← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 238

Sashe 40

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskokinsu babu walwala, ruƙo hannunta kakansu yayi tare da mika ma taj, da mamaki yake kallonshi don bai fahimci me yake nufi ba, har saida yayi mashi da kurmanci Ya nuna mashi cewa ya tafi da ita, sun bar mashi ita, saboda tace in har basu bari tabi shi ba, to zata kashe kanta ne, shiyasa suka yanke shawarar kwara su bar mashi ita, don ko sun barta ba lallai su iya shawo kanta ba.

Babu yadda taj baiyi da su ba akan subar yarsu, hankalinsu sai yafi kwanciya idan tana akusa da su amma suka sanya kafiya akan dole ya tafi da ita, ganin ya turje ne yasa suka fada mashi cewa marainiyace, tun kafin ta mallaki hankalin ta iyayenta suka rasu, bata ta6a neman wani abu daga gare su tarasa ba, don haka sun bashi amanarta, yaji tsoron Allah ya rike masu ita amana su je can su yi aure, hawaye ne suka wanke fuskarshi, jiki asanyaye yasa hannu ya ruƙo hannun danejo,yayi masu alkawarin bazai ta6a bari ta nemi wani abu ta rasa ba, zai dauki dukkan wani nauyi nata zai bata kulawa, sunji dadin abunda ya fada masu a karshe sukayi bankwana da junansu, yaja hannun danejo suka nufi rigarsu Habu.

har sun fidda rai da sake ganin shi, tsawon kwanakin da yayi a rigarsu danejo kusan kullum sai sunzo neman shi a yar bukkarsa, sunyi mamakin ganin ya dawo masu tare da yar matashiyar budurwa, cikin harshen fulatanci danejo tayi masu bayanin komai dangane da taj...."

labarin tajudden da Angel ya ta6a zuciyoyinsu, har hawaye suka zubda masa saboda tsananin tausayin shi da suka ji, bayan komai ya lafa ya sanar da su zancen tafiyar shi, ba don sunso ba sukayi mashi fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa yaga yarinyarsa, kafin tafiyarsa saida suka hada mashi shatara na arziki, bayan haka suka yi masu rakiya har zuwa bakin titi, ba su tafi ba sai da sukaga ya samu motar hayar da zata shigar da shi cikin garin joss tukunna sukayi mashi bankwana.

Tun da suka shiga motar, danejo ta kankameshi, kamar wani yace zai kwace mata shi, wani irin mugun tsoron mutane take ji, mutun ɗayane ta yarda dashi ta kuma damka amanarta agareshi saboda tasanyawa ranta cewa bazai ta6a cutar da ita ba.

Kafin su karasa cikin garin, tuni bacci yayi awon gaba da ita, a yayin da kanta ke asaman kirjinsa, hankalin taj sam ba akwance yake ba, saboda fargaban kada miyagun da suka kai mashi farmaki su gansu, yasan muddin sukasan cewa bai mutuba, to kuwa zasu nemi hanyar da zasu kashe shi ne kamar yadda suka kashe dan uwansa uzair, mutuwar da tayi matuƙar girgiza shi, dabara ce ta fado mashi da sauri ya sanya hannu ya cire gyalen danejo da take daure qugunta da shi, ya lullu6e fuskarsa, Idanunsa ne kadai suke a bude.

Bayan isarsu joss, motar ta sauke su a tasha, driver yace ina kudin mota, sai lokacin ya tuna da baida ko sisi, sai dai kayan da fulanin nan suka bashi, hakuri ya bashi ya hada shi da katon dawon fura, mai motar baiyi gardama ba ya kar6a, ruko hannun danejo yayi suka soma tafiya atare har ya sama masu abun hawan da zai kaisu unguwar da su ke, kafin isar su tuni dare ya ritsa da su.

Da farin cikinsa Ya zo unguwar, amma lokacin dayaga gidajensu a kulle, nan take murnar ta koma ciki, tunkafin ma yaji abunda ya faru hankalinsa yai mugun tashi, baisan ina zai tsoma kanshi ba, ga yar mutane da yake ta yawo da ita, harta fara yi mashi kukan yunwa take ji, tausayinta ne ya kama shi, da ya san hakan zata faru dabai yi kuskuran tafowa da ita ba..

A bun hawa ya kuma tsaida masu, suka nufi gidan uncle abdalla da ita don ya ga ko sun dawo daga south korea, tunkafin me abun hawan da ya kawo su ya sauke shi ya hango gate din gidan a kulle alamar basa nan, tamkar ya daura hannu aka ya fasa ihu haka yaji.

Tunawa da amininsa muhsin wanda Angel ta ta6a sace ma matarsa waren takalmi yasa shi yanke shawarar zuwa gidan shi tare da danejo, yasan acanne zai ji komai daya faru bayan 6acewarsu

Basu sha wahala ba, cikin sa'a suka same shi agida, tare da matar shi, lokacin dayaji sallamar taj a firgi ce ya mike zaune yana kallon kofar shigowa falon, bai gane shi ba har saida ya cire mayafin danejo dake akan fuskarsa tukunna ya shaida shi, muryarshi na rawa yace taj! Dama kana araye? Tsawon lokaci muna ta neman ku babu kai ba uzair duka an nemi ku an rasa"? A rude yake jefa mashi tambayoyin, matarshi da sauri ta nufi danejo ta ruko hannunta suka zauna kan sofa, kafin ta mike ta shiga ciki ta kawo masu abinci da ruwan shi.

"Dan Allah abban muhsin kabarshi Ya huta, bakasan daga ina yake ba, sannan bakasan meya faru dashi! Idan har bai samu nutsuwa ba tayaya zai iya fayyace mana abunda ya faru da su"? Fuskarta a yamutse tayi maganar, jinjina kai yayi fuskarsa da tsantsar al'ajabi yace da taj su shiga ciki yayi wanka ya canza kayan jikin shi, yaga duk sun jigata kamar na almajirai,

Bayan sun huta, sunci sun koshi, har bacci yayi itama danejo ta dan runtsa, wuraren karfe shabiyu na dare yafarka ya taras da muhsin ya zabga uban tagumi yana kallon shi, mamakine yacika shi.

"Ka yi hakuri taj, kada kaga na takura maka, wallahi na damu da rashin ku, hankalina bazai ta6a kwanciya ba har sai ka fadamin meya faru da ku da har kuka gudu aka neme ku aka rasa......"

Mikewa zaune taj yayi, kafin a tsanake ya labarta masa komai daya faru, wani irin matsanancin kuka mai cin rai muhsin ya fashe dashi, bakomai ya firgita shi ba ya kuma bashi tsoro face mutuwar amininsu uzair ta yi matuƙar girgiza shi, cikin shesshekar kuka ya ke fadin"taj dama abunda ya faru daku kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan wata irin masiface, Uzair ya mutu, Angel ta 6ace, rana ɗaya an tarwatsa farin cikin zuri'arku, in sha Allah sai Allah ya saka maku wannan zaluncin da akayi maku....."muhsin ya yi kuka tamkar ransa zai fita,

Lallashinshi taj ya somayi yana fadin yayi hakuri komai ya riga daya wuce, yanzu shi damuwarshi ina aneelerh take matar uzair"?

Daƙyar muhsin Ya samu nutsuwa, ya fara mashi labarin abunda Ya faru bayan 6acewarsu,

Yaji dadin jin cewa Aneelerh tana agidan iyayenta, abun da ya faranta ranshi, Yaron da yaji ta haifa masu, tunkafin ma yaganshi Yaji Ya kamu da kaunarsa, kaunar da yake yima uzair gaba daya ta koma akan yaron da bai ta6a ganinsa ba......' acikin labarin da muhsin ya fada masa abu ɗayane bai sanar da shi ba, rasuwar iyayensa gudun kada zuciyarsa ta buga, kwara idan ya samu nutsuwa ya sanar dashi daga bisani.

A daren ranar kafin muhsin yabar dakin taj, Sai da taj ya gargaɗesa akan kada ya sanar ma wani cewa yagansa saboda rayuwarsa tana acikin hatsari, idan mutanan da suka kashe uzair suka san da zaman shi tabbas zasu cigaba da bibiyarsa har sai sunga bayan shi.

Cikin sanyin murya muhsin yace in sha Allah babu wanda zaiji zancen dawowarshi, zai rufa masa asiri yaci gaba da zama a gidansa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mashi mafita....

Tsawon wata guda suna agidan muhsin, a cikin kwanakin da yayi baya iya runtsawa saboda damuwar rashin angel, duk daren Allah Sai yayi nafilfili saboda angel dinsa, duk ya fita hayyacinsa sam baya da koshin lafiya ciwon kafarsa tamkar ana fama masa shi abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa, muhsin yaso ya bi shi suje asibiti a duba lafiyarshi gudun kada ya rasa ranshi amma yaki yarda saboda bayason wani yaga fuskarshi, ya ƙwammace idan ma mutuwarce ta dauke shi agidan muhsin zaifi mashi sauƙi akan wadannan azzaluman mutanan su kona shi.

A daren wata rana ne, Yana cikin Yin nafilfilin dare, Yajiyo dirar motoci a cikin gidan muhsin, A firgice Ya mike daga kan darduma Gabansa na faduwa, baisan su wanene sukazo gidan muhsin ba, a irin wannan lokacin karfe kusan sha biyu na dare, zuciyarsa na bugawa ya nufi falon gidan don ganin su wanene,

Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, ganin matasan samari masu jini ajika suna shigowa kowannansu sanye cikin shiga ta bakake kaya sun rufe fuskokinsu da facemask.

Bakomai ne ya tsoratar da shi ba face tunawa da wadannan body guards din da suka budewa alhazawannan motocinsu, nan take ranshi ya bashi cewar sune, hakan na nufin muhsin Yaci amanarshi, bayan yayi mashi alkawarin zai rufa masa asiri shine yabi ta bayan fage ya tona masa asiri, zuciyarshi ajagule ya furta meyasa zaiyi min haka! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankalin shi danejo kada suce zasu haɗa da ita su kashe...

A lokacin zuciyarshi ta riga ta gama hasala, Jininsa akan akaifarsa yake, tunkararsu yayi muryarshi a fadace yace"kun biyo ni nan dinma donku kashe ni? Laifin me nayi maku ne? Da ɗaci aransa ya furta maganar, kamar daga sama yaji muryar muhsin daga bayan shi yana fadin"taj, ka tsaya zanyi maka bayani" a sukwane ya juya ya kalle shi a fusace yace"wani irin bayani zakayi min muhsin? haka mukayi dakai? ka cuce ni muhsin, ba zan ta6a yafe maka ba, yanzu dakai za'a hada baki don akashe ni"? Hawaye cike tab da idanunsa yayi maganar, fitowa danejo da matar mushin sukayi daga dakin duk suka tsaya suna kallon su....

Matasan da suka tsaya abakin kofar falon sun harɗe hannayensu akan kirjinshi suna kallon shi, babu alamun zasuyi magana..

"Taj bazan ta6a cin amanarka ba, abun da ya faru da kai ba kai ka ɗai ya shafa ba, hada ni kaina saboda ina jinka tamkar ɗan uwana na, waɗannan matasan da kake gani, ba su zo da niyar su cutar dakai ba, sai don su taimaki rayuwarka, Idan ka basu hadin kai in sha Allah zakuyi nasarar nemo Angel dinka data 6ata, bayan haka zasu tayaka daukar fansa akan mutanan da suka kashe uzair"
Chapter 40 · 0% Book details