← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 238

Sashe 92

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalamanta sun karya zuciyarshi baisan sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, Zahra dake kallon su tuni hawaye sun wanke fuskarta ga wani farin ciki da ya lullu6e ta na ganin Unaisah, Jikin chief owais yayi sanyi lakwas tsantsar tausayinsu ne ya kama shi, ba shi ba hatta Hajiya saratu sai da taji tausayinsu duk da bakomai ta sani ba dangane da rayuwar su ba.

"Taj Ina mijina? Ina uzair! nasan Yana atare ku? Ka faɗa min taj meyasa kuka gudu daga gida? Tsawon shekara da shekaru baku ta6a waiwayena ba? Laifin me nayi maku taj? Idan wani abu ne yasa kuka gudu meyasa baku sanar dani ba? Harga Allah bakuyi min adalci ba taj! dai dai da rana ɗaya baku ta6a nema na ba ko da awaya ne...." Daƙyar ta ƙare maganar, Lokaci ɗaya ta yanke jiki zata faɗi da sauri taj ya tarota ta faɗo kan kirjinsa.

Da sauri zahra ta karaso gabansu tana kuka, zuƙunnawa taj yayi a hankali ya kwantar da kanta bisa laps din sa, har lokacin Angel tana a durkushe kan gwiwowinta da karfi take furta"Aunty aneelerh ki tashi! Dan Allah ki tashi wayyo Allahna daddy ka ce mata ta tashi" duk tabi ta rude zahra ma kukan take tana ambaton sunanta, Hajiya saratu ta kasa furta komai, lamarin ne da ta6a zuciya..

robar ruwa mai sanyi chief ya dauko daga kan table, Ya nufo wurinsu Ya buɗe murfin tare da mika ma Taj, Hannunsa na kerma Ya kar6a Ya tarfa ruwan a tafin hannu Ya watsa mata kan fuskarta, nan take taja mumfashi tare da furzar da shi...

Cikin karyayyar murya ya furta"Anila! dan Allah ki saurareni, wallahi bada son ranmu muka gudu ba, mummunar ƙaddara ce ta afka mana wadda tayi silar barinmu gida..., na rasa komai nawa Aneeleeh..." ya faɗa yana kallon cikin idanunta, dakyar take kallon shi, wani irin azababben ciwon kaine Ya far mata, ita kadai tasan halin da take a ciki.

"Nasan zaki fahimce ni Aneeleerh, har abada kinsan bazan Iya gudunki hakanan ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, dukan mu babu wanda baiyi kewar rashinki ba, kuma ko bayan da muka gudu kina aranmu bamu manta dake ba....."

"Taj ina mijina...."! Gabansa ba karamin faduwa yayi ba, kallon chief yayi da sauri ya girgiza mashi kai alamar kada Ya faɗa mata, saboda a halin da take ciki muddin suka sanar da ita tsaf zata iya zaucewa.

"Aneelerh, bansan Ina uzair Yake ba! Idan ba zaki manta ba, ba atare muka bar gida ba, adaren ranar da abun ya faru kinzo har gida kin same ni kina kuka kika ce uzair bai dawo ba, har na kwantar maki da hankali, tun daga wannan lokacin ban ƙara sanya uzair a idona na, amma muna nan muna bincike akanshi, in sha Allah shima zamu gano shi.

zuciyarta ba karamar karaya tayi ba, tuni ta sake fashewa da wani sabon kukan.

Kafin wani ya sake magana a cikin su, wayar Hajiya saratu ta fara ringing, da sauri ta zaro wayar daga cikin handbag dinta, ta duba mai kiran ta, p.a din tace, picking call din tayi"Okey, Gani nan zuwa yanzu nan.." ta faɗa tare da katse kiran ta dago ta dubi chief.

"My son yakamata na tafi, naso in tsaya amma kirane na gaggawa, duk halin da ake ciki pls ka sanar da ni..." ta fada cikin saurin murya, kafin ta dubi su Zahra.

"Zahra, Ni zan wuce, in sha Allah idan na samu time zanzo asibitin in duba mara lafiyan..." tayi masu fatan Alkhairi, godiya suka dinga yi mata, Har bakin mota chief tare da zahra suka rakata, akan idonsu motar ta fice daga gidan.

Dawowa sukai wurinsu Taj dake a durkushe ƙasa.

"Taj baka fadamin meyasa kuka gudu ba..."? Cikin jin ƙunar rai ta jefa mashi tambayar.

Atakaice ya labarta mata abun da ya faru da su, tun farkon da suka fara yi ma Alhazawan nan leƙen asiri da kuma farmakin da suka kawo mashi atsakar dare harya gudu da Angel....."

sai dai bai sanar da ita wayar da uzair ya kira shi ba ya dai ce shi baisan meya faru da uzair ba, har yau suna neman shi ba su gan shi ba, hankalinta yayi mugun tashi jin wannan musifar data afka masu, hatta zahra tayi matuƙar firgita jikin ta sai tsuma yake abun ya bata tsoro...

"Shiyasa bamu neme ki ba, saboda rayuwarmu tana a cikin hatsari, idan har miyagun suka san muna raye ba za su kyale mu ba, don dole muka killace ce kanmu kafin Allah ya tona asirin su"

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji! taj wannan wani irin tashin hankaline! Ni dama saida raina ya bani ba hakanan kuka gudu ba, Allah Yasa basu kashe uzair ba, nama san mawuyacin abune uzair ya rayu watakil sun kashe min shi...." bai bari ta ƙare maganar ba, Ya fara lallashin ta dakyar Ya shawo kan ta....

Zafafan hawayene suka cigaba da wanke kuncin ta,

"Boss!" chief ne Ya kira sunan shi

"Na'am yalla6ai"

"Ina son magana daku, ban da unaisah"

A hankali Ya ɗago da Aneeleeh, da sauri zahra ta zuƙunna tare da tallabo ta don gaba ɗaya jikin ta ba kwari dakyar ta samu ta miƙe.

Unaisah dake kallon su ta shiga ruɗani tunda chief Yace Yana son ganin su ban da ita...

Ruƙo hannunta taj yayi, suka nufi sofas din wuri ya zaunar da ita

"Daddy meya faru"?

"Kada ki damu, magana ce mai mahimmanci zamuyi, Idan muka gama zamu sanar dake, cike da gamsuwa tace toh

"ɗazu Kin faɗa min kina jin yunwa, ga snacks nan da juice ki sha kafin mu gama magana" yatsun hannunta har kerma suke wurin daukar burger ta fara cin ta.

idanunta akan su Aneelerh dake tafiya suna nufar can nesa da ita, zuciyarta cike fal da farin ciki, kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna, bakinta yaki rufuwa sai faman tariyo fuskar aunty aneeleeh takeyi, burinta su gama maganar don ta tambayeta ina ƙanin ta da daddynta ya bata labari ta haifa mata....

Bayan kowan nan su ya zauna kan kujeru suka nutsu suna jiran jin me chief zai sanar da su

"Inaso ku faɗa masa abun da ya kawo ku neman ƴar sa"! Ya faɗa batare da ya ɗago ya kalli waninsu ba, aɗan ruɗe Taj Ya kalli su Aneeelerh.

Baiwar Allah tama rasa ta ina zata fara, saboda tasan ba lallai Ya amince masu ba.

"Aneelerh kinyi shiru! Faɗa min meyasa ku ka zo neman Angel? Tun jiya chief yayi min bayanin zuwan ku amma bansan cewa ku bane, nayi mamakin ganin ku! Tayaya har kuka gano inda mu ke!? Ya fada cike da son jin ƙarin bayani.

Cike da fargaba Aneeleeh ta fara zayyana masa abun da ya faru na bayyanar benazir, bata 6oye mashi komai.

tunkafin ta ƙarasa maganar yanayin fuskar taj ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, kwata kwata baiji dadin bayyanar benazir ba, saboda tafi ta aransa baya buƙatarta arayuwar shi, wani irin ɗaci yaji aran shi, Aneeelerh ta fama mashi tsohon raunin dake a zuciyar shi.

ko sunan ta baison ji, aranshi ya arayyana da ranta da lafiyarta tsawon shekara da shekaru bata ta6a neman su ba? Idan har shi bata neme shi ba ay yakamata ko yarta ta nema baisan wata irin zuciya bace a kirjin benazir ya riga da yasan halinta domin kuwa ba zai ta6a manta irin rayuwar auran da sukai da ita ba, macace mara kunya batasan darajar aure ba, ta azabtar da shi da soyayyarta.

gaba ɗaya sun lura da yanayin shi, kamar baya atare da su, Aneeleerh duk tasha jinin jikin ta, dafa kafadarsa chief yayi a hankali ya kallesa idanunshi sun kaɗa jawu"dan Allah kada kace inyi hakuri, saboda bana jin zan iya yafewa benazir, hasalima ban yarda cewa dagaske ta damu da mu har haka ba, Allah kadai kasan manufar da take da ita akan mu, ba zan ta6a yarda da benazir ba, matar da ta tafi tabar yarta a kwamin wanka, taje can tana yawon biɗiɗin ta tsawon shekaru bata ta6a neman mu sai yanzu"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunsa tuni sun wanke fuskarshi hakan ba karamin ɗaga hankalin zahra da Aneeerh yayi ba..

Shi kadai yasan ƙunar da zuciyar shi take yi mashi

Shiru chief yayi sam ya kasa furta magana,

Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"dan Allah taj kayi hakuri mu manta da abun da ya wuce, Benazir tayi nadama, neman ku take ruwa ajallo don ta nemi yafiyarku, wallahi taj ta riga ta gane kuskurenta" tana magana tana marairaice mashi fuska don ya tausaya masu"ka dubi girman Allah ka kuma duba darajar yarinyar dake atsakaninku ko dan saboda ita yakamata ka sassauta mata, Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu da muke ƴan adama, taj ita kanta bada son ranta ta gudu ba kamar yadda na faɗa maka asiri akayi mata, yakamata kayi nazari kada ka yanke hukunci cikin fushi, nasan Benazir bata kyauta maku ba, amma ka duba pls, tana fa sonku shiga akayi tsakaninku saboda babu yadda za'ay uwa ta haifi ɗan sunna tayi watsi da shi......"

babu alamun taj zai fahimci maganar ta, idanunsa sun kaɗa jawur bakomai yake tunano ba face lokacin da ta ɗauki cikin unaisah hauka ne kadai batayi ba saboda ta tsani ciki, har fadi take zai bata mata shape din jikin ta, bayan haka tasha yin yunƙurin zubda shi Allah bai nufa ba.

"Pls, koda bazaka yafe mata ba, dan Allah ka amince Unaisah ta gana da mahaifiyarta..." kafin ta ƙare maganar yace

"Aneelerh kin riga da kinsan ƙiyayyar da unaisah take ma benazir, tunkafin ta mallaki hankalin ta, unaisah bata buƙatar mamanta, Nima kuma bana bukatarta...." hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Ga samu ga rashi, kallon chief Aneelerh tayi ya kasa kunne yana sauraron su.

"Dan Allah ka taimaka mana ka sanya baki a maganar nan!...." ta fada hawaye na bin fuskarta.

Duk yadda taj yaso hana chief magana sai da ya sanya baki
Chapter 92 · 0% Book details