Sashe 12
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan shigarsu ɗakin, kamar yarda suka barshi da asuba haka su ka taras da shi, babu abun da ya canza yana a kwance rabin jikin shi lullu6e da bargo, sumar kanshi an ɗaure mashi ita, ta kara tsayi har kusan mid back din sa, ga wani irin pure white da skin dinsa tayi har wani glowing ta ke yi, jikin ummi ba ƙaramin sanyi yayi ba, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa dakin danish, bata ta6a tsammanin jikin yayi tsauri har haka ba, kamar matacce babu abun da ke motsi a jikin sa.
Tsananin tasauyin shi ne ya kama ta aranta ta ayyana wato duk kyan mutun bai isa ya hana kanshi ciwo ko mutuwa ba, jiki asanyaye ta matsa bakin gadon, sheikh imam da taj suna daga tsaye suna kallon shi, yanayin fuskokinsu ya nuna damuwa.
Girgiza kai sheikh yayi cikin jimami ya furta"Ya Allah ga bawan ka nan, kafi mu sanin a wani hali yake a ciki, ya Allah ka sauƙaƙa mashi abun da ke damun shi, Ya Allah ka raba shi da shaidanun dake azabtar da rayuwar sa... cikin harshen larabci yaci gaba da karanto addu'o'i yana tottofa mashi, rashin lafiyar danish ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yai ba, damuwarshi kada yaƙi tashi, duk da yayi imanin addu'o'in da yayi mashi, da sallar daren da yake yi mashi basu tafi hakanan ba, sai dai idan lokacin shi ne yayi.
Cikin rauni na murya ummi ta furta"baya iya tashi"?
Taj da jikin shi ya gama mutuwa laƙwas, Muryarshi babu karsashi ya bata amsa da cewa "baya iya yin komai, sai dai ayi mashi, ta hanya daya muke gane ya farka daga bacci, yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suke kerma"
Jinjina kai ummi tayi, tare da kau da idanunta daga kallon Taj ta dubi sheikh imam adai dai lokacin shima ya dawo da dubanshi gare ta, haɗa ido su ka yi da juna duk saita rasa sukuninta kamar wata mara gaskiya.
"Addu'arki yake buƙata a matsayinki na mahaifiyarsa" har sai da taji gabanta ya faɗi jin sheikh imam ya furta a matsayinta na mahaifiyarsa.
Ɗauke idanunta tayi daga kanshi, kafin ta dai daita nutsuwarta, ta ɗan ɗukar da kanta saitin inda Danish yake a kwance, cikin harshen larabci ta soma karanto addu'oi tana tottofa mashi, bayan ta gama ne ta ɗago tare da kallon fuskar sheikh imam, tayi mamakin murmushin da ta gani ɗauke akan fuskarshi, sunnar da kanta tayi ƙasa saboda kwarjinin da yayi mata
"Chief yana nan ko ya fita ne"? ya tambaya yana kallon Taj.
"Bayanan tun ɗazu da rana ya fita, yana a villa wurin daddynsa, Idan kana buƙatar yin magana zan iya kira maka shi"
Girgiza kai sheikh imam yayi"a'a, dama na tambaya ne in ji ko yana nan"
"yanzu me yakamata mu yi sheikh"?
"Naga har yanzu bai farka daga bacci ba, nasan dole akwai yunwa atattare da shi sannan yana buƙatar wanka, amma kada a tada shi idan har bashi ya farka da kan shi ba" amsa mashi taj yai da toh.
"Ina sauran yaran su ke ne? Sun yi mashi addu'o'in da suka sa6a yi"? ya tambaya yana kallon Man.
"tun da asuba rabon su da dakin, bansani ba ko sun ƙara leƙowa"
"Inason ganin su gaba ɗayan su yanzu"
da sauri ummi ta ce"bari naje na kira su" dama neman hanyar da zata bar dakin take yi.
Bayan fitarta daga ɗakin sheikh Imam ya ɗan haura saman gadon, tafin hannunsa ya ɗaura saman forehead din danish, ya fara jera addu'o'i na musamman yana tofe mashi jiki, tsawon lokacin kafin yacire tafin hannun ya maidashi kan saitin zuciyarshi, yaci gaba da yi mashi kira'ar alkur'ani mai girma, Taj dake kallon sheikh imam dake janyo kira'a ba karamin nutsuwa yaji ba a cikin zuciyarsa.
Tun da ummi ta fito, a bakin kofar ɗakin ta la6e tana sauraron kira'ar sheikh imam mai ratsa zuciya, wasu irin zafafan hawayene suka cika mata idanunta, Jikinta har kerma yake yi, ga dukkan alamu akwai wani abu da yai silar jefa ta yanayin da take a ciki.
Runtse idanunta tayi sosai, jin kukan na shirin kubce matane yasa tai saurin toshe bakinta da tafin hannunta, muryar ta na rawa ta furta
"uhibuk kathiran ya 'abi har yanzu kai mahaifina ne ba abun da ya canza..."
Duk waɗannan sambatun da take yi, A kunnan Unaisah, wadda fitowarta kenan daga dakin su ta kamo hanyar zuwa dakin Danish don ta duba jikin shi, karaf taci karo da ummi ta runtse idanunta tana matsar kwalla.
Muryarta da ruɗani ta furta"Aunty Ummi!"
Furgigit ummi tay saurin buɗe idanunta wadanda suke ajike sharkaf sun kaɗa jawur
Ganin unaisah yasa tai saurin sanya tafukan hannayenta ta share hawayen dake karanyo mata
"Aunty Ummi, yaushe kika shigo? Ina boss? Meyasa ki zubar da hawayen ki? Wani abu ya faru da danish dina ne..." hankalin ta atashe ta fada
Muryar ummi adisashe ta furta"bamu jima da shigowa ba, ni da boss tare da sheikh imam... " ta fada muryarta na ɗan rawa
"kada ki damu ba wani abu bane ya faru da ɗan uwanku, kawai naji tausayin shine ya kama ni, bansan ciwon nashi yakai har haka ba, naji haushin kaina da ban ta6a leƙowa domin duba lafiyar shi ba, yau da naganshi jikina yayi sanyi shiyasa kika ganni awaje ina sharar hawaye... ' wannan maganar da ummi ta furta tayi matuƙar karya ma Unaisah zuciya, idanunta tuni sun cicciko tab da kwalla, ganin hakan yasa ummi tayi saurin furta"dan Allah kada ki yi kuka, addu'armu yake buƙata A halin Yanzu"
duƙar dakai ƙasa unaisah tayi, jiki asanyaye tace"bari na shiga in duba shi"
ta faɗa tare da buɗe kofar tasa kai ta shige ciki, bayan shigarta Ummi ta sauko down stairs don ta kira su Haris kamar yadda sheikh Ya buƙata.
Kafin wani lokaci gaba ɗayansu sun hallara a dakin danish, kowannansu ka kalla babu walwala, tsantsar damuwace akan fuskokin su.
Ɗaya bayan ɗaya sheikh imam yake dubansu har sun yi shirin kwanciya bacci, kowannansu yana asanya da sleeping dress dinsa, kafin ya soma magana cikin sanyayyar muryarshi
"Ku naso ɗan uwanku Ya samu lafiya"! har suna haɗa baki wurin furta eh
"To ku dage da yi mashi addu'a, Ita yake buƙata daga gare ku, nasan kunayi to ku ƙara abisa wadda ku ke yi mashi, Kunga har yanzu mun rasa gane yanayin da yake aciki, yau jikin shi yayi tsauri fiye da kullum, tun safe babu alamun zai farka daga wannan dogon baccin da yake yi, shi kadai yasan me yake ji a jikin shi, addu'a da kuke gani takobin mumine ce da itane zamu yaƙi shaidanun dake sarrafa shi, kullum suna aiki akanshi, safe da dare, why mu bazamu iya tsayawa tsayin daka wurin ganin mun ruguza shirin su ba! Mu da ma mu kayi imani da Allah balle su da su ke mushirikai.... ' tun da sheikh imam ya fara yi masu magana suka nutsu suna sauraron shi, sun kewaye gadon da danish yake a kwance, kokari yakeyi ya tunzurasu donsu harzuƙa su kuma dage damtse wurin yi mashi addu'a, duk maganganun da sheikh imam keyi a kunan ummi da ke a la6e bakin ƙofar dakin tana sauraronsu.
Sautin shessheƙar kukan unaisah ne ya soma karaɗe dakin, kamar jira sukeyi tafara kuka, Jemimah da azeeza suka fashe da kuka, suma sauran kowannansu kwalla ce a idanunsa.
"Ba kuka yakamata kuyi mashi ba, kamar yarda na fada maku addu'arku yake buƙata, A cikin ku akwai wanda ke tashi yin sallar dare domin yi mashi addu'a akan Allah ya bashi lafiya"?
Shiru su ka yi, saboda basu da amsar da zasu bashi, unaisah dake faman zubda kwalla muryarta a raunace ta furta"ina yi mashi, amma ba kullum ba, wani lokacin kona kwanta da niyar tashi inyi mashi bana farkawa, saboda bani da me tada ni"
"Ni bansan yadda akeyi ba, da ace na sani har bacci zan iya hana kaina don inyi mashi addu'a, saboda danish yayi mana abin da bazamu ta6a mantawa ba, ya cancanci mu sadaukar da komai akanshi" cikin sanyin murya batool ta ƙare maganar, taj da sheikh iman sun nutsu suna sauraronsu haɗi da kallon la66an duk wanda yayi magana a cikin su.
Cikin shessheƙar kuka jemimah tace"wallahi nima zanyi ma shi, saboda bana so Danish ɗin mu ya mutu kamar yadda na rasa Majnoon ɗina...." wannan maganar ta jemimah taja hankalin sheikh imam da taj sosai akanta, ta dage sai ku ka ta ke yi, kumatunta har sun yi ja, ruko hannunta sheikh imam yai tare da lallashin ta akan ta daina ku ka.
Hanna dake matsar kwalla ta ce"In sha Allah babu abun da zai same shi, zamu yi iyakar bakin kokarin mu don ganin mun ceto rayuwar ɗan uwan mu da iznin Allah..." daƙyar ta ƙare maganar
"In sha Allah daga daren yau zan fara yin mashi nafilfili, ni saima naji haushin kaina, bamu kyauta ba, har zamu iya dariya muyi bacci, bayan ɗan uwanmu yana akwance rai hannun Allah, komai sai anyi mashi, mutumin daya sadaukar da farin cikin shi akanmu? Ya hana idonshi bacci saboda ya bamu kariya, sai mune zamu gaza hana idanun mu bacci anya kuwa mun kyautawa kanmu"? gaba ɗaya suka fashe da kuka mai tsuma zuciya, haƙika maganar Haris Ta ta6a zukatansu, hatta ummi dake jingine da kofar dakin sai da ta zubda kwalla duk da batasan takan tarihin rayuwarsu ba, amma ta hasko wani abu.
daga gefen gadon Danish sheikh Imam ya zauna jikinsa yayi sanyi lakwas, bai ta6a ƙaguwa da son jin labarin rayuwarsu ba irin yau.
Cikin sanyin murya taj yace"kada ku ɗaurama kanku alhakin laifin da bana ku ba, hana ido bacci ba shi ke nuni da kun damu dashi ba, saboda ku kanku bazaku samu kwarin gwiwar yi mashi addu'a ba muddin baku da kwanciyar hankali da nutsuwa, abun da yakamata, tun da dare yayi in za ku yi bacci ku kwanta da wuri, wuraren ƙarfe uku na dare zan kira unaisah awaya in tunasar da ita, in yaso ita sai ta tashe ku daga bacci ku tashi kuyi nafilfili ku kai kukan ku wurin Allah akan halin da ɗan uwa ku yake a ciki, in sha Allah zamuyi nasara"
Shawarar da boss man ya yanke masu tayi masu dadi.