← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 238

Sashe 9

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra tace"bawani nan, shine Yaƙi zuwa ɗaukarshi da wuri, Yabar shi a school yana ta jira"

"Gaskiya mahboob Baka kyauta mana ba, saboda Allah, Haka akeyi? Sai kabar mana Yaro ga Yunwa" Ummi ce ta faɗa tana satar kallon baby junaid duk don ta nuna mashi taji Haushi.

"Ay mashi uziri mana, hakanan dai Mahboob bazaiƙi zuwa ɗaukar baby junaid ba sai dai idan wani uzirinne Ya ruƙe shi" mami na fadan hakan Mahboob Yace"ay har bayani nayi ma zahran, motana ne Ya samu matsala sai da nakaita gyara, in sha Allah Hakan ma bazata ƙara faruwa ba zan dinga zuwa ina dauko shi akan lokaci"

Ummi tace"haka Yakamata"

"Zonan babyn mommynsa" acewar Ummi ta fada tana miƙa mashi hannu, maƙe mata kafaɗa yayi alamar bazaije ba, Saima Ya ƙara ƙanƙame Zahra, mami na dariya tace"In banda abunki sai kace bakisan halinsa ba idan Yana fushi Yafi buƙatar jin ɗumin mommynsa,"

"Ina auntyn tawa take"?

"Tana a kitchen"

Maimaita kalmar kitchen Zahra tayi, aranta ta furta me kuma Aunty Aneelerh take yi a kicin"? Batayi Ƙasa a gwiwa ba, Ta nufi kitchen din Mahboob Har Ya zauna kan sofa, sai kuma Ya miƙe Yabi bayan zahra.

Tunkafin su ƙarasa kitchen din suka hango Aneelerh ta haɗa uban gumi a kitchen tana girki, Ita kadai.

Sam bata Ji alamar shigowarsu ba, ta zage damtse sai motsa miya take Yi

"Aunty Aneelerh"? atare suka haɗa baki wurin kiran sunanta, da sauri Ta rufe soup pot din, Ta juyo tana fuskantarsu, kafin ta ɗaura idanunta akan Baby Junaid,

Murmushi ta sakar masu "Sannunku da dawowa,"

"Yawww, Auntyna, Yau ke kike Aiki akitchen Ina Ana"? Zahra ce ta jefa mata tambayar, Mahboob Yace"Allah yasa dai lafiya"

Girgiza kai tayi cikin sanyin murya ta soma magana"ba lafiya...." gaba ɗaya ta labarta masu abunda Ya faru zuwansu dakin Ana tare da su mami, Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yayi ba, Musamman Mahboob.

"Bansan Ya zanyi ba, Taƙi faɗa mana abun da ke damunta, Ni tsorona kada wani abu Ya faru da ita" fuskarta da tsantsar damuwa ta furta maganar

"Nima hankalin bai kwanta da ita ba, dafarko nayi tsammanin Damuwar halin da ƴan uwanta suke aciki ne ke damunta, ashe ba haka bane, daga gareta ne" Acewar Mahboob.

Kafin Zahra ta furta magana baby Junaid Ya fashe da kuka, Dama ranshi a6ace Yake, da sauri Aneelerh Ta miƙa hannu ta kar6e shi cikin sigar lallashi take jijjiga shi tana fadin"Am sorry My baby boy, kayi hakuri nasan nice na 6ata maka rai,' muryarshi da shessheƙar kuka Yace"wayyo Allah mommy, Kuna ta surutu Kin ƙi kulani, baki missing ɗina ba" dariya zahra da mahboob su ka yi, hakan Ba ƙaramin 6ata mashi rai yai ba, Hada Jifar Su da harara

Shafa sumar kanshi tayi"Na kar6i laifina, ay min afwa... " zumbura mata baki yayi,

Zahra tace"aunty Aneelerh, Ki tafi dashi ɗaki Ni zan ƙarasa girkin, Inyaso da anjima Sai mu ƙarasa tattaunawa"

"Keda kika dawo daga aiki a gajiye kuma kike neman in bar maki girki, a'a gaskiya Ki bari na ƙarasa ai ba ni kadai nake yi ba, Tare da Ummi muke Yi, bata jima da komawa falo ba.. "

Kafin Ta ƙare maganar, Mahboob Yace"tun da tace zatayi kibar mata kawai, Nima saina tayata, baby junaid yana buƙatar kulawarki, Kije Ki lallashe shi"

Murmushi tasaki Tana kallonsu, Har cikin ranta take jin tsantsar kaunar Yan uwanta, Haɗin kansu Na burgeta, fatanta Allah Ya dawwamar da farin ciki arayuwarsu, Hakika suna kyautata mata.

"Nagode, zahra, Mahboob, Allah Ya barmu mun ku,"

Amsa mata su ka yi da ameen

"Zan shiga ciki, pls zahra Ki dafa mashi indomie" amsa mata tayi da toh, Bayan fitar Aneeleeh daga kitchen din, Mahboob Ya ajiye food basket din Junaid, Yabi bayan aneelerh hannun shi ruke da backpack din Baby junaid,

Bayan Ya ajiye mashi adaki, Ya fito Ya nufi nashi room din, shaf shaf Yayi wanka Ya sanya gajeran wando da ƴar singlet, Kafin Ya nufi kitchen don Ya taya zahra girki kamar wani mace, atare suka cigaba da kula da girkin, suna tattauna fira dangane da matsalar Ana.

"Amma kai a tunaninka meke damunta"?

"Sister Ni kaina nakasa gane wani tunani zanyi dangane da matsalar Ana, sai dai kawai mubita da addu'a, Allah ya yaye mata abunda ke damunta,'

"Ni aganina, Mu kar6i Contact din Ƴan uwanta , mu tuntu6esu may be sunsan meke damunta, tunda sunfi kusa da ita"

"Nima nayi tunanin hakan, Yanzu dai mu jira, zuwa lokacin da su Abie zasu dawo gidan, nasan zasu Kirata su tambayeta,"

"Hmm kana ganin zata Iya faɗa masu gaskiya? Bayan Aunty Aneeleeh tace tare da su mamie suka je dakin nata amma taƙi fada masu, ai ni aganina idanma akwai wanda Ya dace ta fadamawa baiwuci su mami dinba"

Jinjina kai Mahboob Yayi"kin fadi gaskiya,"

"Ni abunma Ya fara bani tsoro, da naji aunty aneeleeh tace Ana ta dinga kwala masu ihu tana fadin su fita subar mata dakinta, Anya mahboob bata da matsalar kwalwa?

Mahboob Yace"Bana tunanin hakan, wata'kil Aljanune suka shige ta, mu cigaba da tayata addu'a Allah Ya kawo mata saukin abunda ke damunta"

"In sha Allah zamuyi mata"

Daga haka basu ƙara magana ba, sun maida hankali akan Girkin da suke Yi.

Fitowa Aneelerh tayi daga Bathroom, Bayanta goye da baby junaid, tayi mashi wanka, sai faman hade mata fuska Yake Yi, Riga da wando ta Dauko ta zura mashi ajikinshi, ta feshe shi da turare, zama tayi gefen gadonta,ta ɗaura shi saman laps dinta, hannunta ɗaya dafe ta shi,tarasa meke yi mata daɗi, Ita dai Hankalinta bai kwanta da halin da Ana take aciki ba, Ji take aranta kamar wani abunne Zai faru, zuciyarta batayi mata daɗi, sam ta manta da baby junaid Tayi zurfi a tunaninta, Har Ya fara lumshe ido zaiyi bacci, Muryar Zahra ta fargar da su,

hannunta biyu ruƙe da plate din indomie, Sai tiriri Take Yi, daga saman indomie din ta shimfiɗa mashi Soyayyan kwai, Mahboob Yana abiye da bayanta, Hannun shi ruƙe da mugs biyu na kakkauran Tea.

"Sannunku da kokari, nasanya ku aiki ko hutawa ba ku yi ba"

"Pls ki daina fadin hakan, Mu yakamata mu Yi maki sannu, anbarki da girki a kitchen, Su mami suna a falo fira tai dadi" Mahboob Ne yai maganar

Asaman Table zahra ta daura plate din, Mahboob Ma ya sauke nashi mugs din, atare suka fuce daga dakin.

Baby junaid tunda yayi tozali da indomi Ya soma sakin murmushin murna, Har wani lashe le6ensa Yake Yi

"Mommy da zafi, kuma ni Yunwa nake ji Allah" ashagwa6e Yayi maganar

"calm down Your Mind my baby boy, Ni zan baka da hannuna, kasan dai mommy bazata bar baby junaid dinta Yaji zafi ba ko"? Ɗaga mata kai yai alamar"

"Yawwa my boy" ta faɗa tare dakai hannu ta dauki fork, ta soma nannaɗo taliyar tana hura mashi da baki idan ta huce saita tura mashi abaki, kusan atare suka cinye indomie din dakwai, Kafin suka sha tea din su.

"Kada kayi bacci, Yanzu za'a fara kiran sallar magrib," ɗaga mata kai yai alamar toh, Janshi ta soma yi da fira duk dan kada yayi bacci.

Bayan Kammala sallar Magbrib, A lokacin Abie da Uncle ɗan Iya sun shigo gidan, babu wanda Ya tuntu6esu da maganar Ana, sun bari ne sai sun huce gajiyar da suka kwaso ,Har saida suka kammala cin abincinsu, Tukunna Ummi ta sanar da su Halin da ake ciki, babu 6ata lokaci, Abie Yasa suka hallara A falon gidan gaba ɗayansu, Ana ce kaɗai ke babu acikin su.

Aneelerh da zahra da Mahboob suna zazzaune kan Carpet, A lokacin baby junaid Ya jima da yin bacci, Yana can kwance saman gado.

Abie da Uncle ɗan Iya suna a zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Abie Yana sanye da farar jallabiya ya manna farin glass a idanunsa, Yayin da Uncle ɗan Iya yake asanye da Riga Yar shara ta farin Yadi, daga ciki ya sanya gajeran wando baƙi.

Su Mamie da Ummi suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun biyu, dukansu Hijabai ne a jikin su. tamkar mutuwa ta gifta babu mai magana acikinsu, Har na tsawon mintuna kafin daga bisani Uncle ɗan Iya yayi masu gyaran murya, suka ɗago suna duban shi, da hannu Ya nuna Mahboob

"Je ka kira ta" Amsawa mahboob Yayi da toh, ya miƙe ya nufi bedroom din Ana, abakin ƙofar Ya tsaya tare da kai hannu yayi knocking kofar kusan sau uku bata buɗe ba, Har ya fara tunanin ko bacci tayi ne sai kuma Yajiyo mutsu mutsunta ta cikin ɗakin.

A hankali ta turo ƙofar ɗakin, tare da leƙo da kanta,

Ko da mahboob yai tozali da fuskarta sai da gabanshi ya faɗi ganin yadda ta kumbura suntum, idanuwanta sun kaɗa jawur, daga gani kukan take cikin yi

In a calm voice Ya furta"ina fata ban katse maki baccin ki ba"

Muryarta adisashe tace"ban kaiga Yin baccin ba,"

Jinjina kai yayi"Uncle ne yace in kira ki, su na a falo shi da su mamie da abie"

Shiru tayi jimmm kamar bazata motsa ba, har saida ya maimaita mata maganar tukunna tace Toh, ka jirani mu tafi atare"

"Okey"

Maida ƙofa tayi ta rufe ta, badajimawa ba sai gata ta fito sanye da doguwar riga, ta yafa mayafi akanta,

Jin ta ruƙo hannun shi acikin nata ne yasa shi saurin kallonta, sam hankalinta ba akwance Yake ba, bai yi yunƙurin raba hannun shi daga nata ba, A haka suka nufi falon, sai da suka kusa isa yayi saurin zame hannun shi daga nata, Takun tafiyarsu ne Yaja hankalinsu mami ga dubansu

Cikin girmamawa Ana ta gaishe da su, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana faman jan numfashi, bayan mahboob Ya zauna.

Abie dake kallon Ana Ya soma Magana a tsanake

"Inaso ki natsu ki saurare ni," jinjina mashi kai tai alamar toh

"Ki ɗauka tamkar mahaifanki ne suke yi maki magana, kada ki ji shakkun faɗa mana abun da ke damunki, saboda mu kaɗai ne makusantanki a yanzu, Haƙƙinmu ne mu kula da rayuwarki, Idan wani abu ya same ki ba zamu ji daɗi ba" wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa kalaman abie sun yi tasiri a zuciyarta.
Chapter 9 · 0% Book details