← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 128

Sashe 31

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai ko kan na karasa naga mama ta kura min ido ido cike da mamaki tace" au shine Ahmad din.

Shiru nayi ita kuma ficewa tayi.

Sati na daya aka sallamoni.
Amma gabadaya na kasa sakewa duk da su faiza na nan amma wnn karon basu gane min ba.
Banda aiki sai Kuka

Sunyi rarrashin duniya sun gaji haka ma mama.

Ranar da daddare bacci ya gagareni don tsabar bakin cikin rayuwa.na tashi na tafi dakin mama banyi mamakin ganinta akan sallaya ta idar da sallolinta tana karatun Qur'an
Kusa da ita na zauna Dan haka ta sami aya ta tsaya sannan ta rufe Qur'ani ta kalleni tace"wai har yanzu bazaki bar wnn kuka ba? Da kyar fa jininki ya sauka bayan asma kina son sawa kanki hawan jini ne? Kina 'yar karama amma kina son ki dorawa kanki damuwa.in dai da tsawon rai to baki fara komai ba a rayuwarki tunda ba kiyi aure ba baki haihu ba.abinda yake gabanki yafi na baya yawa don haka gara ki rage damuwa.

Hawaye na zubowa nace"mama wlh abubuwanda ya faru dani yasa naji komai na rayuwa ya fitan min a rai mama ni kunyan kowa nakeji a gidan nan musamman ya salman da Abba.

Na karasa maganar cikin matsanancin kuka.

Jawoni tayi jikinta tace"ya isa haka nan kuka.haka taki kaddarar take baki isa ki tsallakeba.kuma ki daina dawoda hannun agogo baya ki bar wnn maganar don ya wuce sai dai a kiyaye na gaba.kuma kinga sakaci da addini shi ya ja miki.da ace kin rike addininki hannun bibbiyu wani abun ko zai sameki sai kiga yazo da sauki.

Na gyada kai ina goge hawayena nace"mama ina zargin wani abu gameda maganin da inna ta ban......

Anan na bata labarin yadda duk mukayi da inna da Sadiya.

Shiru tayi ta zuban ido sannan daga bisani tace"su suka Sani da mahaliccinsu.yanzu dai da fatan kin hankalta.kuma in Allah ya kaimu rai da lfy gobe kije ki gaida Abba ki bashi hkr da salman.

Na daga mata kai.
Daga nan na koma daki na shiga toilet na dauro alwala nazo na hau sallayata.

Da safe har 10:00am na tashi don haka na fada wanka bayan na fito na shirya tsaf cikin Riga da siket na atamfa.na saka hijabina na fito

A Palo na sami mama da faiza da sakina suna breakfast sai hira suke.

Suna ganina faiza tace "Queen an fito?

Harara na sakar mata nace" nace bana son sunan nan ko?

Tace"ai ko baki so dashi zan kiraki tunda haka naji yan makarantarku ke kiranki duk Wanda suka je dubaki a asibity.

Sakina tayi dariya tace"Ranki ya dade Queen of beauty !

Faiza tace"amma na BUK.

Shiru na musu na ficewata cikin gida na side din Abba na shiga kasancewar yau Sunday yana nan.muka gaisa anan na bashi hkr.

Murmushi yayi yace" ni kuma me kika min rumaisa? Ai babu komai Allah dai ya tsare gaba

Nace amin
Daga nan dakin mmn sakina na shiga na gaisheta.
Sannan na tafi dakin inna na sameta da Sadiya suna hirarsu harda dariya.

Suna ganina naga yanayin fuskarsu ya sauya Sadiya tace" lfy kika shigo mana ba sallama?

Fuskata a daure nace"don me zaki ji sallamata kina dariya shewa kamar ba musulma ba.
Tace"au dariya da shewa laifine?

Tsaki nayi nace " ni ba wurinki nazo ba.

Na kalli inna wacce naga gabadaya ta zuban ido.

Na mika mata goran mai data bani nace" inna maganin da kika bani naji dadinsa kwarai nayi amfani dashi yadda ya dace ga nan robar na dawo miki na gode sosai Allah ya biyaki abun kika min.

Gabadaya sai naga mamaki ya bayyana a fuskarsu .

Yayinda tuni hawaye ya ciko idona na ajiye robar na fita.
Gidansu ya salman na tafi na sameshi ya shirya zai fita.

Sallamata tasa shi juyowa muka hada ido da sauri na sauke idona kasa duk sai naji kunya kamar na nitse.

Tunda ya amsa sallamar bai kuma ce min komai ba.

Na daure nace" yaya ina kwana?

Bai amsa ba kuma badhida niyar amsawa.

Durkusawa nayi har kasa nace" don Allah yaya kayi hakuri ka yafe min laifin da na maka wlh ba laifina bane na wayi gari kawai na tsinci kaina a cikin mummunan yanayi.

Na karasa maganar cikin kuka.
Ido ya zuba min shi kadai yasan me yakeji a ransa.

Ya daure yace " shikenan na yafe miki amma don Allah ki daina zuwa inda nake don ban son ganinki Sam Sam!

Na girgiza kai nace" yaya idan ka juya min baya bazan ji dadi ba a rayuwa don Allah ka daure ka manta da abinda.......

Cikin tsawa yace" ki tashi ki tafi nace bana son ganinki...

Cikin kuka nace " yaya wlh bazan iya wnn horon ba gara ka min wan......

Yace" OK tunda bazaki tafi ba ni bari in bar miki gidan.

Ya tashi da sauri nima na tashi na fita ina kuka.

Tun daga nan fa komai ya fara birkicewa tsakanina da ya salman don gabadaya baya ko son jin muryata a sanadin hakan har ya daina zuwa kofan mama.

Kafin mu gama hutu tuni an anzo anyi maganar auren faiza da sakina hakama ya salim anje an masa tambaya don so ake a hada gabadaya ayi shi a karshen wnn shekara wato December.
Sai dai ya salman yace shi bai gama shiryawa ba tukun .

Abinda ya baiwa kowa mamaki don tuni sun gama tsara gininsu kuma sun aje kudi dai dai gwargwadon shagalin bikinsu sannan yanzu dawowarsa kano harda business sukeyi da ya salim kuma Allah ya sanya albarka komai na tfy dai dai da yadda suka tsara.
Amma yace shi bai shirya aure yanzu ba.
Don haka su Abba suka sakoshi a gaba akan ya fada musu meye matsalarshi ?

Yace ba komai kawai shi ba yanzu zaiyi aure ba.
Su dady suka kirani suka tambayeni ko dai akwai wani abu da ya hada mu ne?

Nace babu.
Anyi juyin duniya dashi ya fadi mecece matsalarshi amma ya kafe kan ra,ayinshi Wanda a karshe daddy yace Wa Abba su barshi a hankali zasu shawo kanshi!!!!!

Inna kam babu Wanda ya kaisu farin ciki domin komai na tfy yadda malaminsu ya tsara musu a nasu tunanin knn.

Nikam nayi kuka har na gode Allah mama ta ce in yi hakuri kawai mu barwa Allah komai.

Gaskia wnn karon hutun baiyi dadi ba har aka bude makaranta su fa,iza suka koma ni kuma naci gaba da zuwa ina dawowa.ganin na nitsu hankalina ya dawo jikina yasa mama ta barmin motarta da kaina nake zuwa in dawo kuma Alhamdulillah na daina kula kowa dama ni ba wani kawayene dani ba.don haka in naje abinda ya kaini kawai nakeyi in mun gama lectures na dawo gida.anan ma ba na fita daga kofar mama na daina kula harkar kowa.

Ya salman tuni na watsar da lamuransa don na gane ba son aurena yake ba.shiyasa yake wani cewa be shirya ba.

Ahmad kam ba yanda baiyi dani ba mu koma kamar da amma naki na saurareshi don haka ma nace mishi in har da gaske yana sona to ya tuba ya bar shaye shaye yazo muyi maganar aure don ni aure nake son yi.

Tunda mukayi haka bai kuma nema na ba.haka ma fahad muka rabu daga randa nace ni aure zan yi.

Yanzu doctor hakim ne kawai ya rage yana ta bina akan Na amince ya turo magabatansa nace mishi sai nayi tunani.

Watarana Na dawo makaranta Na shiga cikin gida don in duba jikin Zainab don tana zazzabi .

A tsakar gida naga wata wacce kusan zamuyi sa,a fara doguwa ga gashi kam da ga gani ba tambaya 'yar kamaruce don tana shigen yanayi da inna.
Muna hada ido sai naga ta harareni ta shiga palon inna hannunta daukeda kulan abinci da plate.

Murmushi nayi Na wuce dakin mmn sakina Na gaishta Na tamvayeta jikin zainab don tana bacci.

Tace" jiki kam da sauki sosai rumaisa yau kun tashi da wuri.

Nace " eh munyi test ne.
Muka danyi shiru nace" mama wacece Na wuce a tsakar gida?

Tace " hmm latifa ce 'yar yayan inna.ta miki magana ne?

Nace "aa kawai naga ta na min wani irin kallo kamar mun taba haduwa hakan nan kuma ni ko aurensu Sadiya ma ban ganta ba.

Mama ta tabe baki tace"wnn gogaggiyar 'yar duniya ce daga gani don in kinga rashin kunya da takeyi a gidan nan sai kin rike baki.gara ma da baki shiga don tuni Sadiya ta gama gaya mata komai akan kowa .wai naji inna na cewa itace salman zai aura .amma Sam batada respect Allah dai ya kyauta.

Dan murmushi nayi cikin karfin hali nace "amin mama bari in isa side dunmu .ayi ma zainab sannu in ta tashi Allah ya sawwaka.

Tace" to rumaisa amin Na gode.

Na tashi Na fita a tsakar gida Na sami inna a kitchen.
Na gaisheta ta amsa hade da fadin kira min Sadiya a Palo.

Nace"to.

Tun kan Na shiga palon naji kamshin turaren ya salman wnn ya bani tabbacin ya na palon.

Na daure Na shiga da sallama wata tsiririyar murya naji ta amsa min

Na shiga nan da nan naji kirjina ya soma bugawa.

Ya salman na gani yana zaune ita kuma tana zaune kusa dashi ko dan kwali babu akanta ta zuba gashi har tsakar baya.

Abinci yakeci ita kuma tana mishi hira da fulatanci kamar mai rada ta kwantar da murya tsabar kissa da kisisina kamar zata shige jikinshi.

Nayi matukar kokari nayi controlling din kaina na kauda ido na akansu na wuce dakin ciki labule na daga Na kalli Sadiya dake shirya Abdul nace " Sadiya inna na kira.

Duk da ma nagane ba aiken gaske ta min ba kawai tana so inje inga ya salman da wata ne.

Don koda na fita sai naga fuskarta cike da fara,a tace min kin kirata?

Nima murmushi nayi nace eh inna tana zuwa ma.

Tace" to.

Daga nan na wuce kofar mama .
Duk yadda na daure abun ya gagara don haka kawai kuka na shiga yi ni kadai nasan me nakeji a zuciyata

A haka mama ta sameni tace"yau kuma meye faru?

Nace" mama ya salman ya daina sona ya sami wata.
Chapter 31 · 0% Book details