Sashe 33
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na girgiza kai cikin matsanancin kuka nace" banga laifinsu ba ko kadan don wlh nima ina son sanin waye mahaifina....
Na karashe maganar da kuka shiru yayi yace " rumaisa kiyi hkr ki bar kuka insha Allah zamu daidaita komai kuma ki kokari ki tambayi mama labarin mahaifinki idan har bata saurareki ba wnn karon ni zan tayaki mu binciko.....
Nace" aa ka bari kawai hakim kar ka shiga maganar nan.
Na kashe wayar naci gaba da kukana.
Ranar banyi bacci ba cikin dare koda mama ta zo don ta tasheni sai ta sameni akan sallayata ina sallah don haka takoma.
Washe gari su Abba suka kiramu a palonsu.ananfa daddy ya bayyana mata yadda sukayi da yanuwan doctor hakim.
Shiru ta yi sannan daga bisani tace" to yaya ni ban ma San me ma zance ba.kawai abar wnn maganar domin batada wani amfani.....
Abba ya katseta da fadin " Amina ki daure ki fada mana waye mahaifin Rumaisa domin nasan ko itama tana son sanin waye mahaifinta musamman yanzu da maganar aurenta ya fara samun matsala akan.....
Bacin rai sosai ya bayyana a fuskar mama ta ce" yaya har yanzu baku yarda dani ba shiyasa bana son tuna abinda ya faru.Rumaisa dai tana da uba amma nima bansan inda yake ba.in sunga zasu iya barin ayi auren haka to in kuma sunce sai sunsan waye mahaifinta to ni dai ban shirya amsa wnn tambayar ba.kawai su hkr da juna Allah ya kawo mata wani mijin.ni yaya a ganina kuma kun isa Ku zamewa rumaisa dangin uwa dana uba don haka ni bana bukatar a sake kawo min zancen waye mahaifin Rumaisa!
Nikam tsananta kukana nayi na ce "mama don Allah ki taimakeni nima ina son sanin waye mahaifin nawa.
Ta girgiza kai tace " bazaiyiwu ba!
Sosai mama ta kafe ba yanda su abba basu yi ba da mama ta basu labarin inda mahaifina yake taki ta fada .daddy kam tuni ransa ya baci ya kama yima mama fada.
Nikam sai kuka na Sani.
Inna ce ta shigo ta kallemu gabadaya sannan tace" kassim ka daina bata ranka a banza amina bazata gaya muku komai ba domin labarin ta baida dadinji.domin tasan ba ta hanya mai kyau ta sami yarinyar nan ba.
Ba tare da ta tsaya jin Karin bayani ba ta kalleni tace " Rumaisa bari na fada maki ko hankalinki ze kwanta.
Ta ci gaba da fadin " sunan mahaifin ki IBRAHIM.Wanda a shekarun baya da suka gabata shine ya hure Wa mahaifiyarki kunne ta dinga bijire ma yayyunta har ta kai ta kawo ya dauketa sun gudu.bamu sake sanin inda take ba baya wasu shekaru kawai ta dawo tare da ke kina yar shekara biyu kuma yayunta sunce matukar zata zauna dasu to sai dai ta maidaki wajen ubanki domin su bazasu zauna da ita da tarin abun kunya ayita zaginsu.
Shine ta daddage ba kunya ba tsoron Allah ta shuka masu rashin mutunci daga karshe ta fice Wanda bamu sake sanin inda kuke ba sai daga baya muka gane tana wani kauye domin tana shiga cikin gari acewarta tana kasuwanci amma ba kasuwancin take ba.......
Abba ya katseta da fadin " ya isa shatu don Allah!
Mama tace" ai kawai ku batta ta karasa.
Ta kalli inna tace" ki karasa maganarki shatu.
Inna ta yi murmushi ta kalleni tace rumaisa......
Mikewa nayi da sauri na bar palon ina kuka masananci.
Na tafi na barsu.kan kace meye wnn na hada kayana na fita da sauri sai ga ya salman ya kare min kallo yace " ina zakije?
Kai tsaye nace"Neman mahaifina!
Cike da mamaki yace " ke ! Kina cikin hayyacinki kuwa aina zaki je ki nemeshi? Kinsanshine?
Na girgiza kai nace " ko ban sanshi ba zan bi duniya har sai na gano inda yake.
To fa! Abu kamar wasa magana ta zama babba domin har su Abba sai da suka shiga vani hkr da ni dai na dage yau bazan zauna ba zan tafi nemansa domin ya isheni gorin da ake mani.
Inna ta yi dariya hade da shewa tace " jeki abinki rumaisa Allah ya bada sa,a.
Abba ya harzuko yace" shatu wai ke wace irice? Ana kokarin daidaita magana tun dazu amma sai kara hura wuta kike kamar wata shaidaniya wai ina ruwanki ne a cikin wnn maganar to wlh karki kuma sa bakinki bana so don na lura baki son zaman lfy.
Ya kalli mama yace " amina rike rumaisa Ku je ciki kuyi hkr don Allah maganar ya isa hakan nan
Mama ta girgiza kai fuskarta jike da hawaye saboda irin bakaken maganganu da inna ta dinga gaya mata tace" yaya ai babu amfani in tsaida Rumaisa taje kawai.shatu ta rigada ta hargutsa komai ta tayarwa rumaisa hankali ta yanda bazata taba saurarona ba don haka zamanta anan baida amfani taje ta.
Ta kalleni tace "Rumaisa ki je ba komai .mahaifinki cikakken sunanshi IBRAHIM AHMAD GALADIMA.Cikakken Dan Adamawa ne a yola.ina miki fatan alkhairi Allah ya tsareki kuma a duk inda kike a fadin duniya!
Ta karasa tana kuka sosai ta wuce side dinta.
Inna ta tabe baki tace " hmm ayi dai mugani..
Na kalli ya salman da su Abba kawai sai na juya da niyyar tfy daddy da Abba sukace in dawo kar in tafi.
Hawayen idona tuni ya kafe nace" kuyi hakuri kawu zan tafi tunda mama ta vani izni sai dai zan dawo in har bukatata ta biya.
Da sauri na fita Salman ma da sauri ya juya zai bini Wata uban tsawa inna ta daka mishi.
Ni dai tuni na fice na barsu bansan ta suka kare ba.
Bank na wuce Na Ciro kudi daza su ishen karfe shadaya ina tasha na kuwa ci sa,a na sami motar Adamawa saura mutum daya na biya kudi na bada address dina da number din Mamana saboda halin tafiya.
Nayi addua yayinda nake shirin shiga mota...........
Haulyce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
*Dedicated* *_to_* **Ummi** *Abdallah* 🥰
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```
Page➡29
*********Jinayi an riko hannuna ta baya.
Ina juyawa naga ya salman ne.
Ya zuban ido nikam tuni na kwace hannuna.
Girgiza min kai yayi yace" Rumaisa babu inda zakije kawai kizo mu koma gida.
Nace" wlh bazan koma ba don banga dalilin da zai maidani gidanku ba mahaifiyarka da 'yar uwarka sun sakoni a gaba da zagi da gori don banda asali to zanje in samo asalin nawa kuma bazan dawo gidanku ba.
Shiru yayi kamar bazai yimagana ba yace" ni dai nace kizo mu tafi ba wai ki daga min murya attention din mutane ya dawo kanmu ba.
Aikuwa na daddage naki wasa gaske kuwa saida naso tara masa mutane a tasha .don ma driver din babban mutum ne saida ya shiga maganar duk tunanin kowa ya salman mijinane.
Shidai yana rike da hannuna yace bazan shiga mota ba yayinda ni kuma nace sai na shiga yace" Rumaisa kinsan zan iya daukarki ko?
Driver dinne ya dinga bani hkr yace in bi mijina har da nasiha ya fito min da kayana .
Kuka na kama yi nace " ashe da kai aka hada baki ake kuntata mana ni da mahaifiyata a gidanku......
Ya katseni da fadin " ni dai mu tafi kawai.
Ya dauki kayana ya mayar motarsa ya dawo ya kalleni yace " kiyi hakuri ki bar wnn tfyr ko don mkrantarki .
Sai a lokacin na tuna wani abu wai makaranta Wanda a yanzu mun shiga shekararmu ta karshe kuma jibi ma zamu fara test.
Don haka dole na hkr muka tafi
Muna isa gida ko kayana ban sauke ba na fita na nufi bangaren mama
Ina shiga na sameta a kwance tana bacci.
Na karaso gabanta na fara tashintq ina" mama kinga har na tafi amma ya salman yaje ya dawo dani don Allah mama kice ya barni in tafi wlh in naje zan dawo ko don makarantana.
Ganin bata ko motsa ba yasa naji zuciyata ta buga da karfi na mike a tsorace .
Na juya ya salman ne na gani ya shigo nace" kazo kaga me ya sami mama?
Yace " bacci takeyi bayan tfyr ki ta tsinci kanta a wani yanayi har jininta yayi mugun hawa shine aka ce a barta ta sami isashen bacci bayan tasha magani.
Hawayene ya zubo min nace" ka gani ko? Duk abin nan da yake faruwa dani saboda kai ne ! Don Allah don Annabi ka daina shiga harkana ko na sami salama gun Inna.
Bai ce komi ba kawai ya juya ya fita nabi bayanshi a Palo naga mmn sakina ta shigo tana zaune bayan ya salman ya tafine ta ajiyeni ta dinga min magana hade da rarrashi.
Gaskia a kwanakun mun fama da kuncin rayuwa.Inna dai ba abinda ya canza a halinta duk da ba shiga gida muke sosai ba amma duk sadda muka shiga sai ta dinga mana habaici.
Sadiya da lathifa kuwa tuni suka manna ma inna hauka sai harkokinsu suke.Sadiya ta kara wayewa musamman da lathifa tazo ta kara wayar da ita tuni ta yaye Abdul haka suke barinshi gun Inna suyi ficewarsu .
Lathifa kam ta tata samari sosai ma su kudi kunsan kanawa da son farar mace gata kuma kalar Jan hankali don ta iya salon karuwanci sosai. Don haka tuni ta tara samari .Sadiya ma ba laifi ta sami zawarawa.don haka suke buga rons dinsu son ransu.
Duk abunnan basu San ya salman na timing dinsu ba.
Ranar da abun ya isheshi sunje biki wai amma sukaki dawowa har shadayan dare sun bar Inna da Abdul sai faman kuka yake saida ya salman ya karbeshi suka je waje har yayi bacci snn ya dawo dashi ya kwantar ya koma wajen ya ci gaba da jiran dawowarsu Sadiya.
Can kuwa karfe sha daya ta Dan wuce kadan wata dalleliyar mota ta zo dab da kofar gida ta yi parking abun mamaki sai yaga Sadiya ta fito anci ado a matse cikin riga da siket.
Ba ta ma ganshi ba ta wuce gida aikuwa da sauri yabi bayan ta lathifa kam ba ta ma fita daga motar ba kasancewar motar saurayinta ne ta tsaya suyi sallama.