← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 238

Sashe 23

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu gudu sauri sauri ta nufi second floor, ko da ta shiga falon babu kowa.

Tana ƙarasawa bakin ƙofar ta sanya hannu biyu ta dafe ta da karfi har sai da ta buɗe kafin ta faɗa a fujajen shigarta keda wuya, idanun ta su kayi mata tozali da abun da Ya figitar da ita, da wani irin faduwar gaba take kallon shimfidar shi.

Wata irin zuface take tsastsafo mashi tun daga cikin sumar kanshi take gangarowa har izuwa saman fatar wuyan shi, kyakkyawar fuskarshi ta jiƙe sharkaf da gumi, hatta jallabiyar jikin shi ta manne ma fatarshi saboda ruwan zufar daya jiƙe ta, muryart na kerma ta soma kokarin ambaton sunan shi.

"Dad...da..nish" bata ƙare maganar ba, ganin yadda yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suka fara kerma tamkar na wanda sanyi ya kama.

Kasa samun nutsuwa tayi, har batasan sa'adda ta haura saman gadon nashi da rarrafe ta ƙarasa saitin inda kanshi ya ke, ta zuba mashi ido tana kallon shi da tsananin firgi ci.

Cikin lokaci ƙanƙani, Ilahirin Jikinsa Ya jiƙe sharkaf da gumin zufa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai.

Tsabar Yadda Jikinsa ke kakarwa Har gadon kerma yake yi ita kanta jikinta ya kama kakarwa, tun zuciyarshi na bugawa a hankali har ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje, sautin numfashinsa mai haɗe da gurnani ya gauraye bedroom dinsa, da karfi Yake Jan shi tamkar babu wadatacciyar iskar da zai shaƙa.

Ko wani sashe na jikin shi tuni ya soma motsawa, Unaisah dake kallon shi idanunta azazzare duk tabi ta rude ta firgice Lokaci ɗaya tsoro Ya cika ta, Zabura tayi da niyar ta watsa aguje gudun kada Ya cutar da ita don ta fahimci kamar baya hayyacin sa ...

Sai dai kafin tayi wani yunkuri juyawa yayi wani kwakkwaran juyi tamkar mayunwacin zaki haka Ya damƙo sumar kan nan nata daya sha gyara gaba ɗaya ya dawo da ita jikin sa, Yana huci ya matseta kamar zai tsinkata biyu, Ji tayi tamkar an daureta da igiyoyin kaca, hucin zafin jikinsa har anata jikin take jin shi, Zuciyarta ce ta bata shawarar ta hankaɗe shi ta gudu, kafin yai yunƙurin cutar da ita, Cikin ƙarfin Hali ta daddage ta fusge kanta daga ruƙon da yayi mata, gaba ɗaya ta kundumo saman tiles kanta ya daku, Harta zabura zata mike da niyar ta watsa a guje taji ya damƙi ƙafarta ɗaya, ta ƙarfi ya janyota kamar ɗiyar roba ya dawo da ita saman gadon, runtse idanunta tayi da sauri tana ambaton La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.

Dogayen yatsun hannayensa dake kerma ya ɗaura saman wuyanta, ya shaƙeta sosai tamkar zai tsinka wuyan, radadin azabane ya ziyarce ta, ta kware baki ta fasa wata irin ƙara mai sautin gaske, sai faman kiciniyar kwace kanta take yi amma ta kasa saboda ƙarfin dake gare shi tamkar zaki a haka ma don bai da koshin lafiya da tuni yajima da kashe ta cikin rashin sani. Radadin da tajine yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske

Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga room din ta, don taje ta fara shiryasu ganin lokacin dinner din Ya kusa Cika

Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci ɗaya taji gabanta yai mugun faɗuwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba

A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah"

Kofar tamkar an datse ta da key taki buɗewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_

Ta faɗa jiki na tsuma ta zura hannu ɗaya ta dauko wayarta daga cikin aljihun skirt dinta.

Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin buɗe kofar ta datse..."

Muryarshi a ruɗe Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta ƙare maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun kaɗa jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta.

Kamar an jeho shi Ya faɗo falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ƙofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba.

Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya duƙar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai ƴan kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Haƙiƙa sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin ƴan kwanakin nan.

Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun aljani gashi ya damki yarinya a hannun shi

Cikin shessheƙar kuka Ummi take rokonshi akan Ya saketa, kada ya kashe masu ita.....'

Karfin Hali taj yayi da sauri Ya nufi gefen gadon inda su ke a zaune Ya miƙa hannayenshi biyu da niyar ya kawar da ita, Damƙar hannunsa Danish yayi tare da dagowa yana faman lumshe idanun shi tamkar na wanda yasha giya, muryar shi da kasala Ya furta"ina bukatar ruwan da zan yayyafa mata" kusan atare ummi da Taj suka sauke ajiyar zuciya, saboda sunyi tsammanin baya ahayyacinsa ne.

juyawa ummi tayi da sauri ta fita daga dakin sai gata ta dawo hannunta ruƙe da robar ruwan da ta ɗauko a fridge ta miƙa ma taj, shi kuma Ya kar6a ya Miƙa ma danish, a hankali Ya sanya hannu ya kar6a bayan ya cire murfin ya tarfa hannunsa dake ɗan kerma Ya ɗebi ruwan ya watsa mata akan fuskarta, lokaci ɗaya ta zabura zata fara buge buge da sauri boss Ya damƙi hannunta, tare da dago da ita ya zaunar.

Wani jiri jiri take gani a idanunta, hannu tasa ta dafe makoshinta tana fadin ruwa ruwa zan sha.

Kwafa mata ruwan yayi abaki ta rurruke robar duka ta shanye shi, ta dago da luhu luhu idanunta wadanda suka kada jawur da su Sam ta manta a ina take zaune, gani take kamar amafarki lamarin Ya afku, Kwata kwata bata lura da danish ba, wanda ke a gefenta kuma shi ya bata ruwan da ta sha.

"Unaisah, are you okey? Ina fata bai ta6a lafiyar jikin ki ba"! Cikin kulawa ummi keyi mata magana

Kallon ummi tayi murya na ɗan rawa ta furta"nayi mafarki danish Ya farka, Har Ya shaƙe min wuyana" ta faɗa tana shafa wuyanta

"Ba mafarki ki ka yi ba, dagaske ne Ya faru, danish Ya farka sai dai baya a hayyacinsa ne lokacin daya shaƙe ki" boss ne ya bata amsa, da wani irin Hanzari ta dubi danish da ke gefen ta, idanunsa suna a lumshe numfashin sa na fita a hankali.

Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kukan farin ciki, ta kamo yatsun hannayensa acikin nata, Muryarta cikin shessheƙar kuka take fadin"My man...kana lafiya? jinjina mata kai ya danyi alamar eh.

"Alhamdulillah Ya Allah, Alhamdulillah..." sakin hannunsa tayi ta sauko daga kan gadon ta zube saman gwiwowinta tare dakai goshi kasa tayi sujjada tana mai nuna godiyarta ga Allah.

Murmushi taj ya soma saki yana kallon danish, Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e shi mara misaltuwa Yaji dadin farfadowar nan tashi, Har ya fara tunanin haduwar shi da Prime minister.

Har yanzu Danish babu fara'a akan fuskar shi, jefi jefi Ya ke kallon su da lumsassun idanunsa, ganin lokaci na shirin kure masu yasa ummi ruko hannun unaisah tace su tafi su fara shiryawa, kamar karta baro dakin tana tafiya tana waiwayon danish gani ta ke kamar in ta fita zai koma yar gidan jiya, har sai da boss yace mata zai kira chief yanzu awaya tare da sheikh imam tukunna ta ɗan samu kwarin gwiwar barin dakin.....

Batare da 6ata lokaci ba, Taj Ya kira chief awaya ya sanar da shi dangane da farfaɗowar danish, A lokacin chief Har Ya kira likitan da zai duba shi, yayi murnar jin zancen tashin danish, kafin ma karasowar su dakin sai da ya Kira Shiekh Imam suka jira Ya zo falon Kafin suka sauko shi da likitan dayazo duba dashi a tare suka nufi dakin shigar su keda wuya Chief owais ya nufi danish, tamkar dan uwansa na jini Ya miƙa mashi hannu ya taimaka mashi ya sauko daga kan gadon gaba ɗaya yayi hugging dinsa a jikin shi, ya ɗaura hannayensa abayansa yana dan bubbuga shi, har rada yai mashi a kunna ya furta"nayi farin ciki da samun lafiyar ka, Ina fata babu abun da ke yi maka ciwo ayanzu..." ya fada tare da dafe kafadun danish ya dago da shi.
Chapter 23 · 0% Book details