← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 238

Sashe 149

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungumar da chief yayi mashi ba karamin kashe mashi karfin jikin yayi ba, Zuciyar shi taso ta karaya sai dai baya jin zai iya amincewa da su, kalaman chief sun tsaya mashi aranshi sun kuma sanya mashi kokwanto a tunanin shi, ga wani irin yanayi da yake ji mara misaltuwa atare da shi yana ji kamar suna da connection da chief, sam ya kasa ta6u ka komai yanayin fitar numfashin shi sam babu kwanciyar hankali.

Lumsassun idanunshi ya ɗaura akan hannayen chief daya dafe flat tommy din sa, Har cikin ran shi baiji dadin bijire ma shin da yayi ba, baisan ya akai yake jin mutumin aran shi ba, Yana matuƙar ƙaunar Chief baya son bacin ran shi.

Komai dake faruwa akan idonsu big guy, sun yi shiru suna jira suka ga martanin da zai mayar wa chief.

A hankali Danish ya daura tafukan hannayen shi akan na chief ya damƙe su sosai yana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa, In a weak voice Ya furta"Ka yi hakuri, bazan iya ba ku hadin kai ba, pls kada ku tursasa min akan abun da banyi niya ba.." yana faɗan hakan ya 6an6are hannun chief daga ruƙon da yayi mashi ya fuce daga dakin, wani irin jiri ne ya kusa ɗibar shi da sauri ya dafe ƙofar da tafin hannun shi.

Da ƙarfi Big guy ya ture kofar Observation room Ya futo Yana huci Ya nufi Danish dake kokarin komawa gurin su Sajeed, da sauri sauran Jami'an dake a tare da shi suka biyo bayan shi ganin yadda ya fusata, sun san halin shi yana da bad temper.

Taj dake abiye da su hankali atashe Ya ke danna wayar sa layin Salsabeel ya kira cikin sa'a ya ɗaga ko sallama baiyi ma shi ba ya faɗa mashi abunda ke faruwa, salsabeel ya zabga salati dama sai da yai fargaban faruwar hakan, saboda shi yasan wanene Danish, mutum ne mai kafiyar tsiya ga girman kai da rashin yarda.

"Yanzu haka ina acikin head quarter din, wallahi nasan za'a rina shiyasa na yanke shawarar zuwa saboda shi" acewar salsabeel bayan sunyi sallama taj ya mayar da dubanshi ga big guy wanda tuni Ya cimma Danish wani irin kukan kura yayi tare da kai hannu Ya damƙi kwalar rigar shi, Jami'an dake a kewaye da su suka rurruƙe hannun big guy suna kokarin su raba tsakanin su.

Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana, Kusan atare su Unaisah suka miƙe idanunsu azazzare suke kallon su cike da faduwar gaba.

Da wata irin kakkausar murya ya furta"Who the hell are you? ɗan uban wanene kai a kasar nan? Me kake taƙama da shi ne huh? Kana da wani gata ne daya wuce Allah da shi chief din ne? Saboda tsabar rainin wayau yana magana kana amsa mashi da gira tsaran wasan ka ne shi"? Ya faɗa yana bin shi da wani ƙasƙantaccen kallo, big guy irin bauɗadɗun mutanan nan ne masu saurin fushi, wani lokaci sai daga baya su yi dana sani, shiru Danish ya yi batare daya tanka ma shi ba.

Big guy yaci gaba da fadin"Da kasan wanene chief da ba ka yi mashi haka ba, in ba dan aikin shi ba kai ka kai matsayin da zai kula ka ne? Ka rasa wa zaka yi disrespecting sai mutun mai kima da daraja a idon mutane, mutumin da ya ke hana idon shi bacci don ya taimaki rayuwar al'umma, mutun mai tausayin da jin ƙan na ƙasa da shi..." ya faɗa A harzuke Yana kallon cikin idanun Danish wanda yayi kasaƙe yana kallon shi, karfin halin mutumin ya bashi mamaki yadda ya damƙi kwalar rigarshi batare da jin shakkar yin hakan ba.

"Sir, ka yi hakuri ka daina yi mashi faɗa, me zai hana mu lallashe shi ni inaga idan muka bi shi ta lallama zai bamu hadin kai kodan abunda muka ji wurin yan uwanshi dole muyi mashi uzuri" CI ne yai maganar cikin kwantar da murya

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Agent zahra Yace"sir Please, ka kyale shi, He's still young, it's not your place to argue with him, He doesn't know anything, We need to persuade him gently." cikin tausasa murya ya faɗa yana kallon fuskar Big guy tamkar baisan suna magana ba Ya haɗe rai ba annuri ko kaɗan akan fuskar shi.

Dafa kafaɗar shi COO yai"Allah Ya huci zuciyar ka Yalla6ai, mu kan mu bamu ji dadin abun da yayi ba amma yakamata muyi mashi Uziri saboda baisan komai ba..."

bai kare maganar ba Unaisah ta fashe da matsanancin kuka, kamar jira su Batool su ke ta fara kuka suma suka fashe da kukan gaba daya sautin shesshekar kukan su Ya karade kunnuwan jami'an dake agurin, tsabar tashin hankaline Yasa suka fashe da kuka dama tun da suka fito daga dakin tambayar zuciyarsu araunace take saboda raunin da aka fama masu

ga kuma wani tashin hankalin da suke kallo duk da basu san meya faru ba amma sun fahimci Danish ne yayi wani abu badai dai ba.

"OMAR, pls ya isa haka! Ka sake shi, nayi magana da Salsabeel awaya ya faɗa min yana acikin head quarter din yanzu zai shigo"

idanun shi jawur Ya dubi Taj a fusace Yace"Taj I won't let him go. He must return and answer the chief's questions, ya 6ata min rai ya rasa wazai disga sai chief din mu? Tsaran wasan shi ne? duk kokarin da ya ke yi akan su shi baya gani ne? Ni bana son mutun mara ɗa'a irin shi ..."

Ya fada tare da cije le6en shi ya maida dubanshi ga Danish wanda tuni Jikin shi Ya fara kakarwa wata irin zufar 6acin rai ce ta fara tsatstsafo mashi, Numfashin shi ya fara hauhawa yana fita cikin sauri, lokaci daya temperature din jikin shi ya ɗau wani irin zafi, idanun shi suka rune zuwa Ja.

"Yaya Omar dan Allah Ka sake shi, nayi maka alkawarin zan shawo kan shi" cikin shesshekar kuka Unaisah tayi maganar

Haris yace"dan Allah Ya Omar ka ƙyale Danish, Idan laifi yayi maku ku yi hakuri zamu fahimtar da shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya yi hakuri Ya saki Danish

Adaidai Lokacin da Salsabeel Ya faɗo arean da suke yana faman wurga idanu don ya gano inda suke kwatsam idanun shi suka sauka akan gungun jami'an da su ka kewaye su.

Gaban shi ne yayi wani irin faduwa aguje ya nufe shi har yana bangaje jami'an dake sintiri kamar mahaukaci haka suke kallon shi

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Yana ƙarasawa ya sanya karfi ya raba tsakanin big guy da Danish Yana faman haki ya dubi Danish wani irin faduwar gaba yaji ganin sa6ar majici akan wuyan shi babu wanda Ya lura da sabar sai shi da Allah ƙaddara zai ganta, wahalallan Yawu ya haɗiya la66anshi na rawa ya furta"Danish, please...don't. Please, Danish, try to control your anger.."

gaba ɗaya jami'an sun ruɗe da ganin yadda Salsabeel ke lallashin shi, Musamman Big guy ranshi ya ƙara 6aci a faɗa ce yace"meya sa ka ke bashi hakuri"?

Salsabeel bai tanka mashi ba saboda tashin hankalin da yake tunkaro su batare da su sun sani ba, In har evil heart dinshi ta motsa zai rikiɗa ne ya canza halitta, ya tarwatsa head quarter din gaba ɗayanta ba ƙamar 6arna zai yi ma su ba.

Da hannu ya dafe saitin zuciyar Danish, Ya marairaice mashi fuska tare da girgiza mashi kai alamar A'a...

gaba daya jami'an sun kasa fahimtar me Salsabeel Ya ke nufi!

Wani irin dogon numfashi Danish Yaja cikin zafin nama Ya bangaje hannun Salsabeel daga kan kirjin shi yana faman fitar da huci mai zafi ya miƙi hanya, aguje su Unaisah suka bi bayan shi suna kwala mashi kira ko kallo ba su ishe shi ba, bai sha wahalar gano kofar da suka shigo Soc din ba Ya fu ce daga ciki Ya nufi main enterance gate na head quarter din.

Kafin karasawar shi big guy ya kira layin ɗaya daga cikin jami'an dake tsaron gate din Ya basu Umarni karsu kuskura su bar shi Ya fita.

Lokacin daya karaso Yana tafiya kamar baya acikin hayyacin shi, hankulan jami'an dake sintiri gaba daya ya dawo kan shi, fisatattun jami'an dake tsaron gate din suna ganin shi suka gane shi ne matashin da aka basu umarni karsu bari ya fita, aikuwa azafafe suka yi mashi ƙawanya kamar zasu rufe shi da bugu.

Yan uwanshi sai kuka suke suna ambaton sunan shi hadi da yi mashi magiya akan ka da ya tafi ya bar su, babban abunda suke ma fargaba in ya fita ina zai dosa?

Dakyar chief ya iya lallashin zuciyarshi cike da rashin ƙwarin jiki ya fito daga ɗakin Ya nufi su big guy dake atsaitsaye curko curko sun kasa kunne suna sauraron Bayanin da Salsabeel ya ke yi masu dangane da Danish

"Ga chief nan" taj ne Ya fada kusan atare suka kai duban su gare shi, damuwa ce karara akan fuskar shi.

Bawan Allah da buɗar bakinsa sai cewa"Ina Danish? Ina sauran yaran"? Kafin wani daga cikin su Ya bashi amsa sautin ringing wayar big guy ya katse hanzarin su

Da sauri Ya kara wayar a kunnan shi.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Sir, Yaron nan fa Ya fita! Mun yi kokarin mu dakatar da shi amma mun kasa, gaba ɗaya ya watsar da jami'an da sukai kokarin hana shi fita..." a kidime Big guy ya furta"what? Ya fita! Garin yaya hakan ta fadu"?

Wani irin faduwar gabane Ya ɗarsu a zuciyoyin su, sunyi matukar mamakin jin hakan shin tayaya akaima har ya iya fin karfin jami'ansu Ya fuce daga head quarter din?

"Yaran suna nan, amma ɗaya daga cikin ƴan matan mai launin ido ruwan toka ta kubce mana, yanzu haka wasu daga cikin jami'an mu sun bi bayan su"
Chapter 149 · 0% Book details