

Ni dai ina ta kaina domin a dan kwana biyun nan gabadaya laulayin sai karuwa yakeyi abinci ko wani iri naci sai nayi amai .ina sha magani amma a banza ba abinda ya ragu don haka ya kasance sai drip ake sa min lokaci zuwa lokaci.

Sai da nayi kwana hudu a gidanmu snn ya salman ya samu ya zo.

Ina kwance a dakina kasancewar kofata a bude ina dan jiyo hirarsu da mama .

Don har mama tace mishi "rumaisan ma bata jin dadi salman.

Yace"Subhanallah goggo Amina me yake damun rumaisah?

Mama tace kai dai ka isa tana dakinta waka a bakin me ita ai yafi dadi.

Ta karashe maganar da murmushi.

Shi dai bai fahimceta ba don haka kawai ya shigo dakin ya sameni kwance ga drip.

Har yaji kirjinsa na bugawa ya karaso gadon da sauri yace"Innalillahi baby abin har ya kai fa haka dubi yadda kk rame baby me yake damunki?

Murmushi na sakar masa hade da fadin"yayana kar ka daga hankalinka rashin lfyata na karuwa ne.....

Ya katseni da fadin"what....baby are you serious?

Gyada masa kai nayi ina murmushi nace"sosai ma yayana munje asibity an tabbatar min ina daukeda cikin babynka wata daya kaga sai mu gode wa Allah mu kuma rokonsa yasa wnn karon rabonm......

Bai bari ya karasa jin karshen labarin kawai ya rumgumeni ya shiga kissing dina ko ta ina tsabar murna ya manta da drip dinda aka samin sai da na tuna masa ya dago da sauri yana murmushi yace" my dear da inada ikon bude zuciyata tabbas da na bude miki domin kiga irin farin cikin da take ciki bakina bazata iya bayyana tsanrsan farin ciki da zuciya ta ke ciki ba masha Allah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu wnn kyautar da kudi baya siya.sai dai fatan Allah ya raba lfy.

Tunda ya fara magana nake murmushi nace"amin yayanah.

Ya rike hannuna daya yace"babyna kwanan nan duk na shiga cikin wani yanayi na damuwa amma gashi lokaci guda daga zuwana wajanki damuwata ta yaye duka tabbas rumaisah ke alkhairice a rayuwata na godewa Allah da yabani ke a matsayin abokiyar rayuwata Allah ya maki albarka .

Nace"ameen yayanah nima burina a kullum bai wuce inganka cikin farin ciki da annashuwa ba domin hakan ba karamin faranta min yake ba Allah ya barmu tare yayanah nima na gode da irin kulawa da tattali da kk nuna min.Allah ya biyaka da gidan aljannah.

Murmushi yayi yace"baby me kk so na miki neh ?

Dariya nayi nace"yaya babu komai.

Yace"no please tell me me kk so don Allah?kina so na goyaki ko na miki rawa?

A tare mukayi dariya sosai har na koma ina mamakin yadda yaya yake kwasan dariya kamar bashi ba .

Haka muka kasance cikin farin ciki kamin ya tafi ya shafa marata yafi a irga.

Daddy ya kirashi akan maganar cikina da abinda doctor yace anan daddy yace"yanzun ya kk ganin za,a dauki matakin kulawa da ita?

Ya salman yace"daddy ni inaga kawai gara na barta anan gidan domin zata fi samun kulawa tunda ni ba mazauni bane kullum kuma ga yanayin cikin yazo da laulayi don haka na ke ga gara ta zauna kusa da goggo Amina domin zatafi samun kulawa sosai har Allah ya yaye mata laulayin.

Daddy yace"madallah dana dama nima tunanin da mukayi knn da goggon naka amma mukace baza mu takuraka ba sai munji ra,ayinka .

Ya salman yace babu komai daddy Allah ya rabalfy

Mama da daddy suka amsa da amin.

Daga nan ya salman ya tafi gidansu ya sanar da abba komai abba yayi farin ciki sosai snn yace"kunyi dabara gara a barta gaban Aminan zata fi samun kulawa don haka kayi kokari kaje ka dawoda matarka domin bazaiyiwu kabar gidanka ba kowa ba.

Shiru ya salman yayi don gaskia baya son ya dawoda salmah tun yanxu yafi son sai ya gama azabtar da ita don yasan tana balain son ta dawo don kullum sai ta mushi text na ban hkr.

Anan abbah yaci gaba da bashi hkr yace zai dawoda ita amma sai ta karasa samun saukinta jikinta.

Sam ya salman yaki fadawa innah batun cikina hasalima yanxu ya daina sakin fuska suyi hira don haka itama innah fita harkarsa tayi acewarta sai ya sauko ta bashi hkr.

Ni dai a bangarena naso in koma gidana domin nafi bukatar yayana a yanxu musamman da naji salmah zata dawo gani nake kamar zata hanashi zuwa wajena.

Kullum ya salman sai yazo gidan mama indai aiki bai masa yawa ba sosai nake samun kulawa bana komai daga kwanciya sai cin abinci se wanka da sallah .

Salmah kuwa sai da tayi wata daya a gidansu snn ya salman ya dawo da ita kuma yace matukar tana son su shirya to sai taje ta baiwa innah hkr kuma tayi alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba.

Tace ta amince don dai wnn ai mai saukice tunda tana sonshi komai ma zata iya yi.

Hakan kuwa akayi ya kaita gidansu don ta baiwa innah hkr.

Suna shiga palon innah da sallamah sai da kirjin inna ya buga dam don haka ko sallamarsu bata amsa ba ta mike da sauri ta shige dakin ciki.

Jikin salmah a mace ta kalli ya salman kamin tayi magana ya katseta da fadin "zauna ina zuwa.

Daga nan ya bi bayan innah ya sameta a zaune bakin gado sadiya kuwa tana kan gadon sai sheka bacci take .

Yace"innah ga salmah tazo kuma gunki tazo domin ta baki hkr?

Inna tace"tazo ta bani hkr ko ta karasa ni ? Kaga salman don Allah don Annabi ka tattara matarka ku bar gidan nan bana bukatar ganin ko mai kama da ita a rayuwata.

Ya salman ya sassauta murya yace"kiyi hkr innah salmah tayi nadaman dukkan abinda ta aikata ki sake bata dama a karo na biyu don Allah inna kije ku gaisa.

Inna ta girgiza kai tace"ba dani ba wlh tattarata ku tafi na yafe mata duniya da lahira kuje kawai ba sai na fita mun gaisa ba kuma dan Allah kar kuma kawota gidan nan bana bukatar ganita .
Chapter 91 · 0% Book details