← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 238

Sashe 7

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malam Ina ka shiga ne? Ka tafin mun da rabin raina"

On the other hand sautin dariyar Big guy ta karaɗe Kunnuwansa,

"Nifa Yanzu Haka Ina daki kwance saman gadona"

"Bana son Iya shege, To ita ina kabarta?

"Ka riga da kasan Halin Jarin naka, yarinyarce da kiriniya, Tunfa dazu dana nuna mata kitchen din nace mata ta dawo cikin yan uwanta, bayan na fada mata hakan na wuce room dina, yanzu haka bata wuce kitchen din, Cikin kattai" ya karasa maganar Yana dariya.

Daure fuska boss yayi tamkar Yana agabanshi,

"Zamu hadu dakai ne, Allah idan wani abu Yasamu Yarinyar nan jikinka ne zai gaya maka dan rainin wayau" ya fada tare da yin rejecting kiran,

Cikin takun sauri Ya nufi hanyar zuwa kitchen din, ba laifi akwai tazara tsakanin kitchen din da main falo,

Lokacin da Ya Isa katafaren kitchen din gidan tamkar a restaurant tsabar haɗuwarshi, kai kace ba wurin Girka abinci bane saboda girman shi da ƙawatuwarshi, An zuba kayan aiki masu tsada da inganci, gaba ɗaya masu girka abincin Gidan Jami'an Isod ne cikin chef'uniform, matasan samari masu jini a jika, daga ganin Yadda suke aiki zaka shaida kwarewarsu a 6angaren catering, ko mace bazata nuna masu Iya sarrafa abinci ba, A ƙalla sunkai su Bakwai, Babu wanda Ya lura da shigowar Taj acikinsu, Gaba ɗaya Hankalinsu na akan Unaisah, dake agaban kitchen island tana Yanka masu kayan Lambu, abun da ya ɗaure ma taj kai, ganin Yadda sukayi mata rumfa kamar zasu haɗiyeta tsabar yadda suke binta da mayataccen Kallo, Ta saki baki sai Labari take basu su kuwa sun Kasa kunne suna sauraron daddaɗar muryarta, Tunda suka kafe ta da idanunsu ko kyaftawa basa yi kamar zasu haɗiyeta.

Gyaran Muryar da Taj yayi masu ne Yaja Hankulansu ga dubanshi, kamar sunga wani mugun abu, A gaggauce su kayi saurin barin Inda Take, kusan atare suka buga ƙafa Haɗi da sara mashi.

Kallon Harara Ya watsa masu, Cikin harshen turanci Ya furta"wannan wani irin gangancine zaku bar Yarinya tana amfani da wuƙa? Kun wani tsareta da idanunku kamar zaku lashe ta" Sunnar dakai su kayi Suna faman sosa keya suka hada baki wurin furta"sorry Sir, ba laifin mu bane, Itace ta buƙaci damu koya mata girki, munyi kokarin Hanata amma saita sanya mana rigima"

Wurga eye balls dinsa Yayi akan Unaisah dake Kallon shi, Har ta ajiye wuƙar hannunta, nufo shi tayi fuskarta da murmushin Yaƙe tace"ay ni nace su bani In tayasu aiki, Kuma dama Na iya ba yar koya bace" ta fada tana ruƙe qugunta da hannu.

Wani kallo Ya jefa mata me kama da harara, bakomai Yake tunawa ba face lokacin da tana yar ƙaramarta, ranar daya tafi aiki yabarta a gida tana jin yunwa taje ta kunna cooker gass da sunan zata yi girki, wuta ta kama a gidan, wai yau itace take mashi kurin ta Iya girki ba yar koyo bace? Girgiza kai Yayi haɗi da yin murmushi tacikin face mask dinshi

"Daughter, ƴan uwanki sunata nemanki, Yakamata Kizo Mu koma falo" maƙe mashi kafaɗa tayi"ay bamu gama girkin ba"

"Bana son gaddama, zo ki wuce mu tafi"

Marairaice mashi fuska tai"dan Allah kabarni wallahi inason In Iya girki kala kala,"

"Kada Ki damu, zansa a koya maki amma ba yanzu ba, dokar Aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, baki ga maza bane a kitchen din"? Cikin lallashi yayi mata maganar Yana nuna mata chefs din dake tsaitsaye cirko cirko suna kallon su

"Yalla6ai, da dai anbarta ta koya tun da ta nuna tana so, kuma ni aganina maca ce ita, wata rana zataso tayi ma mijinta.... "Tunkafin chef din daya dauko Maganar Ya karasa boss Yayi mashi wani kallo mai nuni da kashedi, Hakan yasa shi yin saurin Katse maganar,

Janyo hannun Unaisah Yayi dakarfi Ya fito da ita daga kitchen din, Chefs din basu ji dadin zuwan Shi ba, Ya raba su da Yarinyar data ɗe6e masu kewa yau, zuwanta Ya faranta masu rai, sunji dadin surutun da tadinga yi masu, komai nata burgesu Yake yi.

Ranta Ya 6aci, Ganin yadda ya janyota daga kitchen din, da sauri ta fusge hannunta tana fadin"Ni ka ƙyale ni, in tafi da kaina" Ta faɗa tana daure mashi fuska, Sam Yakasa ce mata komai sai dai kallonta da yake yi.

"Bansan meyasa ka takura rayuwata ba, girki fa kawai na roƙa kabarni In tayasu amma ka hanani, dan Allah menene alaƙata dakai ne? Na lura so kake kana Yin iko dani, Idan don saboda taimakon da kukayi mana ne ay dan Allah ku ka yi ko"? A fadace ta faɗa tana zare mashi gray eyes dinta tamkar zata rufe shi da bugu,

Har saida Yaji gabanshi Yaɗan fadi, sauƙinta ma yasan halinta,

"Meyasa ni kadai kake ma haka?

"Saboda ke jini na ce" a zuciyarshi Ya furta maganar

"Kiyi haƙuri Idan na 6ata maki rai, bana son 6acin ranki, Ƴan uwanki ne suke ta nemanki, bayan haka kamar yarda na fada maki dokar aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, waɗannan chefs din da kike gani dukansu a lokacin baya ba mutanan kirki bane, Dayawansu Ƴan shaye shaye ne da masu bin matan banza, wasun su mugayen ƴan ta'adda ne wadanda suka gagari Iyayensu da hukuma, Ire iren su chief Yake kamowa Ya koya masu hankali, Idan suka shiryu sai ya maida su Jami'an Isod..."

Waro ido waje tayi jin Ya ambaci mugayen ƴan ta'adda.

"Ba Zanso abun da zai cutar min dake ba, Haƙƙina ne kula da rayuwarki Unaisah dan Allah kada ki hanani Yin aikin lada... " in cool voice ya faɗa...

Wani irin kallo yaga tana bin shi da shi, kamar akwai wani abu da take son ganowa

Muryarta na rawa ta furta"dan Allah ka cire min face mask din fuskarka inason ganinka"

Girgiza mata kai yayi"zaki ganni amma ba yanzu ba, amma meyasa kike son ganin fuskata"?

"Saboda muryarka, tayi min kama da ta daddyna wallah sai nake ji kamar daddyna ne kai, duk da nasan ma ba shi bane, ina ji araina baya araye ma" idanunta har sun ciko da kwalla.

"Kina ji aranki ni daddyn ki ne" ɗaga mashi kai tayi alamar eh"

"Ki ƙaddara aranki cewa Ni ne" ya faɗa tare da ruƙo arm dinta, Ya janyota jikin shi, haɗi da kwantar mata da kanta saman kirjinsa, wani irin sanyine taji ya ratsa zuciyarta, lumshe idanunsa yai a hankali ya sanya hannu tare da zame face mask dinsa, Sumbatar head dinta yai, kafin da sauri ya maida mask din fuskarsa.

Tsawon mintuna biyar cuf suna manne da juna, sai daga bisani ya raba ta da jikin shi, baiwar Allah jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwan sanyi,

Shafa gefen fuskarta yayi da tafin hannunsa"Ina sonki my daughter" murmushi tayi mashi"Nima ina sonka daddy na"

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*

*(Kaɗan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya, unaisah zatayi waya da Benazir😍 Garkuwa zaiyi tashin bazata, kada ku bari abaku labarin walimar hateem😂🤣 Ni kaina zumuɗin ta nake yi🔥🔥🔥)*

*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 9 Complete
by
Novels Elite Admin
May 24, 2024
Sponsored Link

_ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_

سجن القدر💋✊🔥

~Takun Ƙarshe🔥~

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

Har Ya ruƙo hannunta za su shiga ciki sai kuma Ya dakata yana faɗin "Au namanta, Auntyn ku ummi tana buƙatar abinci ban sani ba, ko akwai abunda chefs suka gama girkawa yanzu"? ya tambaya yana duban ta.

"Akwai naga sun kammala Rice and chicken stew tare da coleslaw hada zobo ma ... " kafin ta ƙarasa lissafa mashi yace"Okey, Ki jira ni, bari na shiga ciki in kar6o mata" amsa mashi tayi da toh.

Bayan shigarsa kitchen din ta soma tunanin ko awani hali Garkuwarsu ya ke a ciki? ta yi matuƙar damuwa da shi, ganin shi da take yi a mawuyacin hali ba karamin karya mata zuciya ya ke yi ba, rabon da ta sanyashi a idanunta tun da asuba da su ka shiga yi mashi addu'a, da tunanin shi ta wuni ta bari sai da anjima ta shiga duba shi.

"My babe, I'm back" Muryar Boss man ce ta fargar da ita, da sauri takai dubanta gare shi, Hannayen shi ruƙe da handle din wooden tray mai faɗi, daga saman shi haɗaɗdun warmers ne babba da ƙarama tare da plates da sauran tarkacen kayan abinci"

Miƙa mata yayi kar6i nan, ta sanya hannu ta kar6a cikin kitchen din Ya koma jim kaɗan Ya dawo hannayen shi ruƙe da wani madaidaicin faranti mai ɗauke da mixed drinks masu sanyi.

Ganin tana kallon shi yasa shi kashe mata ido ɗaya, murmushi tasakar mashi, a tare suka jera zuwa cikin falon.

Jikin Batool Har Kerma Yake Yi wurin mikewa da wani irin sauri ta nufi Unaisah zata rungumeta, ganin Tray a hannunta yasa ta dakata tana faman ɗaure mata fuska tace"Ina kika shiga inata nemanki"

"Ina a kitchen fa, Girki Na tsaya taya masu aiki" ta faɗa tare da wucewa ta sauke tray din hannunta saman Carpet, Parveen tun da tayi tozali da Abinci takasa samun sukuni, Tafi kowa zalama.

A Plate Batool ta zuba ma Ummi abincin ta hada mata da pineapple juice ta miƙa mata, fuskarta da fara'a ta kar6a tana fadin nagode My babe," a tsanake ta soma Ci.

Ɗaya bayan ɗaya unaisah ta soma kasa masu abincin tana miƙa masu a plate, bayan ta gama da su itama ta zuba nata tare da Boss man a plate ɗaya, suka zauna suna ci gwanin ban sha'awa, falon Yayi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke ci...

"Ummi Ina son Yin magana dake bayan sallar magrib" Boss ne yayi mata maganar, amsa mashi tayi da toh.

"Amma wannan ɗin abincin daren mu ne"? Acewar Parveen, Harararta Naufal Yayi.
Chapter 7 · 0% Book details