← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 128

Sashe 7

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan dariya ta yi tace "wayyo rumaisa muje to.

Muka shiga ta nuna min komi sannan ta fita.

Bayan nayi wanka ta ban zaninta da t shirt na saka ina ma kaina dariya a madubi.

Itama ta shiga ta yi ta shirya sannan muka kwanta.

Bacci na rika yi da kyar na tashi nayi asuba na koma mama kyaleni tayi nayita sharar baccina har sha daya yunwa ya tashen.

Nayi wanka nayi brush na shirya sannan mama tace in tafi dining inje in karya.

Habawa nayita zuba kauyancina.

Da wuri ya salim yazo ya daukeni don gobe zamu wuce Abuja.

Mama ta bani waya. Karama Nokia tace in rike zamuna gaisawa.kuma ta bayarmin kaya kala bakwai amin dinki.

Dadi kamar zai kasheni.

Mun dawo da daddare ina parking inna ta sameni a daki.

Tace" ke shirin me kk yi hakane?

Nace " inna gobe ne tfyr tamu Abuja ai.

Tabe baki tayi tace " shiyasa kk ta rawar jiki haka .kinje kun gama munafurci da uwarki sai shigewa salim kk.to me zaiyi dake waye yasan asalinki?

Kaina a sunkuye tuni hawaye ya fara zubowa .

Saida ta kare min zagi tass snn tace" ki tashi kije kiyi wanke wanke tunda sammako zakuyi ga kuma zanin gadona guda biyar na jika ki wanke tass sannan ruwan kumfan ki je ki wanke ban daki. In kin gama Na daura pepe soup na ganda a wuta kiyi hadi ki Kira ya nuna ki sauke.gobe da ssassafe ki tashi ki hura wuta ki dora ruwan shayi saura ki kuskura ki in tashi in sami ba kiyi min yadda nace ba kiga abinda zan miki.

Ta na gamawa ta fita nasan dakin Abba zata tafi don yau gurkinta ne.

Na kalli agogo karfe goma har yayi da sauri na tashi na fita wanke wanke nayi na gama na kama wanke bedsheets inayi ina duba girkina har na gama wankin naje na karasa parking ina zaune a Palo har saida na sauke pepe soup din sannan na kwwnta a gajiye .

Asuban farko na Riga kowa tashi naje na hura huta na Dora ruwan tea snn na wanke ban daki don jiya naga dare yayi ina tsoro.wanka nayi nayi brush hade da alwala.

Kamin inna ta fito har na shirya tsaf don har da ki da tsakar gida na share.

Shida saura ta shigo ta sameni a shirye tsaf.

Na gaisheta harara ta watsa min tace " kina ta rawar jiki zaki Abuja wai har kin gama aikin ne?

Nace"I na gama

Tabe baki ta yi ta shige ciki naji tana tashin su sadiya.daga bacci sai fada take musu.

Bayan mun karya karfe bakwai muka dauki hanya.
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

➡ page 6
Mun isa Abuja lfy.
Nikam sai kallon kauyanci nakeyi.lallai Abuja babban birnine .

Gidan kawu kasim kam ba magana don ya tsaru iya tsaruwa kai gabadaya anguwan haka gidajen suke sai ka rikice ka rasa wanne yafi.

Muna sauka sai ga fa'iza wacce take bin ya salim da kuma Dan karaminsu hakim.

Da fara,a suka mana sannu da zuwa.

Fa,iza ta dauki kayana mukayi ciki.anan naga mummynsu ita ma da fara,a tace" mutanen kano oyoyo marabanku da zuwa.

Na Dan russuna nace" ina kwana aunty.....

Cike da fara a tace" aa kinga' yata kuje ciki kiyi wanka ga breakfast na shirya muku a dining in kun gama kije ki kwanta ki huta.

Ta dafa kafadana ta na murmushi tace" in yaso sai mu gaisa a nitse.

Naji dadin yadda suka karbeni sosai.

Faiza ta kaini dakinta ta nuna min ban daki nayi wanka na canza kaya na fito dining tuni ya salim da hakim kam suke jira. Anan fai,za ta musu serving ta kalleni tace" rumaisa me zan sa miki.

Nayi murmushi nace komi ma na inaci.

Tace"wow ya salim na sami ' yar uwa.

Dariya yayi yace" sai kuyi ta ci.

Itama dariyar ta yi sannan ta sakamin dankali soyayye da kwai sai pepper soup na kayan ciki.sannan ta tura min kayan tea itama ta hada nata

Mun fara ci tace"wayyo ya salim na manta ban gaya maka abinda ya faru a BEYHAD ba.

Ya salim yace" an wuceni sosai ko.

Sai lokacin hakim yace" ya salim series ya fara dadi kasan me ya faru?......

Fa,iza tayi saurin fadin " MAYA ta kashe maman ARJUN.

Da sauri yace "don Allah fa an kamata?

Hakim yace ina za,a kamata ka mantata ne ai tuni ta yi makirci wai ta mutu arjun ya kasheta .aka kama arjun aka jefashi prison.

Ya salim ya Dan dafe kai yace" ai dama nasan za,ayi haka.don she is very dangerous.

Haka suka dinga hiran series har muka gama break fast.muka dawo Palo .

Ya salim kam yana da saukin kai don hira yake da kannensa sosai ba kamar salman ba.

Nan da nan na sake .faiza ta dinga koya min ado .yayinda mummy kuma take koya mn girki zamani kala kala.

Yauma bayan mun fito daga kitchen wanka mukayi ina bayan mun gama shiryawa na kalli.fa,iza ina murmushi nace " faiza shigarki tn burgeni wlh naga ke baki damu da saka Riga da siket ko da zani ko wando sai dogayen riguna.

Tace " ni banson abinda zai takurani ne rumaisa don nafi feeling free a cikin dogayen riguna.

Ta karaso kusa dani ta zauna tace'kema in kina so ki fara sawa.

Na tabe baki nace " ina na ga kayan ma tukun dududu dogayen rigunana basu wuce uku bane.

Ta yi dariya tace " kar ki damu ina da sabbi na zaman gida guda biyar zan baki kuma nasan zamuje shopping in daddy ya dawo zai bamu kudi.sai ki zabi iya son......
Karar wayar ta ne ya katseta ta dauko sai naga ta saki murmushi ta daga hade da limshe ido tace" hello yaya.

Ta danyi shiru snn tace"yaya munyi missing dinka sosai yaushe zaka zo Abuja?

Ta sakeyin shiru snn tace " gata nan muna tare a bata ne?

Da sauri ta mika min waya hade da fadin ya salman ne.

Na karba da nasa a kunne nace" yaya ina wuni?

Lfy.ya fada snn yace" me ye full Name dinki da kk using a school?

Nace RUMAISA IBRAHIM AHMAD.

Yace " OK

Sannan ya kashe.na mikawa faiza nace ya kashe ta karba tana murmushi tace gaskia wnn guy din zai kasheni da sonsa.

Zaro ido nayi ina kallonta nace waye faiza?

Ta mika min wayar ta ina dubawa photon ya salman na gani cikin kakin sojoji.

Rass naji gabana na faduwa na mika mata da sauri nace" faiza ai yaya salman ne me ya hadashi da kayan mugayen nan kuma?

Dariya ta yi ta zauna tace" kina nufin baki San yaya soja bane?

Na girgiza mata kai snn nace ban Sani ba wlh.

Tace to soja ne ki Sani daga yau .

A tsorace nace " ya rasa abinyi ne.......

Dariya ta yi tace" aa ra,ayinsa ne kawai.

Shiru nayi ban kuma cewa komi ba.

Tace "wlh rumaisa son ya salman nake kamar zan mutu wlh ko rumaisa ni inaga zan fada masa kawai duk abinda zaiyi ma yayi na gaji da noke noke.

Nan da nan annurin da ke fuskata ta gushe.na rasa dalilin da yasa maganar ta ya ban haushi.

Har ta gane tace" lfy rumaisa .

Nayi ajiyar zuciya nace" hmm faiza zanso ace ke ce matar ya salman amma kinsan ya salman ba wacce yake so kamar Salima to ya zakiyi ki cusa kanki ? Kuma inna ma dasu sadiya sonta suke kamar zasu hadiyeta tsabar alherinda take musu.

Jikin fa,iza a mace tace " hmm ai rumaisa ni kaina nasan labarin wnn salimar tashi bansan ya zan yi ba sakina tace min yana sonta sosai.

Nace abin takaici wlh kuma ma naji ance iyayenta sunce baza su bashi ita ba amma sai dagewa yake ko me ya gani a jikinta ne oho.

Faiza ta danyi shiru snn tace" ni fa inaga daddy Na zan fadawa .

Nace eh kin kawo shawara kuma wlh zasu amshi maganar hannu bibbiyu sabida zumunci ya kara dorewa.Allah dai ya sanya alheri.

Tana murmushi tace amin sis Na gode da kulawarki gareni.

Gaskia faiza ba karamin so takewa salman.

Nayi wata Na daya Abuja .ana saura one week a bude school ya salim yace in shirya salman zaizo daga Lagos mu wuce kano tare.

Kawu kasim ya bama aunty Zuwaira kudi masu yawan gaske yace akaini shopping Na sayi duk abinda nake so.

Murna Na dinga yi nan muka shirya da faiza muka tafi da Momy gaskia nasha siyayya kam masha Allah. Har waya Na canza katuwa nima Na shigo gari.

Ko da muka dawo faiza ne ta koya min yadda zan dinga amfani da wayar nan da nan Na gane komi.

Wai sai ga rumaisa a Facebook,WhatsApp.har da Instagram
Tunda na sami waya bana komai sai aikin danne danne.

Fa,iza ta shigo da sallama ban ma jita ba ta wuce toilet wanka ta yi ta fito ta zauna gaban mirror ta fara kwalliya.

Ajiye wayar nayi nace " to sai ina da wnn yammaci ko zamuje shan ice cream?

Ta harareni ta cikin madubi tace " wani ice cream kinaga har ya salman ya kusa shigowq Abuja ban mushi kwalliya ba.

Dariya nayi nace " to yanzu wnn adon duk na yayan ne?

Ta yi fari da ido tace kwarai da gaske.

Nace " yayi👍🏻

Ta tashi ta dauko dogon riganta na atamfa tasaka ta zauna ta murza daurin Dan kwali har gaban goshi ta zubo da gashi kan kafada.

Dariya nayi nace abin naki fa da gaskene.to sis ya sunan daurin nan?

Tace" sunansa" ture kaga tsiya"

Na saka dariya nace aikuwa na gani matar soja

Ta daga min gira hade da fadin " yessss

Sannan ta dauko turare ta fara fesawa da sauri na tashi gudun kar ya shige min hanci.

Aikuwa cikin rashin sa,a ina mikewa ta fesa setin hancina.

Wayyo nan da nan na rikice numfashina ya sauya kirjina ya fara toshewa.

Jifa ta yi da turaren ta kamani tana " na shiga uku rumaisa asma dinki ne ko sorry ina inhaler dinki.
Chapter 7 · 0% Book details