← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 128

Sashe 118

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacinda ya salman ke ta faman hidimar suna nafisa kuma ta shiga tunanin yanda zatayi ta samu kudin masu yawa a gunsa.don gabadaya adda A'i ta sakota a gaba
wai me take jira har yanxu bata samo musu komai ba ga salman se kashe min kudi yake tayi yakamata itama ya bata kasonta mai tsoka.
Haka nafisa ta shiga kwantar masa da kai cikin kissa da kisina har ta shawo kanshi dama yana cikin farin cikin haihuwar twins don haka ya bata kudi masu tsoka har tana mamakin yawansu anan tunaninta ya fara canzawa shin ta turawa adda A'i ko kuwa ta rike kayanta don gaskia tana son kamin ta bar gidan salman ta samu ta taimakawa suraj shima don yanxu shine babban burinta a.amma wata zuciyar kuma na gargadinta akan karta ta kai kololuwa gurin kyautatawa namiji a karshe yazo ya juya mata baya .gashi kudin sunada yawa dolene ta nemi shawara don haka ta kira nabila don tafi yarda da ita akan madiha da sa,adatu don a ganinta zata fi rike mata sirri.........

Hauly ce🥰🙏🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡99

**********Kafin ta kai ga kiran nabila sai ga kiran suraj ya shigo wayanta nan da nan ta dauka fuskarta cike da fara,a yayinda take wani kwantarda murya.

Hira suka shiga yi sosai anan ya shiga tambayarta yaushene zata kashe auren nata gashi ta kusa shekara daya yanxu?kuma har yanzu babu abinda ta samo musu .....

Shigowar salman ne ya sa tayi maza ta katse kiran cikin tsananin tsarguwa ta tashi tana karasawa gabansa tace"yayah yaushe ka dawo?

Ya danja hancinta snn yace"tun dazu na dawo har na kuma shirin fita ban ganki ba shiyasa na shigo naga ko lfy.

Hannunshi ta rike hade da fadin"lfy lau yayah wlh na danyi baccine kawai.

Ya zuba mata ido har ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa.

Tace"zauna mana yaya.me kk so na kawo maka ruwa ko lemo?

Ya daga mata hannu yace"no am ok.yanxun gidanmu zanje in zaki je ki shirya mu tafi.

Harga Allah bata son zuwa gidansu innah amma bazata iya cewa salman bazata ba don haka dole ta shirya.

shi kuma da ya fita part dina ya shigo ya sameni da larai wacce mama ta samomin don tayani hidimar yara.

Ina baiwa Hanif nono yayinfa hanifa ke kuka a hannun larai tana jijjigata take .A haka ya shigo ya samemu da sauri ya karbi hanifa a hannun larai ita kuma ta fita.

ya karaso bakin gadon yana jijjigata yace"me ya sami goggona take kuka?

Nace"tashi sukayi a bacci suna jin yunwa........

Ya katseni da fadin"to ki bata mana itama tasha haba baby .kawo abbana ki karbeta.

Ko har yaushe yaya salman zai daina kirana babyn nan ne oho.

Na mika masa hanif snn na karbi hanifa ina fadin "shikenan mamana yi hkr am sorry.

na fara bata nono.
Snn na kalleshi nace"yaushe ka dawo ban sani ba?

Yace"tun dazu kuma yanxu ma fita zanyi ina son in bar miki sako idan munir ya dawo kice ya jirani kar yaje koina.don na kira wayarsa bai daga ba.

Nace"to ba matsala.wayartashi kuma inaga ya sata a silent ne kuma ya manta kasan shi da mantuwa ai.amma lfy dai koh?

Yace"lfy lau so nake in bashi wani aikine don gobe zan tafi lagos.

ya fada yayimda ya kwantar da hanif ya sumbaci goshinsa yana murmushi yace"good boy.

Ya matso kusa dani yana shafa kan hanifa dake shan nono "Allah ya muku albarka my kids.

ya rankwafo itama ya mata kiss a goshi snn ya dago muka hada ido bazan iya juran kallonsa ba don haka na sauke idona kasa ina murmishi nima din kissing dina yayi yana cewa"ki kula da kanki da twins bari muje gida mu gaida su innah.

Murmushi nayi nace"se kun dawo ku gaishesu da kyau.

ya tashi hade da fadin to zasuji.

Yana fita ya tarar nafisa tana jiransa a babban palo taci kwalliya kamar wacca zataje party.

Daga nan suka tafi.a hanya sai tunani take akan wadan nan kudin nata har suka isa.

Inna na harde a palo tana aikin kallon shirin dadin kowa na arewa24 kasancewar ba itace da girki ba yau.Ac na ratsata ta koina hmmm.

Kusa da ita nafisa ta zauna tana cewa"goggo yau ke kadai kk hutawa kayanki .

Ya salman ya zauna can nesa kadan.
Inna ta kalli nafisa tace"daga ina kuke irin wnn kwalliyar.

Nafisa tayi dariya tace"daga gida mana.

Salman ya gaisheda innah cike da girmamawa snn ya tashi ya fita.anan inna ta kalli nafisa tace"Ya maganar tfyr naki kamaru?

Nafisa ta dan bata fuska tace"ba na gaya miki yaki yarda ba kuma kema kinki kisa baki ai idan kk masa magana ze amince ....

Inna tace"ke dai ki hkr mana nafisa sai in zanje muje tare kinsan salman da ra,ayin tsiya in ya kafe ba mai tankwarashi.

Nafisa ta dan turo baki tace"ai shikenan?

Inna tace"yawwa ko kefa .ni nama fi so se kin haihu sai kije da danki ko yarki a hannu su hamma zasu yi farin ciki sosai.

Nafisa ta tabe baki tace"ai ni goggo banda komai.

Inna tace"Allah zai kawo kullum sai na miki adduq nafisa.naso ace ke kk haifi yan biyun nan amma ba kome kema zaki samu naki.
amma don Allah karki kuma yin irin abinda kikayi a baya.

Tace"insha Allah goggo bazan kuma ba wlh tun lokacin nadama nake.domin koda naga momyn farida ta haifi twins se naji abin ya matukar bani sha,awa.

Inna tayi murmushi tace"kar ki damu 'yar auta kema zaki samu mu dage da addua.

Haka inna da nafisa suka dinga hirarsu har salman ya shigo suka tafi a hanya saida suka biya shopping mall nafisa tayita diban kaya son ranta.snn suka dawo gida .

Mun fito palo muna zaune dawowar munir bai jima ba yayi wanka ya sauya shiga snn ya zo palon ya zauna kusa dani hade da kallon twins yana murmushi yace"twins fatan kun wuni lfy.

Ya dago ya kalleni yace"mama daddy bai dawo bane?

Nace"ya dawo har ma yace ka jirashi karka kuma fita.don ya kira ma baka daga ba.

Da sauri ya ciro waya a aljihu yace"o my God na mance wayar na silent tun zanje masallaci.

Nace"ai kai dama ka cika mantuwa da yawa.

Ya kwantar da kansa kan kujera yace"mama wlh yunwa nikeji.kuma ni matsalata bana son girkin yan aikin nan.

Nace"to za,ayi nafisa dai kasan yanxu itace da girki kullum kuma ita bata girki dama masu aiki ke komai .

Tabe baki yayi ya lumshe ido snn yace"inaga kamin ki soma girki gidan hajiya Amina zan na zuwa inci abinci ko ince ta dinga turo min tunda ita da kanta take girki.

Nace "tab aiki ya sameka.....

Farida ce ta fito daga dakinta wacce tunda ta dawo school take ta bacci wai kanta na ciwo se yanxu ta fito ko kallonmu batayi ba ta wuce dining side.

Na kalli munir nace"ga farida nan ka fada mata me zakaci se ta dafa maka.

Sai lokacin ya dago ya kalli farida wacce tayi kici kicin da fuska jin zancan zata shiga kitchen dan bata son girki a rayuwarta.

Tashi yayi ya isa wurinta yaja kujeran dining ya zauna .
Sanin halinsa yasa ta fadin "ina wuni?

Ya amsa da lfy
Tace"me za,ayi serving naka?

Ya girgiza kai yana kallon kulolin abincin snn yace"bazan ci ba.

Sai lokacin ta dago ta kalleshi snn tace"o sorry na mance ashe baka son girkin masu aiki.to me zakaci knn?

Ya dan daga kafada yace"nima ban sani ba.ke zaki nemo min abinda zan ci din in kingama cin abincin naki .

Farida ta bata fuska tace"ya ka daure kaci wnn mana pls.

Girgiza kai yayi yana tashi snn yace"in kin dafa min ki kawo min part dina ina jiranki.

Ya wuce abinsa a ranta tace"za kaci girki kuwa wlh in dai nice.

Tayi kwafa.a dai dai lokacinda ya salman suka dawo knn Nafisa na rike da ledoji tayi sallama.

Na amsa snn ina musu sannu da dawowa.
Nafisa ta zauna kusa dani tana murmushi ta dauki hanifa tana cewa momyn farida wani riguna na sayawa my baby (hanifa) masu kyau bari in gwada mata in gani .

Murmushi nayi nace"to abin son kai ne knn babynki kawai kk ma sayayya ina na hanif dina?

Dariya tayi tace"na saya mishi takalmi shima harda agogo.

Nima dariyan nayi anan ta shiga gwada musu tanayi tana daukansu a hoto.

Khalil yace"aunty nafisa ni ina nawa tsarabar to?

Tace"karka damu dear naka special ne dan albarka .

Nace"to ni kuma fa?
Sai lokacin ta dago ta kalli ya salman da tunda suka shigo muka mishi sannu da dawowa ya zauna a kujera yana kallonmu bai ce komai ba.

Murmushi tayi tace"naki special ne yana gun yaya.

Nace"gaskia naki wayon ai shi bai shigo da komai ba gaki kece da kaya niki niki snn ki hanani duk kin dauka kin rabawa yaranki.

Dariya tayi tace"karki damu momyn farida bari na baki turare body spray mai dadi.tsabar dadinsa yasa na siyeshi guda biyu ko yaya ma saida ya yaba kamshin.

Ta bude jakarta ta dauko body spray tana murmushi ta bude ko kan na ankara tuni ta fesa min da sauri na kauda kai cikin rashin sa,a kuwa iska ya kwashi turaren zuwa hancina direct wani wawan shaka na masa wanda yasa a take numfashina ya dauke na wucin gadi.anan fa al,amari ya canza na dafe kirji numfashi na fita wani iri .........

Ya salman ne ya karaso gunmu da sauri shida khalil Farida ma ta taso dama tun dazu taketa hararar nafisa na lura haushin nafisa takeji sosai se kace itace nafisan kishiyarta nan ma ina taka mata birki.

Sannu suka hau yi mun ya salman ba shiri ya jawo ni zuwa jikinshi ya kalli khalil yace"khalil je ka dauko inhaler dinta a drawer da sauri.

Nafisa duk ta tsorata tana jeramin sannu yayinda tuni tayi jifa da turaren gefe.

Farida ta sakar mata harara tace"kinsan mama ciwonta bai son a fesa mata turare direct amma kk zo kk dinga fesawa a hancinta wnn ai gangancine.
Chapter 118 · 0% Book details