← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 238

Sashe 39

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya ƙi komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya haɗa mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai buƙata......

Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba ɗaya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba ɗaya hankalinshi baya akanta....

Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta.

Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta.....

Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba.

Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta.

Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar hausar ke fita irin ta ƴan koyo.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa

Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta ɗebe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira kaɗan kaɗan saboda rashin sabo, da kuma ƙarancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba.

Tun daga ranar daya haɗu da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, roƙansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ƙara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta ƙwalla rai akanta ne?

Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da buɗar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu na neman wuce gona da iri.

Cikin kwantar da murya yace masu su yi hakuri, su daina bugunta indai saboda shi ne yanzu zai tafi yabar masu rigarsu" sam basu fahimci me yake cewa ba, sai ma wani irin kallon tsana da suke jifar shi da shi, har ya juya zai tafi danejo ta ruƙo hannunsa, a fusace gidado ya ruƙo hannunta, suka riketa don kada tabi shi.

Sautin kukanta ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, shi kanshi baya son rabuwa da ita, ba don yaso ba sai don ba yadda zaiyi ne...

Har yayi nisa da tafiya, ya ɗan dakata zuciyarshi na raya mashi ya juya ya kalle ta, watakil bazai sake haɗuwa da ita ba, har zuwa lokacin da zai bar dajin,

Juyawar da zaiyi keda wuya, kwatsam idanunsa suka sauka akan rigar Angel dake shanye kan ɗaya daga cikin bukkokin su, daga gani wanke ta akayi aka shanya don ta bushe, da farko bai tantance abunda idanunsa ke nuna masa ba, sai da ya ɗan kara ƙura idanunsa tukunna Ya shaida itace rigar baccin da ke a jikin Angel aranar da ya gudo da ita, sune kayan jikin ta, was wasi yafara yi a cikin zuciyarsa tayaya akai rigar unaisah tazo dajin a hannun fulani? Ko dai suma suna da irin rigunan gayu ne"? Farat ɗaya zuciyarshi ta bashi amsa da cewa me zai kawo irin wannan suturar a hannun mutanan da ke rayuwa a daji? Sai dai idan tsintar ta su kayi...' muryarshi na rawa ya furta"idan har dagaske ne abunda nake hasashe tabbas Wani ya ceto rayuwar Angel ɗina bayan na jefata a cikin ruwa tun da gashi har rigarta ta bayyana...

Ba zato ba tsammani, suka ga mutumin da suka kora ya watso da gudu ya dawo wurin rigarsu, har sun har zuƙa zasu fara dukanshi da sandunan su sai kuma suka fasa ganin Ya damƙo rigar da danejo ta shanya kan bukka, ruƙe rigar yayi a hannunshi zuciyarshi na bugawa da matsanancin karfi ya soma ambaton sunan Angel Angel, Lokaci ɗaya su bawuro da su hasiya suka kalli juna da mamaki jin yana ambaton sunan yarinyar da danejo ta tsinto a cikin ruwa, tambayar shi suka soma yi wanene shi? Ya akai yasan yarinyar?

Hawaye na zuba daga idanunsa ya dago rigar yana nuna masu yace" wannan rigar ta ƴata ce Angel, da hannuna na jefa ta cikin ruwa, dan Allah ku fada min a ina kuka samu rigar? Ko dai kune kuka ceto rayuwarta....." kukane yaci karfinsa, gaba daya ya rikice masu, su kansu so suke son san me yake cewa don suji ko shine mutumin nan da yarinyar take nema don bazasu ta6a mantawa ba da irin kukan data dinga yi masu tana kaisu bakin ruwa donsu nemo mata daddynta tun basu fahimtar me take cewa har suka gane cewa wani nata ne take nema..

Danejo ce kaɗai ta fahimci me Yake cewa, nan take ta fashe da kuka Cikin harshen fulatanci ta sanar ma sauran ƴan uwanta abun da taj Ya ke faɗi nan suka gane cewa shine mahaifin Angel, yarinyar data tsaya masu aransu, har yau har gobe basu cireta aransu ba, hakika sunyi farin ciki mara misaltuwa da ganinsa.

Tsabar farin ciki yasa danejo ta watsa da gudu ta fada kan kirjinsa ta rungume shi tana kuka, ta soma tambayarshi ina Angel? Ko ya ganta"? Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, a ruɗe ya tambaye ta me take nufi? Ba su suka taimake ta ba" cikin sanyin murya danejo ta labarta mashi komai daya faru tun daga lokacin da ta tsintota a cikin ruwa har zuwa time da ta gudu daga rigar su.

Wani irin jiri yaji yana shirin kwasarshi saboda kuncin dayaji, bakomai ne ya jawo mashi jinkirin da yayi ba nazuwa daukarta face loosing memory din da yayi.

Zubewa yai kan gwiwowinsa zuciyarsa a hautsine tamkar zata buga, gaba ɗaya suka kewaye shi, suna kallon shi gwanin ban tausayi, ganin yadda ya ke matsar kwalla.

Saboda son da suke ma Angel yasa suka yi mashi kyakkyawar tarba, a kalla ya shafe wata a rigar su, kafin Yaji bazai iya cigaba da zama a dajin ba, kwara ya koma gida watakil idan yaje can ya sameta ta koma wurinsu Aneelerh.

Ranar da taj ya shirya tafiya, zai bar rigar, ya yi masu bankwana kamar karsu rabu, yace masu zai fara zuwa wurin mutanan da suka taimake shi kafin ya wuce garin su, guzurin tafiya suka hada masa, kowa ya kawo abunda yake dashi, suka bashi sannan sukace mashi idan Allah yasa yaga yarsa angel ya fada mata sunyi kewarta, zuciyarshi cike fal da kewarsu ya kamo hanya zai bar rigarsu, harfa yayi nisa yajiyo takun gudunta sai faman kwala mashi kira takeyi, a hanzarce ya juya yana kallonta, danejo ce hannunta ruƙe da kullin kayanta, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, ganin ta biyo shi.

Karasowa tayi tana haki tace"dan Allah ka tafi dani inason ganin Angel"

Girgiza mata kai yayi"kiyi hakuri bazan iya tafiya dake ba, meyasa kika yarda dani har haka? ki yi hakuri ki koma wurin ƴan uwanki" fashewa tayi da kuka.

Ana cikin haka, yajiyo sautin takalman yan uwanta kusan gaba dayansu ne suka biyota.
Chapter 39 · 0% Book details