← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 238

Sashe 35

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu kamar wasa har Bayan Magrib ana gab da za'a rufe taron babu prime minister babu Unaisah, Ga mutane sunataso suyi mashi bankwana saboda ba lallai gobe su haɗu da shi, asubar fari zasu bar nigeria, babu wanda bai jaraba kiran layin hateem acikin su ba, sai dai wayar tayi tayin ringing, ba'a picking, Shima owais sun kira layinsa wayar bata shiga, ransu yayi mugun 6aci, sauƙin su ɗaya zuwan gimbiya mujeedat itace ta sanar da su inda Hateem yake, ba tare da 6ata lokaci ba, suka yanke shawarar zuwa can su same shi, kusan gaba daya mutanan hall din suka nufi gidan prime minister don suyi mashi bankwana tun da shi yaki dawowa dakin taron, yana can tare da sanyin idaniyarsa.,

Idan muka koma bangaren zahra da batool lamarin Ya fara Tsoratar da su ganin Har mutane sun fara watse wa babu alamun Unaisah zata fito daga toilet, kwatsam wayar zahra tafara ringing, da sauri ta ɗaga ganin sunan hajiya saratu.

"Meet me outside the hall right now, Zarah!" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, bayan ta katse kiran, Ta kalli batool jikinta yayi sanyi lakwas sam bata so ta tafi tabar Hall din ba tare da an gano unaisah ba.

"Ki yi hakuri sister batool, tafiya zanyi ba don naso ba, matar da ta gayyace ni dinner din nan itace take kirana, shawarar da zan baki, Ki sanar da sauran yan uwanki da kuma jami'an dake tsaron hall din su taimaka maki ku gano yar uwarku" ta fada tare da ruko hannayen batool a cikin nata kafin taci gaba da cewa"kada ki manta idan kun gano unaisah ki sanar da ita cewa na tafi da kewarta" batool ta amsa mata da toh, kamar kar su rabu da juna su ka yi sallama.

Bayan tafiyar zahra, batool tabi yan uwan su daya bayan daya ta sanar da su zancen bacewar Unaisah, nan fa hankalin su yai mugun tashi, su sajeed suka bazama nemanta, tsantsar tashin hankaline da damuwa akan fuskokinsu, babban abunda suke ma zullumi kada ace wani mugun abunne ya faru da ita, dama sun lura bakowa ke son su ba, tsaf za'a iya cutar masu da yar uwarsu, bacci tuni yayi awon gaba da jamimah, Sai dai haris ya goyata abayan shi, itama Azeeza daukarta Naufal yayi abayanshi sbd lalurarta, Parveen da su Hanna idanu sunyi jawur ga bacci suna ji ga kuma tashin hankalin rashin yar uwarsu, babu wanda Ya lura da halin da su ke a ciki saboda babu mutane sai jefi jefi wasu suna bakin hall wasu kuma sun tafi gidan Hateem kusan su kadai ne suka rage a hall din sai servers din dake tattara kayan abincin da aka yi amfani da su, da kuma interior designers din da suka fara kwashe kayan decoration din dakin taron.

A lokacin da ba su yi tsammani ba, Sai ga Boss tare da biy guy sun shigo hall din cikin takun sauri, sun zo ne domin tafiya da su ganin lokacin yayi, su parveen na ganin su suka fashe da kuka da gudunsu suka nufe su tare da fadawa jikin boss da big guy suna kuka suka fada masu basu ga unaisah ba, ta 6ace sun nemeta sun rasa.

Da tsantsar tashin hankali Taj Ya furta"wai wata unaisah ne ta 6ace? Ko kuna nufin Angel dina"? Adabarbarce Yai maganar Yana dubansu,

Sajeed Yace"ita muke nufi, tun dazu muke nemanta bamu ganta ba, mun duba ko'ina"

Kallon juna boss da big guy su ka yi a lokaci daya,

wani irin bugun fargabane Ya darsu a zuciyar taj, Jin Angel dinsa ta bata babu ita,

Muryarshi na rawa yace"bata fada maku inda taje bane"?

Hada baki sukayi wurin cewa Eh

Dafa kafadarsa Big guy yai ganin Yana neman rikicewa.

"In sha Allah babu abunda zai same ta, zamu nemo ta, sauƙin ma akwai cctv a dakin taron zamu ga inda ta shiga ne"

Mayar da dubansa yayi kansu batool"sajeed, Ka tafi da su bakin hall din, akwai Jami'an mu dake jiran ku zasu tafi da ku gida"

Muryar batool da shesshekar Kuka tace"ni dai bazan iya tafiya, in ba tare da unaisah ba, zan jira har agano ta ...." kafin ta rufe baki Sajeed Yace"nima bazan tafi ba, kamar yadda muka zo tare da yar uwarmu atare da ita zamu koma"

!

"kwara kubarmu anan wlh ko mun koma gida, hankalin mu bazai kwanta ba, ko runtsawa bazamu iya yi ba, in har unaisah dinmu bata dawo ba...." Haris ne ya fada idanunsu sun ciko tab da kwalla, gaba ɗaya sun turje akan ba zasu tafi ba....

Cikin rauni na murya taj Yace"Ya isa haka! Ku daina zubar da hawayen ku, ku samu wuri ku zauna Yanzu zamu nemo ta," da sauri suka samu kujeru duk suka zauna suna jiran tsammani

Ba su fara zuwa dakin cctv din ba, big guy ne ya bada shawarar su fara bincika restrooms din dake a hall din kafin su fara zuwa can, da sauri suka nufi hanyar da suke, daya bayan daya suka dinga dudduba cikin su ba su ga kowa ba, cikin rashin sani suka tsallake kofar wanda take a ciki ba tare da sun ankare ba, tsabar kidima yasa taj sulalewa jikin bango Ya zukunna, idanunsa sun kada jawur dasu, fuskarshi duk ta yamutse idan harfa ba ganin unaisa sukayi ba to kuwa bazai ta6a dawowa dai dai ba

"Ni nafi tunanin ko dai tabi family din chief xuwa can gidan prime minister" big guy ne Ya fada Yana duban fuskar taj, wanda tuni ya hada gumi duk da sanyin A.c din dake a wurin babban tashin hankalin shi kada Ya rasa yarsa tilo da yake da ita, tabbas zuciyarsa zata iya bugawa.

Ganin bai da alamun motsawa ne Yasa Big guy dafa kafadarsa Cikin kwantar da murya yace"dan Allah ka yi hakuri ka daure ka ta shi, mu shiga cctv room din zaifi sauki muga ina ta shiga"

Zuciyarshi a hautsine Ya cire facemask dinsa tare da jefar da shi gefe daya.

Cikin sanyin murya ta wanda Ya karaya yace"Wallahi tun ina agidan su salsabeel nake jin faduwar gaba, shiyasa nakasa samun nutsuwa na kamo hanya nazo hall din nan ashe abun da zan taras kenan" ya fada tare da kallon big guy"ka tafi ka duba, don bana jin zan iya matsawa daga wurin nan, jiri nake gani a idanuwana"

Dan murmushin gefen fuska Big guy yayi mashi dazolaya yace"duk son nan da kake yi mata ahaka zaka damka ma wani kato ita yaci gaba da kula da ita"

Kallon harara Boss Ya jefa mashi"kaga pls kada ka daura min wani hawan jinin, ka tafi kawai, Ina jiranka"

Yar dariya yayi kafin ya juya ya bar wurin

Dafe kansa yai da tafin hannunsa, wani irin ciwon kaine Ya farmasa, Yana cikin wannan Halin, kamar ance ya dago ya kalli Floor din wurin nan take eye balls dinsa suka sauka akan Stone din rigar unaisah, da alama daga jikin rigarta Ya fadi kasa, mika hannu yayi tare da daukar shi Ya kura ido Yana kokarin tariyo a ina ya ta6a ganinsa, sai da ya zurfafa tunaninsa kafin lokaci daya ya zabura ya mike yana bin kofofin toilet din dakallo saboda ya tuna itace ta sanya abaya me adon gold stones.

Kofar da suka tsallake basu duba ta ba, ita Ya nemo, ganin ta adatse ya kara tabbatar mashi da tana a ciki.

Muryarshi har rawa takeyi wurin ambaton sunanta"Unaisah!Unaisah!My Angel" shiru ba'a amsa mashi ba, nan fa hankalin shi ya kara tashi, Ga shi Ya duba babu key jikin kofar, Karfi yasa wurin bangaje ta da kafadunshi sai dai ko gizau kofar batayi ba, Ja baya yayi kafin Ya nufeta da iya karfin shi na karshe yayi mata wani irin bahagon bugu, nan take kofar ta saki, shi kanshi bai yi tsammanin Yana da karfin da zai Iya bude ta, batare da key ba Allah ne ya taimake sa.

Karasa ture kofar Yayi, a fujajen ya fada cikin toilet din yana faman zubda gumi, shigar shi ke da wuya idanunsa suka sauka kan Unaisah dake kwance saman floor, baiwar Allah ita kaɗai tasan radadin azabar da ta fuskanta, taci bakar wahala ta jigata sosai, zufa ta gama wanke jikinta, Takalmanta ware da ware sun yi gefe guda, Ga mayafinta a kasa, hannunta daya dafe a saitin cikin ta, da wani irin rauni da murya ya furta"My Angel" A sukwane da sanyin gwiwa Ya zube gabanta saman gwiwowinsa, duk irin dauriyarsa baisan sa'adda hawaye masu dumi suka soma sintiri kan kuncinsa ba, yatsun hannayensa na kerma ya daura su kan kafadunta tare da janyota ya dawo da ita kan kirjinsa, ya rungume abunsa tare da runtse idanunsa yaci gaba da shesshekar kuka Yana ambaton sunan ta....

"Am.. sorry my Angel laifina ne da ban zauna a dakin taron ba, da duk hakan bai faru ba....."

Baisan meke damunta ba da yai silar shigarta wannan Mawuyacin halin, baisan Ya akai aka kulle ta a restroom ba.

Yana acikin wannan Yanayin big guy ya shigo da saurin shi, Yana ganin taj rungume da unaisah Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Daga bakin kofar ya tsaya don baisan me zai taras ba.

Cikin sanyin murya yace"idonta biyu"?

Muryar taj kasa kasa Yace"bansani ba, kamar ta sumane anan, amma daga gani taci bakar wahala"

Big guy yace"mun gano wacece Ta kulle ta a restroom din, Kuma in sha Allah zamu bincikota sai ta dandani kudarta wallahi" Yana fuci Ya faɗa

Babu alamun taj Ya fahimci me yake cewa hankaklinsa na akan Angel dinsa yace da shi"please Ka koma wajen yan uwanta kada su ji mu shiru, yanzu zan fito da ita" amsa mashi yayi da okey, a hanzarce Ya fice.

Har ya yunƙura zai mike Yaji alamun lemar wani abu a hannun shi, da sauri Ya dago da tafin hannunsa Yana kallon jinin daya ta6o, sai lokacin Ya fara jin karninsa a hancinsa, Idanunsa azazzare yake kallon jinin Hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta dinga harbawa da karfi da karfi tamkar zata fasa kirjinshi,duk a zaton shi wani mugun abun akayi mata, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana mashi kodai raping dinta wani yayi ko kuma Wuka aka caka mata.
Chapter 35 · 0% Book details