Sashe 61
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mika mata hannu Aneelerh tayi muga wayar da sauri ta bata, duddubawa tayi kafin tace"zanyi magana da mahboob yakai maki ita wurin gyara, kada ki damu idan an dawo da ita sai ki nuna min hotunan" ajiyar zuciya zahra tadan sauke"shikenan amma duk da haka saina tsala masa wayar nan" ta fada tare da yunkurawa zata zane bayansa fashewa yayi da kuka yana fadin"aunty zahra kada ki bugeni, Allah Yana sama Yana kallon ki..." dariya zahra tayi"kasan da hakan shine ka fasa min wayar"? Muryarsa da shesshekar kuka Yace"ay mommy zata canza maki wata cikin kudina" tuntsirewa tayi da dariya cike da zolaya tace"ban ta6a sanin kai matsoraci bane sai yau, ay ko daga yanzu tun da na gano lagwonka, da zarar kamin rashin ji zan zane maka baya da wayar cazana" maƙe mata kafaɗa yai, ba tare daya tanka mata
*HAJIYA ADAMA🤍*
A hankali tai parking motarta, fitowa tai cikin shiga ta lace, ta yafa mayafi kan kafadarta, fuskarta manne da farin glass, Shopping bags ta ɗauko a back seat na motar, kafin ta Nufi cikin gidan tana gab da zata shiga bedroom din su ta tsinkayi Muryar Uncle abdallah yana waya
"Kayi hakuri nasan ba haka mukai dakai ba, na saba alkawari amma ka dubi halin da nake aciki, lokaci ɗaya na rasa ɗana bayan haka na rasa ɗan yayana tare da yarsa, na rasa yayana da kakata kai kadaine zaka Iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kudin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su indai suna araye na ƙwammace na ƙare rayuwata a talauci akan inci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..."
Muryarsa amarairaice yayi maganar kamar zaiyiwa mutun da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya
Cak Ya tsaya da yin maganar ba tare daya ƙarasa ta ba, sakamakon kamshin turaren hajiya adama da hancinsa ya shaƙo masa, a hankali Yai rejecting call din yana kokarin dai daita nutsuwar shi
"Ba halin ki bane Yi min la6e,"! Taji Ya faɗi fuskarshi ba fara'a
Bata tanka mashi ba, har sai da ta ƙarasa gaban gado ta daura shopping bags din kafin ta juyo ta dube shi da alamun rudani akan fuskarta
"Gaskiya ka faɗa ba halina bane, amma wannan wayar da kayi yanzu ta ɗan ɗaure min kaina, dear wani kudi ne naji kana fadin zaka mayar adawo maka dasu idan suna araye!? Har kake fadin ka ƙwammace ka ƙare rayuwarka a talauci akan ganin damuwana na rashin haihuwa? Su wanene kake yin magana akan su?
da wani irin kallon tuhuma take duban shi.
Hannu Yasa yaɗan shafa keyar shi, daga ganin fuskarsa babu kwanciyar Hankali, tsufansa Ya ƙara bayyana musamman fuskarsa duk tayi tamoji tamoji.
Maimakon Ya bata amsar tambayarta sai cewa yai"Har Kin kammala siyayyar?
Dame dame kika siyo mana ne" A waske Ya faɗa tare da nufar Shopping bags din da ta ajiye kan gado, Ya buɗe Yana dudduba kayan ciki.
Kamar sakarya Haka Ya barta a tsaye Tana kallon Ikon Allah.
"Hajiyata, Yunwa nake ji, pls Ki dafa min abunda zan dan ci"
gyaɗa kai tay aranta ta ayyana koma menene zan bincika duk da ba halina bane amma da buƙatar nasan dawa kake waya akan su wa kake magana
Cire mayafin tayi, ta daura sa kan gadon, Kafin Ta juya tana fadin"Sorry dear, nabarka da Yunwa, bansan lokaci Yaja har haka ba, bari naje kitchen na shirya mana abun da zamu ci"
Bayan fitarta daga dakin ajiyar zuciya ya sauke, kamar wanda Ya ku6uta daga hannun dogarawan sarki, kwantar da kansa yai kan pillow idanunsa sun kaɗa jawur bakomai Yake tariyowa ba face nasihar yayansa Malam Zaheer haƙiƙa yayi babban rashin da har abada bazai ta6a samun makancinsa ba
Agogon ɗakin Ya kalla kusan ƙarfe Biyar Na marece, lumshe idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin radadi daga gani yana acikin matsananciyar damuwa, Muryoyin su Uzair ne suka fara yi masa gezau acikin kan shi bazai ta6a manta ranar da suka shigo ɗakinsa da zumuɗin sanar dashi sun samu matayen da zasu aura.
"Kunyi shiru bakuce min komai ba"
"Taj ka fara fada masa" harara Taj Yai ma uzair ay kai yakamata ka faɗa masa ni kunyar shi nake ji Allah, acikin kunne sukeyin raɗar
Murmushi Uncle abdallah yai sai yake ganin kamar komai A yanzu Yake faruwa.
"Mijin mace ɗaya, abincin Ka Yana jiran ka" kamar daga sama ya tsinkayi muryar Hajiya adama, da sauri Ya mike Ya shiga toilet jim kadan Ya fito Ya nufi dinning din, A tsaye Ya same ta tana karasa jera masu abincin
Murmushi suka sakarma Juna"Bismillah, babyn Hajiya adama" atare suka zauna suna fuskantar Juna.
"Sannu da kokari matar mutun ɗaya, nagode da kulawarki agare ni, Naji dadin girkin nan" ya fada Yana kokarin tura jallop rice din daya debo a spoon"Shiyasa nake alfahari dake saboda kin Iya girki"
Murmushi tasaki Jin Yabon da yai mata"nima ina alfahari dakai," shiru suka danyi kowa yana cin abincinsa can ya ƙara dagowa ya saci kallon fuskarta karaf suka hada ido duk saiya rasa sukuninsa
"Wai lafiya naga kamar wani abu na damunka"?
Girgiza kai yai"ba wani abu, kawai ina tunanin ranar da zamu rabu" ras taji gabanta Ya fadi arude tace"Abdallah? Meya kawo maganar rabuwa? Anya kuwa kasan me Harshen Ka ya furta"?
Ya ɗan tsorata da ganin Yadda Ta ɗaga hankalin ta.
"Kaga In baka lafiya muje nakaika asibiti bawai ka kama Yi min sambatu ba"
babu wasa akan fuskarta tayi maganar.
Cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri hajiyata, Nima zolayarki nakeyi, maganar rabuwa da nayi kinsan akwai mutuwa ko kuma wata kaddarar ta rayuwa da zata iya sanyawa mu juyawa juna baya!
Harara ta galla masa, tuni idanunta sun ciko tab da ƙwalla mikewa tai da sauri tana fadin"banji dadin maganar nan ba, eh nasan mutuwa dole ce amma meye na kawo maganar rabuwa muna tsaka da cin abincin mu"? Ta jefa mashi tambayar hawaye nabin fuskarta shiru yayi sam ya rasa amsar da zai bata
"Na rasa uzair da taj, na rasa unaisah, haba kabarni inji da wannan radadin mana, akan me zaka tada min maganar rabuwa...." rai a6ace Ta bar dining din ta nufi bedroom dinta
Da sauri Ya miƙe yabi bayanta jiki na rawa saboda baisan bacin ranta, lallashin ta Ya dinga yi kamar zai mata sujjada dakyar Ya samu ya shawo kanta har ta daina fushin da shi
*💘EX-PRISONERS❤*
Wuraren ƙarfe takwas na dare Gaba ɗayansu sun hallara A main falo din gidan yadda kasan gidan biki ko suna, sai surutu sukeyi suna yin firar yaushe rabo abu Yaƙi ƙarewa kamar Yauce rana ta farko da suka fara sanin junan su, da alama dai gidan Chief Ya zama Gidan marayu kowa ka kalli fuskarsa annurin farin ciki ne, ummi tana azaune kan sofa tare da batool hannun ta ruke da waya video take daukar su ba tare da sun sani ba.
Mutun ɗayace babu acikin su, Unaisah dake a daki Tana shiryawa, kamar yadda sukai da daddynta zai kaita Part dinsa dake agidan, wata hadaddiyar abaya ta sanya launin black and white ta ɗauko mayafi tayi rolling nasa akanta, tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi da turare yarinya fa ta zama budurwa wani irin gayu take ji,
Bayan ta sanya takalma, ta soma tunanin Ina ta jefa wayarta, sai yanzu ta fado mata aranta, farat daya tafara tunanin aunty pretty matar da sukai waya shekaran jira da dare gaba daya ta manta saboda lalurar da ta same ta ga kuma baiyanar daddynta da yan uwanta da suka ƙara mantar da ita zancen matar.
_Neman wayar ta soma yi, tun daga kan mirror har cikin closet din su, tsabar ruɗu itace har karkashin gadon su neman wayar, zukunnawar da zatai keda wuya taci karo da kananun hotunan nan, tura hannu tayi tare da janyo su zuciyarta cike fal da tunanin hotunan wanene._
_Kamar a mafarki take kallon fuskokin mutanan dake akan hoton, wani babban mutun ne mai kyan sura ya ɗauki wankan tailored suit a jikinsa, ɗayan hoton baturiya ce fara sol itama suit ne a jikin ta._
_Ƙurawa hotunan ido tayi tana kallonsu ba tare data Iya gane daga ina suka fadowa ba, ko wanene Ya jefa su karkashin gado, to ko dai Aljanune suka ajiye su? ta fada acikin ranta, can kuma ta sake kallon hoton Alhaji sai taga kamar an daura mashi fuskar Sajeed banbancin su sajen dake a fuskar alhajin da kuma manyantakar sa shi kuma sajeed bai da saje a fuskarshi_
*Mu haɗu gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*
*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
1 COMMENTS
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Anonymous
27 June 2024 at 04:14
Dan Allah kurkukun kaddara takun karshe 22
Reply
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.