← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 128

Sashe 54

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Runtse idona nayi na sake budewa na kalleshi shima ni yake kallo .

Ba Wanda ya iya cewa komai a tsakanimu sai kallo rumasau ne ta karaso da hijabinta tana " lfy yar uwa.

Ganin ya salman ya sata sakin murmushi tace " laa darling yaushe a garin namu?

Sai lokacin muka farka daga duniyar da muka tafi dukanmu biyu.

Da sauri na kauda idona daga kallonsa yayinda shi kuma ya kirkiro murmushi ya dora kan fuskarsa yace " yanzun nan kuwa sweety ina danuwana?

Tace " a darling ko gausawa bamuyi ba ka fara tambayar dan uwanka? Zo muje ciki tukun yana nan bai jima da dawowa daga aiki ba.

Suka shigo nima na biyosu a baya bayan ya zauna ta ce " minti biyu don Allah darling.

Ta fada yayinda ta shiga ciki ta barmu.

Duk na jini a takure a hankali na dago kaina na kalleshi nace " yaya ina wuni.

Yace " lfy.
Daga nan shiru mukayi ni dai na rasa dalilinda yasa ya salman yaketa fushi dani alhalin yasan ba laifina bane.

Jikina a mace na tashi na bar gidan na koma na sami mama tana girki nace " yawwa mama dama yunwa nakeji.

Tace " ni kuma jiranki nake dama ki dawo in tambayeki meyasa kk matsawa su salim da zuwa gidansu ne?

Nace " mama ya salim tuni ya koma wurin aikinsa baima zama a gida yanzu kuma ba anan muna zaune ruman ta kirani ba?

Tace " hmm ki dai barsu su sake yafi

Nace " to shikenan mama ai dama......

Karar wayata ta katseni na dauka aunty samira ce
" hello aunty

Tace " na,am Ihsan kinyi shiru a kano abinki muna ta kewarki.

Murmushi nayi nace " zan dawo ai Aunty

Tace " hmm yaushe?

Nace " next week insha Allah.

Tace " tabdi har next week? Ihisan gara fa ki dawo kawai maganar gyaran Jikinki da sauran kayan sokkoto da na miki oda duk suna ready ke suke jira kuma kinga gara ki dawo da wuri ki fara amfani da komai don wnn karon bazan yarda da asaran da kk min last time ba.

Nace " kai aunty wancan danayi ta yi ma fa yana nan karfa ya ja min matsala kinsan abu in yayi yawa.

Tace " ba wani yawa da zaiyi so nake ki zama tauraruwa a idon yayana.don haka yanzu munyi magana da daddynku ki dawo jibi kawai .

Na bata fuska nace " haba aunty jibi.

Tace " to bari ince daddyn ya fada miki da kansa.

Nace" aa kawai sai na dawo.

Tace " to za,a turo miki kudin jirgi ki gaida ruma da sauran yan gida.

Tura baki nayi nace" to zasuji.

Ta katse na kalli mama nace" kinji mama wai jibi na koma fa.

Tabe baki tayi tace " hmm ummah ta gaida assha ni don kin zauna anan ma me yake kara min ? Tunda shatu ta sakoki a gaba gara dai ki koma gidanku yafi tunda Allah ya baki sa,a matan babanki naji dake.

Nace" wlh kuwa mama kowa sona yake aunty samira duk jiji da kanta muna shiri kamar kawaye wlh.

Mama ta yi dariya tace" to ai kusan kawayen ne koda yake dai ta girme ki tunda sa,ar yayanki samir ne.ni wlh mamakin lamido nakeyi da ya rasa wacca zai aura sai 'yar cikinsa saboda budurwar zuciya irin tasa.

Nace " laa mama daddy bai tsufa ba kinganshi da aunty samira sunfi matching sosai saidai fa tana sawa yana biye mata sosai ko a gabanmu ne tayita zuba mishi shagwaba yana biye mata haushi ya samir sukeji ni dai ko a jikina.

Dariya mama ta yi sosai snn tace" hmm maza knn.da kyau .ita rukayya ba,a nuna mata soyayya?

Nace" aa Momy ba ruwanta wlh bata cika damuwa da harkar kowa bama.

Tace" ai naga alama tunda har ce min take na koma gidanku .

Nace "ai mama gara ki koma din ai kinga tunda daddy ya matsa sosai su ya awwal ma suna so ki dawo.

Tace" kinga ni kin isheni da surutun banza zo ki dauki kular abinci ki kai Palo in yaso ki dawo ki dauki plet kije kici ni wanka zan shiga don kasuwa ma zanje.

Nace " to."yayinda na dauki abinci na fita palo

Ya salman haka muka dinga wasan buya a cikin kwana biyu kan in tafi don bai son mu hadu.

Ni ko naso mu hadu nayi mashi sallama don har kiransa nayi bai amsa ba.na fita harkarsa.

Ruma bata so tfyna ba Sam dole ta hkr

Nima kaina in na tuno da wnn auran nakanji kamar kar na tafi wlh.

Hakan dai na daure na tafin!!!!!!

Hauly ce
[9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🎨```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🎨

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡49

***********Na dawo yola da kwana biyu aka fara min gyaran jiki yanzu ko fita ba,a so nayi.aunty samira ko ta dage sai duddura min kayan mata take wasu ma ban ko taba jin sunayensu ba ga na tsugunno daga Maiduguri wasu na shafawa ne .

To ni dai ba yanda na iya haka nake ta faman amfani dasu .

Jikina kam yayi kyau abun ba,a magana koina kuwa kamshi ke tashi a jikina.

Yanzu duk gari ansan nice amaryar Sarki Abdallah duk da ba fita nake ba amma tuni yarima ya turo dogarai gidanmu suna nan suna a bakin get koda yaushe.ga hadimai kuwa sun kai shidda masu yi min hidima tun banje gidansa ba.ko motsi nayi sai an min sannu duk inda na zauna fifita ake min abinci ma da na bari a baki za,a bani in na fita kuwa koina sai praising dina ake.wayyoni Rumaisa Ashe haka sarauta keda dadi?

Tuni sunana ya tashi daga Ihsan na koma gimbiya.

Abdallah kam shirin nadin sarauta ya boye shi yanzu ba mai ganinsa nima tunda na dawo kano ban ganshi ba sai dai yakan kirani wasu lokutan amma ba sosai ba.

Wnn karon daurin aure kawai za,ayi ba wasu shagali saboda nadin sarauta.

Gari duk ya cika da jama,a na nesa dana kusa ga manyan sarakuna sunzo na arewa har da sarkin musulmai yola ta cika ba ko inda za,a sa tsinke.

Gidanmu ma haka gidan galadima ma ba,a magana wnn karon ma daddy da Abba sunzo tare da Maman sakina da mummynsu salim.

Ana gobe daurin aure da daddare karfe sha daya yarima yazo aunty rukayya ne ta zo ta gaya min wai yana palon daddy nace" tab Ashe maimartaba zai sami lokaci har yazo?

Aunty rukaiya ta yi dariya tace " a to gashi nan dai yau yana son ganin amaryarsa ne.

Nayi murmushi snn na tashi na gyara jikina nasa turare muka fita koina cike da yanuwa da abokan arziki.muka wuce palon daddy .

A tsaye muka sameshi da manyan kaya Wanda suka kara masa kwarjini palon kuwa duk ya cika da kamshin turarensa mai dadin gaske .

Cike da girgimawa aunty rukayya ta ce masa" ranka ya dade gata.

A kasaitance yayi mata magana"ina yaya ?

Tace" bai dawo ba ranka ya dade dake kasan yanada manyan baki yau.

Kai kawai ya gyada mata.

Ta mike hade da fadin " a huta lfy.

Tana fita ya kalleni kaina a sunkuye nace " ranka ya dade ka zauna mana.

Kai tsaye yace min ba zama ya kawoni ba Ihsan sauri nake banida isasshen lokaci yanzu.

Nace" hakane amma lfy kazo a wnn lokacin?

Ya danyi shiru snn daga bisani yace " eto lfy za,ace .amma a gaskia na zo ne in sanar dake da kaina daurin aurena dake bazaiyu ba .....

Mikewa nayi ba shiri ina kallonsa a razane nace" mene? Don Allah me kake shirin fada min ? Anya kuwa kana cikin hayyacinka ? Maganar aurefa ba wasa bane don Allah kar ka kuma yi min irin wnn wasan ranka ya dade.

Murmushi yayi yace" wasa kuma? Ni Abdallah na taba wasa dake a iya sanina da kikayi?

Jikina ne ya mutu hawaye suka fara zubo min nace " yanzu abinda zaka min knn ? Ka rabani da dukkan farin cikin rayuwata snn yazo kace ka fasa aurena bayan an gama sanarwa koina duk fadin Nigeria sunsan da maganar auren nan amma shine zaka zo ka mana irin wnn wulakanci ? Don Allah karkasa daddy na yaji kunya kayi hkr ka fada min laifina zan gyara.amma kar ka jefa daddy na cikin bakin ciki ya gayyaci abokansa na nesa dana kusa har da wayanda basa kasar nan duk sunzo idan akace an fasa auran nan bansan........

Daga min hannu yayi yace kinga ni sauri nake banida isasshen lokaci kamar yadda na fada miki a baya kiyi hkr ki samo wani kawai.

Cikin muryar kuka nace " to me yasa? Me na maka?

Juyowa yayi muna fuskantar juna sosai yace " mummunan labari naji akanki akan irin abubuwanda kika dinga aikatawa a jamiar bayero a kano kinsan ni yanzu babban mutum ne mai daraja da kima a idon jama,a bazan iya auren matar da ta gama zubar da ajinta da mutuncinta da kimarta na 'ya mace a waje ba.don bazan gurbata rayuwar gidana ba a matsayina na babban mutum mai jagorantar alumna......

Tsananin mamaki da ya bayyana a fuskata karara ko motsi ban iya nayi ba kallonsa kawai nakeyi har ya gama fada ya kama hanyarsa zai fita sai ko ga daddy anan ya lura da yanayinsa ya tsaidashi yana" Lfy Abdallah?

Shiru yayi baice komai ba ganin baiyi niyyar magana ba yasa daddy ya kalleni yace " ke Ihsan lfy?

Na goge hawaye nace " daddy wai cewa yayi ya fasa aurena..

Daddy yace" subhanallahi me ya faru Abdallah?

Kai tsaye yace " ka tambayeta na fada mata dalilin da yasa.

Daddy ya kalleni cikin tashin hankali yace" Ihsan ki fada min me ke faruwq don Allah?

Kuka nake mai tsanani nace " nima daddy bansani ba.

Daddy ya riko hannunsa yace " kaga kanina don Allah ka fada min me ke faruwa kar Ku Sani a damuwa don Allah!
Chapter 54 · 0% Book details