← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 128

Sashe 108

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sa'adatu tace"hmm ba sai su fada ba kina gani jiya ina gaisheda da adda A'i ta kama zagina haka kawai wai don na sauka a gidan nan ban sauka a gidansu innah ba.

Nace"ai gaskiane kamata yayi kije can kuyi hidimar bikin tare har a gama ba shikenan ba.ni dai gaskia in ba so kuke ku ja min magana ba kuje ku taya su aikin jeren nan yana da yawa kinga tin jiya suke aiki daya .

Sa,datu ta tashi hade da fadin to bari naje aunty tunda kin matsa.

Ta kalli farida dake aikin chatting tace"muje farida.
Farida ta bata rai tace"gaskia ni goggo sa,a bazan je ba kina fa gani jiya na kai musu abinci goggo sadiya ta dinga min tsawa wai banida nitsuwa.

Nace"hkr zakuyi gabadayanku tashi kuje dan Allah.

Haka ta tashi ba don ransu na soba suka tafi.

Gaskia a cikin kwana biyun nasha habaici gun su sadiya tunda suka fara jeren nan zagina suke har Allah Allah suke su sameni a babban palo domin suyita min habaici don haka da na gane daki nake shigewa abina har suka gama jerensu suka kulle side din amaryan suka koma gidansu innah

Bayan an daura aure a camaroo gabadaya suka kamo hanyar Nigeria su angwayen sun riga dawowa.kamin daga baya gayyan amarya kuma suka iso gidan innah suka sauka harda amaryarsu domin aci gaba da hidimar biki sei an kare tukun kamin amarya ta tare.

Murna a gun su innah ba,a magana domin biki akayi sosai na kece raini .duk da banda lfy haka nake daurewa.naje parties din duka har aka gama saura kawo amarya.

Randa aka kawo amarya gabadaya muna babban palo nida ruma sa,a farida sakina aunty samira da rukyn Hakim munci adon na kece raini domin karbar amarya haka nan suma tawagar amaren sunsha ado abin ba,a cewa komai domin suna isa gida ya gauraye da kamshi.

Sun kawo min amarya wurina hade da yi mana nasiha .
Kallo daya nayiwa amaryar naji gabana ya fadi don gaskia nafisa kyakkywace first class ma kuwa ga haske ga gashi gata yarinya karama hmm ai dole ne kawai ya salman yayi rawan jiki akanta Allah dai ya bani ikon hkr akan duk abinda zan gani.

Bayan su yan uwan innah sun gama nasiharsu Adda A'i ta karba "don haka rumaisa kece babba ki rike girmanki domin se kin rike ne nafisa zata girgimamaki.saboda nafisa yarinyace akanki .kuma kiji tsoron Allah karki zalunceta domin nafisa bata da tashin hankali ko kadan kuma tana da hkr da juriya .

Murmushi nayi nace"karki damu adda A'i kowacce da halinta zata zauna Allah ya bamu zaman lfy .
Gabadaya sukace amin.
Yayinda suka tashi suka nufi side din amarya madiha ke cewa kuma wani wani shekaran zamu dawo bikin suna.

Sadiya ta karba "in Allah yarda yaruwa ta.

Mudai bamu ce musu komai ba farida ce take ta faman cika tana batsewa domin tuni na gargadeta akan kar ta kuskura tace komai domin babu sa,anninta a cikinsu bana son raini.

Sukuma suna isah kofan dakin amarya zasu shiga kawai sai ga amarya ta yanki jiki ta fadi kasa sumammiya Subhanallah gabadaya suka rikice sai faman salati suke anan raihana tayi maza ta kawo ruwa aka zuba mata ta farfado amma gabadaya bata cikin hayyacinta sai nuni take musu da kofan dakin tana cewa ga wata mata da wuka tana zuwa zata soka mata .
Su dai basu ga komai ba lokaci daya ta kuma kurma ihu ta sake sumewa.

Ihunta yasa muma muka ji da sauri muka tashi muka zamu tafi sashin sai ga raihana ta fito da sauri har hada baki muke "raihana lfy.

Ta girgiza kai tace"babu lfy rumaisa ina ya salman .
Kamin nayi magana tace "ki kirashi a waya yazo akai nafisa asibity suma tayi har sau biyu.

Subhanallah muka fada gabadaya yayinda sa,adatu tayi sauri suka tafi da raihana side din amarya.
Nikuma muka koma palo da da su ruma anan na shiga neman wayar ya salman amma busy don haka na kira ya salim na fada masa komai yace shikenan bari yazo shi yanxu.

Yana zuwa muka tafi dashi sashin nafisa inda muka samu sun shimfideta kan kujera suna ta mata fifita hade da yi mata sannu.

Na karasa wurinsu da sauri nace"ku riketa muje akaita asibity.......

Ko kan na rufe baki nafisa ta shiga nuna ni tana cewa "gata nan wayyo Allah zata soka min wuka gashi a hannunta .

Ta kuma sumewa.
Ni kam cak nayi a tsaye na rasa me zance .

Tab aikuwa su Adda A'i abin nema ya samu me zasu jira gaba daya suka taso min kamar zasu cinyeni danye ya salim yayi kokarin dakatar dasu amma ina zagina suke yi inaga ba don ya salim ba da dukana ma zasuyi .

Ya salim ya ja hannuna da sauri muka fita daga side din gabadaya amma don jaraba har binmu sukayi madiha da adda A'i da sadiya .

Anan fa su sakina da ruma ma suka shiga maida musu martani harda farida.

Side din ya salman muka wuce da ya salim ya zaunar dani kan gado hade da fadin" ki zauna anan karki yadda ki fita.ina zuwa.

Ya fita da sauri yayinda yaja kofan.

Inna kuwa labari na samunta ba sai ta fashe da kuka ba ta kama fadin ai dama tasani tunda Amina na cikin yan daukan amarya tofa dolene hakan zata faru .haukatarda nafisa muke so yi kuma wlh bamu isa ba.

Da kyar ya salim ya kashe wutar a na gidanmu yace su dauko nafisa su tafi asibity suka ce wnn ba rashin lfyn asibity bane asiri nayi ma nafisa tunda gashi tana nunani tace nazo kanta rikeda wuka ta suma.

Don haka suka tattarata suka dawo gidan innah kowa da abinda yake fadi .
Ya salman kuwa sun nemeshi har sun gaji shiru.dama suna dawowa daurin aure daga cameroo ya tafi lagos .

Nikam ya salim na fita na fashe da kuka cikin tashin hankali na kira mama na shiga sanarda ita abinda ya faru duka.

Itama hankalinta ya tashi sosai tace" abin nema ya samu.ta nan suka bullo kuma?dama abinda suke so knn wayasani ma ko plan suka shirya don su hada ki da salman ?hmm wa'yan nan mutanen sun fara bani tsoro nidai .yanxu kina inah ?

Nace"ina side din ya salman gabadaya mama sun taso kamar zasu cinyeni danya wai asiri nayi wa nafisa zan haukatata yayinda wasu daga cikinsu har cewa tsafi mukeyi muna so mu hallaka nafisa ni da ke.

Mama tace innalillahi wa inna ilaihir rajiun o ni Amina wnn bala,i da me yayi kama? Ina salman ?

Nace"baya nan.
Tace "yanxu kiyi hkr don Allah karki fito inda suke ina tsoron kar suje su miki wani abu ki bari se komai ya lafa se ki fita in kuma basu hkr ba kawai ki taho nan gida ki bar musu gidan kar su miki illah gashi dama ba lfy ne ya isheki ba.

Nace"to mama.
Da haka mukayi sallama.

Kusan awa uku ina side din ya salman yadda ya salim ya zaunar dani haka nake zauna na kasa motsi kwakkwara.

Har ya salim din ya kuma dawowa ya kalleni cike da kulawa yace"rumaisa don Allah karkice zaki tashi hankalinki akan wnn maganar kinga bakida lfy.

Kuka na saka hade da fadin ya salim bansan me nayiwa mutanen nan ba suka sakoni a gaba kanajin irin sharrin da suka min ? Snn ga zagi da cin mutunci ciki harda mahaifiyata da dukkan dangina ni ya zanyi ne?

Zama yayi kan bed side drawer yace"hkrn dai zakici gaba da yi komai zai wuce insha Allahu .

Nace"har yaushe ya salim har yaushe? Abu shekara da shekaru....

Karar bude kofa ne ya katseni ya salman ne ya shigo hankalinsa tashe ya karaso gabana yana kallona yayinda ya zauna gefena ya jawoni jikinsa hade da fadin "rumaisa don Allah bana son ki daga hankalinki kan abinda ya faru naji komai kuma nasan ba gaskia bane sharrine kawai amma ba komai nasan matakin da zan dauka akai .ki daina kuka kinji bana son ki daga hankalinki kinga ba ke kadai bane yanxu.

Haka ya dinga rarrashina har sai da ya shawo kaina na dan kwantar da hankalina snn ya kalli ya salim yace"dan uwa sannu da kokari ba don kai ba bansan wani hali rumaisa zata shiga ba.

Ya salim yace "ba komai amma ya kamata duk inda zakaje ka dinga sallama kuma me yasamu wayoyinka a kashe?

Yace"wlh ba kashewa nayi muna wani wuri ne da babu network sam sam jirginmu kuma ya samu matsala .wani aikin gaggawa ne ma ya taso mana wlh shiyasa na tafi ba sallama.

Ya salim ya tashi hade da fadin to Allah ya kyauta ni bari in je in kwanta dare yayi karfe sha biyu ...
Ya salman yace"ok dan uwa ka huta gajia na gode.

Bayan ya salim ya tafi ya salman ya da da kwantar da murya yana kara rarrashina hade ce min in kwantar da hankalina.

Haka ya sakani naci abinci nasha maganina mukayi wanka muka kwanta.na samu da kyar bacci ya saceni

Washe gari kuwa da sassafe ya tashi ya tafi gidansu innah.

Sati daya ana abu daya kusan kullum su adda A'i sai sunxo sun zageni sai da ya salman ya taka musu birki ya zazzagesu kuma yace kar wanda ya kara zuwan masa gida in ba haka ransu zaiyi masifar baci.inna kuwa a waya ta kira ta zageni tass ta gama haka nan ta kira mama ma ta zageta hade da ja mana Allah ya isa.

Nafisa kuwa anata jinya don anyi na asibity shiru na gargajia ma haka sai da suka koma islamic medicine sannan ta fara samun sauki.anan suka fahimci aljannu ne.

Raihana tazo gida tana bani hkr akan abinda su adda Ai suka dinga yi mun nace babu komai raihana inda sabo ai na saba.
Haka nan taje ta baiwa mama hkr .sai lokacin na sami salama.tuni yan kamaru sun koma haka nan sa,adatu tun ranar da abin ya faru washegari ta tafi farida ma nasa driver ya maidata Abuja gudun kar taje ta ce zata tanka musu don itama rashin hkr ne da ita .gida ya rage sai ni daya .
Chapter 108 · 0% Book details