Sashe 63
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 7 min read
"duk da bana danasanin ƙaddarar rayuwar da ta riske ni saima farin ciki da nakeyi saboda a kowani rashi da nayi toh akwai nasara acikin sa" tun da tafara magana danejo ta nutsu tana sauraronta, har cikin ranta tana mai mamakin girman yarinyar da kaifin basirarta, komai nata na dabanne shiyasa take da saurin siye zuciyar mutune.
"Aunty danejo, Kinga ikon Allah ko? Bayan na tafi sai gashi Allah Ya hada ki da daddy na har kun yi aure, amma baki takura kanki ba babu danginki a kusa, ki bani labari ya kikaji da kika fara shigowa cikin burni" yar dariya danejo tayi kafin ta fara bata labarin irin yadda ta tsinci kanta farkon shigowarta birni, ta tabka ƙauyanci taj ba karamin hakuri yayi da ita ba, saboda tsoro da rashin sabo da irin rayuwar birni.
Gaba daya suka kama yin dariya kamar wasu zautattu, Yadda kasan wasu aminnan juna.
"Amma dangin ki fa? Shikenan ba zaki sake haduwa da su ba"?
"Ay Yayi min alƙawarin zai kaini rugarmu nan badajimawa ba" murmushi Angel tayi"amma naji dadi watakil nima in bi ki muje, in gano su hasiya da bawuro"
"Baki manta da sunan su ba" jinjina mata kai unaisah tayi"ban manta ba, na haddace su akaina"
"Dama kece bakuwar da zanyi"? ɗaga mata gira tai alamar eh.
"Daddynki Ya faranta min raina, naji dadin ganin abun da banyi zato ba, amma lokacin da kika gudu ina kika je ne , tayaya akai aka gano ki? Ta fada cike da son jin karin bayani.
"Ki manta kawai, nadai ci wahala amma komai Ya wuce, bana son tuna baya" jinjina kai tay alamar ta fahince ta.
"Ina daddyn naki yake"?
"Nabar shi a falo su biyu ne tare da ɗan uwana Danish"
Ruƙo hannunta tayi"muje falon" saukowa sukayi daga kan gadon atare suka fito
A lokacin Taj Yana zaune kan sofa tare da Danish, tun bayan tafiyar Unaisah hankalinsa Yaƙi kwanciya, musamman da yaji ta daɗe bata fito ba, taj Yaso Yaja shi da fira sai dai Yaƙi bashi hadin kai, Jin motsin saukowar su down, yasa shi saurin kai idonsa ga dubansu, lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya ganin Angel dinsa.
Fuskar taj ɗauke da murmushi yake kallon su, danejo kuwa tun da ta daura idonta kan fuskar danish gaban ta Ya fadi rass har sai da ta ɗan dakata da tafiya saboda taji fargaban ganin masifaffan kyan dake gare shi, ganin ta dakata da yin tafiyar ne yasa unaisah yi mata gyaran murya tare da cewa"Shi ne dan uwana danish, kada kiji komai atare da shi muka zo"
jinjina kai tay kafin ta bi ta suka karasa saukowa down asaman sofa dake fuskantar su taj suka zauna, kowan nan su murmushine akan fuskarshi banda danish wanda hankalinsa ke akan unaisah.
"daddyn Angel, inatayamu murna cikin ikon Allah sai gashi Allah ya bayyana mana ita, amma meyasa baka fada min anganta ba"?
"Saboda inaso na baki mamaki" yar dariya tayi"wallahi ka bani mamaki kuma ka faranta min raina, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita daga sharrin makiya da mahassada dama duk wani abun cutarwa" har cikin ranshi yaji dadin kalamanta"ameen ameen, ga dan uwanta nan ku gaisa da shi" tun da tafara magana taki yarda ta kalli danish saboda tsoranshi da take ji, kallo ɗaya da ta masa kafin su sauko down ta gane ba shi kaɗai ba ne.
Muryarta na dan rawa ta furta"eh ta fada min sunan sa danish, ya kake dan uwan angel, Ina fata kana lafiya" muryarsa kasa kasa Ya amsa mata da lafiya, ba tare da ya dube ta ba
"Amma daddy Angel ya kuke da shi"?
Taj yace"yanzu ba lokacin tambaya bane idan na samu time zan maki bayani, tashi muje kitchen mu dauko masu abunda kika shirya masu"
mikewa tayi taj yabi bayanta suka nufi kitchen
A hankali unaisah ta sanya idonta a cikin nashi, Murmushi tasakar mashi har dimple dinta Ya lotsa, sai yai tamkar baisan tana yi ba.
"Ba dai fushi kake da ni ba? Fadamin ko na bata maka rai na"? Ta fada tana ɗage mashi gira wani kallon kasan ido mai kama da harara ya wurga mata
"Na fahimce ka, nasan bai wuci saboda na tafi na barka bane, ni narasa gane kishin da kakeyi akaina, sau biyu kana dukan daddyna, na farko ka jefa masa pillow daga upstair saboda yayi hugging dina, na biyu kuma ka Naushe shi da wannan kafcecen hannun naka saboda ya gyara min mayafina, next time inaga hannayensa zaka karya idan Ya ƙara ta6ani..." ta faɗa tare da ɗaura kafa daya bisa ɗaya tana jifar shi da harara kallon kawai yakeyi bai tanka mata ba.
"Ƙwara tun yanzu ka fara yi masa biyayya kana kyautata masa, saboda daddyna shi yake da ikon mallaka maka ni, Idan ba haka ba wallahi kana ji kana gani zai aura min...."
kasa ƙarasa maganar tayi ganin yana nannaɗe hannun rigarshi, ay tuni tasha jinin jikinta, damtsen hannunsa Ya fito fari sol ga zanan tattoo na tambarin kurkukun kaddara, adan tsorace tace"my man yanzu saika buge ni akan wannan maganar" banza yayi da ita babu alamun zai tanka mata.
Murmushi tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake a jiye kan sofa inda tabar ta, a fakaice ta soma daukar shi video ba tare da sanin shi ba, saboda yayi mata kyau he looks so sexy cikin sleeping dress expecially da ya naɗe hannun rigarsa zanan tattoo dinsa ya bayyana.
A tare Taj da danejo suka shigo falon hannayen su ruke da trays na kayan abinci, kafin su karaso tayi saurin ajiye wayar, ta yi ma danish alamar ya gyara hannun rigar sa, hannu yasa yaja hannun ya rufe damtsen nasa, bayan sun ƙaraso saman lallausan carpet din falon suka sauke masu farantan.
"Bismillah My daugher, inaso ki ba auntynki mamaki, Ki zauna Ki cinye abincin nan ke da dan uwanki Danish" murmushi unaisah tayi kafin ta sauko ta zauna.
"Malam Danish bismillah" ya faɗa Yana nuna masa carpet din, sam baiyi niyar ci ba, amma saboda unaisah Ya sauko Ya zauna, shima taj din da danejo suka zauna suna fuskantar su, tuni kamshin abincin Ya karaɗe hancin su, wani haɗaɗɗen dambun Shinkafa ne ta zuba masu a plate, Yaji kayan kamshi ga nama manyan yanka da ta jera masu asaman dambun, ta tsiyaya ma su juice mai sanyi a cups, tun da suka fara cin abincin, Ta lura da yadda danish yake ci kamar zai fasa ƙaramin bakinsa, da alama dambun yayi masa daɗi, hatta taj da danejo satar kallon sa suke yi su kansu ba suyi tsammanin zai iya cin abincin har haka ba, bayan sun kammala cin dambun ta sake zuba masu farfesun ƴan ciki, kamar masu fama da yunwa haka suka tasa shi gaba suka lamushe, ta kuma ƙara zuba masu gurasa haɗi na musamman taji kuli kuli da kayan lambu da aka yayyanka ga mai dake kyalli asamanta tare da tsiren nama, danish bai ta6a cin gurasa ba sai Yau, kai harta dambun shinkafar yaune karo na farko daya fara cinshi, yaji dadin abincin har ƙwarar cikinsa yayi, Angel dake kallonsa sai faman sakin murmushi takeyi ba tare da ya lura da ita ba, bayan sun kammala cin abincin kowa yayi kulu wash rabu hani'an danejo ta kwashe kayan abincin ta nufi kitchen da su
"Daughter, dare yayi muje na raka ku gida, Kada chief Ya tuhume ni, kinsan yanzu bani da hurumin daukarki tun da a karkashin kulawarshi ku ke har zuwa time da zamu kammala bincike"
"Bakomai daddy, na fahince ka," shafa gefen fuskarta yai, danish dake kallon su tuni ya hade ransa, shi fa har yanzu bai daina kishi da taj ba, saboda baisan alaƙar dake a tsakanin iyaye da dansu ba.
Fitowa danejo tayi daga kitchen, ganin su tsaye yasa tace"ya akai nagan ku a tsaye ku zauna mana muyi firar yaushe rabo"
Taj ya ce"Zasu tafi ne" ɗaure fuska tay"bangane me kake nufi ba, nayi zaton ta dawo gida kenan," girgiza kai yai"ay tana a gidan amma a part din chief suke da zama, zata dinga zuwa kuna gaisawa da juna...." dakyar ya samu ya fahimtar da ita, atare suka raka su unaisah har gida kafin sukayi masu sallama.
Lokacin da suka shiga falon babu kowa har sun koma bedrooms dinsu alamar time din bacci yayi, kamar kar su rabu da danish har saida ta raka shi bedroom dinsa kafin ta dawo ta nufi nasu dakin, tana shiga ta samu deeja kwance kan gadon su sai jan minshari takeyi, murmushi tasaki tana kallon ta, har yanzu kwalliyar dazu ce akan fuskarta duk ta ca6e kamar ƴar mahaukaciya, ta jima tana kallon ta, kafin ta fara cire kayan jikin ta, ta musanya dana bacci, fuskarta dauke da annurin farin ciki, ta hayekan gadon, bata damu da rashin ganin batool ba, tasan bazata wuce dakin aunty ummin su ba, huggin pillow tai, Allah ne kadai yasan dadin da take ji sam ta manta da zancen kiran aunty pretty gaba daya tunaninta akan abun farin cikin daya faru yau ne
______________________________________✍️