← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 238

Sashe 189

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

dakatawa yayi da yin maganar wani irin kululun bakin ciki da takaici ne ya tokare makoshin shi"a matsayin mu na mashahuran da duniya tasan da zamammu, abun kunyane asan me muke aikatawa, Ina jin tsoron mu rasa kimarmu da darajarmu fiye da yadda nake jin tsoron mutuwata, mutuncinmu zai zube a idon duniya, girmamamu da mutane suke yi suna ganin martabarmu zai tashi abanza, daga nan basai nayi maku bayanin abun zai faruwa ba, kun riga da kunsan sakamakon bazai ta6a yin kyau ba..." ya fada yana binsu da kallo daya bayan daya.

bakowane daga cikin su ya karaya ba, shi dama Elder mutunne mai wata aƙida tun fil azal baya son duk wani abu da zaisa mutuncin shi ya zube yana girmama ƙimarsa.

muzkutawa Jan le6e yayi kafin da wata irin muryar mai tattare da zafin fusata Yace"garkuwar kurkuku Ya zama garkuwar Fursinoni, ƙaddarar kurkuku ta zama mummunar ƙaddara agare mu, babban kuskuren da muka tabka shine barin tsohuwa Tamira da ranta, a lokacin da muka kashe Habibulllah, da mun sani mun haɗasu duka mun kashe su, shima garkuwarmu da ace bamu kawo ƙaddara gidan kurkukun mu ba, nayi imanin bazai ta6a cin amanar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa"ita kuma Khala Elder Kayi hakuri da abunda zan faɗa, tunkafin zuwan wannan lokacin saida muka baka shawarar ka kasheta saboda ita din tana da kyakkyawar zuciya kuma tana ƙyamatar abunda muke aikatawa amma saboda kaunar da kake mata, shi yaja har ka gaza Yanke mata hukuncin daya dace"

Cike da danasani Elder ya sunkuyar da kan shi ƙasa, tunda suka fara magana, Jan wuya Yana a kishingide Yana binsu da kallo babu alamun kaɗuwa atare da shi, shi kuwa Jan kunne kamar yafi su shiga damuwa dama duk cikinsu shine mai raunin zuciya.

Jan Ido Yace"kada ku bani Kunya, duk wani abu daya faru ya riga daya faru, Mu fa Elders ne, babu wani mahalukin daya isa yaga bayan mu, abun nawa muka aikata bamu ta6a karaya ba sai wannan lokaci don kawai wasu kananun kwari sun kai mana farmaki? Rai nawa muka salwantar? Ya fada cike da gadara.

"sai wadannan zasu gagaremu! In har muna so mu dawo da karfin ikonmu dole mu bi abun da allon tsafinmu ya nuna mana, dole mu aiwatar saboda itace dama takarshe da ta rage mana wadda zamuyi amfani da ita gurin dawo da ran kurkukun ƙaddara"

Ya faɗa tare da dan dakatawa yana dubansu"a wannan karon dole mu cire sonkai atsakaninmu, bi'amana mu kashe duk wanda Yasan sirrinmu koda mafi soyuwa ne agaremu..."

sarai Elder Ya fahimci da shi yake magana.

"ita kuma dama ɗayan nan data rage mana itace mu cire Zuciyar Yarinyar nan, Mu ba dodon tsafin mu Ya handame ta, sannan mu kashe ƙaddarar kurkuku, ta hakane kaɗai gidan kurkukun ƙaddara zai farfaɗo...."

wata irin mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, ganin har yanzu suna da saura damar da zasu cigaba da aiwatar da shaidancin su.

Cike da izza Jan wuya yace"abun farin ciki, Garkuwar da suke taƙama da shi, Ya rasa ranshi saboda shi wawane shashasha, Ya sadaukar da kanshi saboda ya basu kariya, duk da muma munyi babban rashi amma wannan duk ba wata matsala bace da zamu daga hankalinmu akai, Ni ta inda najiye mana dadi gaba dayansu wadanda suka san sirrinmu basu san fuskokin mu ba, tayaya suke tunanin zasu iya yin nasara akanmu? In banda ma sudin dakikai ne iya fa sunayen mu suka sani, sai kuma sirrinmu amma azahirin rayu basu san su wanene Elders Ba...."

Maganar Jan Wuya ta faranta masu rai, ganin sun samu mafita...

"Yanzu wanene Zai kawo mana Yaran?" Jan harshe ne yayi tambayar, Cike da isa Jan wuya yace"kubar komai a hannuna"

tuntsirewa suka kuma yi dariya hahaha
_________________________________✍️

Shin Ya Labarin Tsohuwa Khala❓

*Bayan wani lokaci*

Farfaɗowa tayi daga dogon suman da ta yi na tsawon awanni, A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhu ne ya mamaye ganin ta, tana ƙoƙarin motsa jikinta taji kamar an daddaureta.

gumin zufa ne Ya wanke fuskarta, bata gama wartsakewa ba sai nishi take yi tana jan numfashi..

takun tafiyar mutun taji a cikin kunnanta yana tunkaro ta, cikin disasshiyar murya ta furta"wanene"?

Kakkausar murya Elder ce ta razanar da ita yayin daya furta"me nayi maki dana cancani cin amana daga gare ki"

Shiru tayi bata furta kalma ba, Hankalinta dai idan yai dubu toh ya tashi, zuciyarta sai dakan uku uku take tasan yau sai buzunta, mai kwatarta a hannun Elder sai Allah.

A hankali Hasken fitilun dake saman ceilling din ɗakin ya haskaka ko'ina tana a zaune kan Kujerar ƙarfe, a rude take kallon igiyar kacar da suka ɗaɗɗaure jikinta da ita, ko yatsanta bazata Iya ɗaga wa ba, Da sauri takai dubanta gare shi yana a tsaye Ya juya mata baya, tun da taganta adakin da suke hukunta wanda yaci amanarsu na gidan kurkukun kaddara Ta tsinci kanta da jin matsanancin faduwar gaba, ga wasu karfafan Evil giants data hango tsaye abakin kofar dakin..

"Tun da naga irin makaman da sukai amfani da su gurin kashe giants nasan cewa koma wanene ya basu makamin acikin mu yake, saboda mu kadai keda irinsu acikin gidan kurkukun nan ake ƙera su, bakowa yazo min araina ba face ke dama kin jima kina gaya min zaki dauki fansa akaina"

Cike da karfin Hali tace"banyi mamakin abun da kayi min ba Elder, Ni angaya maka bani da zuciya a kirjina ne? Taya kake tunanin bazan ci amanarka ba? Dama akwai amana tsakaninmu? Kaida ka rabani da kowa nawa, har kana da bakin furta naci amanarka? Akwai maci amanar daya wuce kai mugu, Hakanan kawai saboda nasan sirrinka bisa kuskure ka rabani da dangina, ya'yana, Jikokina, ka kafe ni da asirinka cikin kurkukun nan."

idanunta jawur ta faɗa yayin da hawaye ke shararowa kan kuncin ta..ta daura da cewa

"tun lokacin dana nasan sirrinku, a ranar na daukar wa kaina alwashin saina yi silar Tonuwar asirinka, kowa yasan wanene kai, da miyagun ayyukan da kake aikatawa, shiyasa na dinga satar makamanku ina boye su saboda tanadin zuwan wannan ranar"

bata ƙare maganar ba, Taji Ya sheƙe da dariya, cike da izza Ya juyo ya fuskance ta, batare daya furta kalma ba, gently yake jujjuya sandar hannun shi.

"Dariyarka ta bazance Elder, Ni nasan Ayanzu haka Ƴan hanjin cikinka kaɗawa sukeyi saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya, Na kunsa maka bakin cikin da har abada ba zaka manta ba, naja maku babbar asara, koba komai Yau kaga wadanda suka fi karfinka"

ta fada da murmushi akan fuskarta.

Wata Yar iskar dariya Ya saki, Kafin Ya furta"dame kike takama ne? Da ido Ta nuna mashi sama tace"Allah, shine abun tinƙahona, koken dana daɗe ina kai mashi akanka Yau ya amsa addu'ata, daga Yanzu ka kasance cikin shiri akowani yanayi mutuwa zata Iya riskarka, zaka wukalanta ka zama kaskantacce, kimarka da darajarka zasu zube a idon duniya....."

bata ƙare maganar ba Elder Ya buga sandar hannunsa ta daki ƙasa har saida ƙura ta tashi, wani irin radadi taji acikin kanta hakan yasa ta dakata da yin maganar.

Yana Huci Yace"kina tunanin kinyi nasara akaina ne? Bayan Duk wani shirinki Ya tashi Abanza, wadanda kike takamar zasu ga bayan mu a yanzu haka babu ko daya acikin su, duk sun mutu a hannun giants din mu, suma fursinonin da kika ku6utar basu tsira ba zamu kashe su ne"

Wani irin faduwar gaba taji arazane Ta furta"kana nufin Danish da Owais sun mutu su ma" jinjina mata kai yayi" gaba daya sun mutu...Don haka kidaina farin ciki, saboda haryanzu baki kamo hanyar da zaki ga bayana ba, kashe Elder ba abune mai sauki ba, Ita kanta mutuwar tsorona take ji..." a gadarance yai maganar.

ta kiɗima da jin maganar shi, idanunta cike tab da kwalla ta furta"saboda shafewar basira da jahilci kamanta kafin kai anyi wasu azzaluman da suka gabata yanzu duk suna ina ? Ta jefa mashi tambayar bai furta kalma ba.

"mutuwa bata tsoronka Elder Lokacin ka ne baiyi ba, Allah yana sane da duk wani abu da kake aikatawa dama ce ta dan wani lokaci kuma kajira ka gani wlh karshenka bazai kyau ba" ta faɗa tana sharar kwalla

"kuma karya kake min, Danish dina bai mutu ba, owais dina ma bai mutu ba ina ji araina suna araye..."

Fashewa yayi da dariya"ki yarda ko karki yarda matsalarki, Kina kurarin kin tona asirina, bayan Har yanzu asirina arufe yake saboda babu wanda yasan ainihin Elder, ko fuskata basu sani ba, taya zasu iya tona min asirina? Bayan Ko tuhumata basu isa suyi ba saboda basu da wata shaida...." ya fada yana sakin dariyar shakiyanki.

ranta a 6ace ta furta"ni zan tona maka asiri..." ta faɗa tana huci.

Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"kin ta6a ganin gawa tayi magana"?

Cike da tashin hankali ta zare ido tana kallon shi, matso da fuskarshi yayi saitin tata"Oh wai kina tunanin zan barki araye? Bayan kece kika san su wanene Elders, Ko da can da kika san sirrina nabarki araye nayi danasani da ban kasheki ba, da nasan zaki zamarmin masifa da tuni najima da fille kanki...."

gaba daya tabi ta rude da jin maganar shi muryarta nawa ta furta"kada ka kasheni, Kabarni da raina, Ina son naga ya'yana da jikokina, Ina so na koma gurin dangina, ko dan son da kake min da zaman amanar damukayi da juna ka kyaleni da raina.."

Girgiza kanshi yayi"ke da ganin su, Sai a lahira, nasoki tamkar raina amma tunda kika nunamun tsantsar kiyayyar da kike min naji nima kin fita araina, Inasonki amma nafi son mutuwarki ayanzu idan nabarki zaki zamarmun annoba"

Ya faɗa tare da dafe saitin zuciyarshi, batay mamakin ganin hawaye da suka cika idanun shi ba..
Chapter 189 · 0% Book details