← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 238

Sashe 13

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mungode sosai, Allah yasaka maku da mafificin alkhairinsa, Allah ne kadai zai iya biyanku, " godiya suka shiga yi ma shiekh imam da boss man......

"Yakamata kuje ku kwanta, ku yi bacci kada a makara" amsa mashi su ka yi da toh, bayan sunyi ma sheikh imam sallama, Suka nufi hanyar fita daga dakin jin takun tafiyar sune yasa ummi tayi saurin nufar bedroom dinta tana shiga ta fada saman gadonta taci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita...

Unaisah taso ta samu damar ganin danish dakyau, amma saboda shiekh imam yasa takasa tsayawa, Idan har ba ita ta kashe mashi switch din dakinsa ba, ta kuma lullu6e shi da bargo ba, to kuwa hankalin ta bazai kwanta ba, tunani zatai tayi kamar ba'a lullu6e shi.

Ɗaya bayan ɗaya kowannansu ya nufi room dinsa bayan sunyi sallama wa junansu, zuciyoyin su cike da zullumin halin da danish yake a ciki.

Basu bar dakin shi ba, sai da Taj Ya lullu6e shi dukanshi da bargo, ya kuma kashe switch din kafin Suka fito tare da sheikh imam, har bakin motar da aka kawo shi ya raka shi, sun ɗan juma a jikin motar suna tattaunawa duk dai akan halin da danish yake a ciki ne, har ƙara jaddada mashi sheikh yayi akan su dinga dubawa akai akai ko Allah zaisa ya farka daga baccin, kafin daga bisani su ka yi sallama.

_______________________Boss Bature✍️

💋CHIEF OWAIS💪

Aso Villa.

A yayin da yake a kwance saman katafaren gadon shi dake a Villa tsantsaran gaske, ya lullu6e half body dinsa da lallausan duvet dinsa, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake fitar da numfashin sa, ga wani irin sanyin A.c daya ƙarama dakin nashi ni'ima, babu haske dakin sai na bedside lap ɗaya da aka bari a kunne...

sautin ringing ɗin wayarsa ne ya farkar shi, da wata irin kasala ya kai hannu ya lalubo wayar, A hankali yaɗan ware reddish eyes nasa masu dauke da bacci ya duba sunan mai kiran nashi, yayi mamakin ganin kiran prime minister Hateem, slowly ya dubi agogon bango ƙarfe wani abu na dare.

Ya ilahi ya faɗa a zuciyarsa kafin ya miƙe zaune ya ɗaga kiran ya ƙara a kunnansa

"Uncle... " iya abunda ya iya furtawa kenan.

On the other hand muryar prime minister ta karade kunnuwansa.

"I'm sorry na katse maka baccin ka, na tashi yin night prayers ne, shi ne na kiraka don inji awani hali yarona yake aciki, saboda mafarkinsa ne ya tada ni daga bacci" chief owais dake ta faman lumshe idanunsa, cikin yanayi na kasala ya furta"uncle saboda shi ka tada dani daga bacci"?

"I'm so sorry my son, bansan ya zanyi maka bayani ba"

Lumshe sexy eye dinsa yai kafin a hankali ya furta "Uncle, ka kwantar da hankalin ka, yanzu ni bana agidana, nazo Villa ne, amma in sha Allah gobe zan koma gidana da wuri saboda shi'

Har cikin ran prime minister yaji dadin maganar Owais

"Zullumi nakeyi, daga gobe shikenan bazan sanya shi a idanuwana ba, jibi da asuba jirginmu zai bar nigeria, gani nake kamar idan na tafi ba lallai na sake dawowa ba, balle har na sa ran ganawa da shi.... " dafe kai chief owais yayi da hannu ɗaya, Lamarin yafara kokarin rikata mashi lissafin kwalwarsa, aranshi ya ayyana anya kuwa Daddy Hateem bai fara zaucewa wa ba? ko dai ya samu matsalar kwalwa ne? Ko kuwa yafara ɗaga kwalba ne, Idan ba haka ba akan wani dalili zai ɗaga hankalin shi akan yaron da bai haɗa alaƙar komai da shi ba? Wannan wata irin ƙaunace?

Jin shiru chief owais bai furta mashi magana bane yasa shi cewa"naji kayi shiru son, ko ka koma baccin ne...

Slowly ya mayar da kanshi saman pillow,.

"Uncle, I'm confused..."

kafin ya ƙare maganar prime minister ya tari numfashin sa

"I'm confused too, Owais....nasan me ka ke tunani aranka, may be ma kana yi min kallon kamar nafara zaucewa, owais na dauki soyayyar yaron nan amatsayin jarabta daga Allah, ni dai kawai fatana ya zama alkhairi agare ni, dan Allah ka tayani da addu'a Allah ya bashi lafiya...

Lumshe ido chief owais yai, bakomai yake tariyowa ba face ranar da suka fara tozali da juna shi da danish suna a saman bene, suka jefa ma junansu kallon kallon, aranshi ya ayyana ba lallaima idan yaron ya dawo hayyacinsa ya kula prime minister ba saboda Yana da ilmin sanin halayyar ɗan adam, da ido kawai ya kalli danish ya fuskanci yana da wuyar sha'ani, yin mu'amala da shi ba abu ne mai sauƙi ba.

"In sha Allah zan tayaka da addu'a, ni dai fatana ka daina sanya damuwa aranka, ka kwanta ka yi bacci, muna da liyafa a gobe"

Yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar prime minister ta cikin wayarshi.

"Nagode da kulawarka agareni my son, Allah yayi maka albarka" amsa mashi yayi da ameen

Har zaiyi rejecting kiran muryarsa ta sake katse shi

"Pls kada ka koma bacci, ka tashi ka shiga toilet ka dauro alwala, kayi mashi nafila ko da raka'a biyu ce, Allah ya bashi lafiya"

Babu musu yace"In sha Allah zanyi" bayan sunyi sallama, chief owais yayi shiru yana tariyo kalaman Daddy hateem, shi kanshi yafara hasashen tabbas akwai wani 6oyayyan sirri dake a tattare da kaunar da uncle dinsa ke yima yaron Allah kadai yasan ko menene.

Jefar da wayar yayi saman gadon, kafin ya miƙe ya zura ƙafafuwansa ƙasa inda ya ajiye gucci slippers din sa, yunƙurawa yayi ya miƙe ya nufi switch din dakin ya kunna a hankali haske ya gauraye ko'ina, wato wani hamshaƙin bedroom ne, komai na cikinsa launin royal blue and white colour ne.

A gaban dressing mirror ya tsaya tare da ɗaura hannun shi ɗaya ya dafa mirror chair.

Wasu hadaddun Cashmere pajama ne a jikinsa riga da wando masu tafshi launin sky blue, sumar kanshi tasha gyara sai daukar ido take yi ga wani kamshi dake fita daga cikin ta, chief karshe ne a fagen haɗuwa.

Moving slowly ya nufi ƙofar toilet dinsa ya shiga daga ciki, alwala ya ɗauro ya fito fuskarsa da lemar ruwa ya nufi walk-in closet dinsa jim kadan ya fito sanye da jallabiya, ya hau kan darduma ya dai daita nutsuwarsa da kyakkyawar niya ya kabbara sallah.

A kalla yayi kusan raka'a goma sha takwas batare da gajiyawa ba, har sai da yaji kafafuwanshi sun soma rurruƙewa tukunna ya dakata, ya zauna yana jero addu'o'i duk dai akan danish yayi su kamar yarda Uncle hateem ya nemi alfarmar yayi mashi.

Bayan ya kammala komawa yayi saman bed nasa ya kwanta, tare da kai hannu ya ɗauki wayar shi, jim yayi yana mai mamakin ganin sakonta, a kalla sunfi wata biyar ko sallama basa yi ma juna, shiga cikin message din yayi, tare da karanta sakon da ya gani, ko kusa bai ji su a zuciyar shi ba, saboda kokwanton da yake yi, video din Ya kunna ya fara kallo, yana faman lumshe idanun shi, tayi mashi kyau yaji dadin kallon video din, almost 3 times yana maimaita kallon shi, kafin daga bisani ya fita daga chat din ya daura idanunshi kan hoton wallpaper din sa.

A tsanake yake kallon baby face dinta, ta zare idanunta a hoton daga ganin hoton screenshot din shi aka dauka, kuma anyi hoton ne batare da sanin ta ba.

Sam baya gajiya da kallon hoton, A hankali ya ɗaura soft pink lips dinsa saitin fuskar ya sumbace ta, kafin ya ɗaura hoton saman kirjinsa a haka bacci yai awon gaba da shi.

________________________✍️

Taƙi runtsawa ta addabi kowa ta hana su bacci saboda Jazz baizo ba, tace in har baizo ba to bazatayi bacci ba suma kuma bazasu yi ba, dakyar Salsabeel Ya shawo kanta Ya samu ya lalla6ata har ta ƙyale sauran ƴan uwanta suka kwanta a dakunansu, itama takwanta harfa ya kwanta da niyar ya runtsa can tsakar dare yajiyo bugun ƙofa, a firgice ya farka Yaje ya buɗe, Khadeeja ya gani tsaye ta ruƙe qugu tana faman kumbura mashi fuska tace Ina jazz din yazo? Agogo ya kalla sam yama kasa buɗe baki ya bata amsa, tace dama nasan baizo ba, ya manta dani, wlh Allah nima nayi fushi da shi.

Cikin kwantar da murya salsabeel yace"dan Allah kiyi hakuri kije ki kwanta bacci, dare ne yanzu, gobe in Allah yakaimu da safe zan kira maki jazz"

Maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata kwanta ba, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ɗaure mata fuska ya daka mata tsawa tare da fadin"Zaki wuce kije ki kwanta ko saina yi ƙwallo dake" fashe wa tayi da kuka da gudu ta nufi falo ta zauna saman sofa tana kuka, ko tsoro bata ji ita kadai kamar aljanna" ko ta kanta baibi Yaja kofa Ya rufe Ya koma ya kwanta.

Sai da tayi kukan mai isarta, kafin Ta miƙe tana shafa ciki Alamar yunwa take ji, kaitsaye ta nufi Kitchen ta shiga ta soma kiciniyar kunna gas, tsabar rigima.

Mutsu mutsu tajiyo a kunnanta, hakan yasa ta dakata ta juya tana ƴan waige waige don ganin menene, Karaf idanunta suka sauka akan Ƙatoton 6eran dake tafiya saɗaf saɗaf Yana tunkarota baƙi wulik da shi, sam bata ji tsoron shi ba, Abun ka game ta6in hankali, Praying Fan ta ɗauko cikin sanɗa tabi bayan shi ta daddage ta kwaɗe shi da fan ɗin, ko shurawa baiyi ba ya sheƙa, Bindin shi ta ruƙo tana faman sakin nishi tace"Zaka ci ubanka, Kai ne 6arawon dake cinye mana sauran da muka rage a kitchen ko"? Ta faɗa tana leƙen idanun 6eran Yayi zuzuru dashi.

"Ba zaka yi magana ba? Baka da gaskiya bakin munafuki, kai ne kake gwigwiyar mana bready, Bari na kai ka Gaban Alƙali Ya salsabeel Ya kashe min kai har lahira"

Ta faɗa tare da fitowa da gudu ta nufi bedroom din salsabeel, Har Ya koma bacci, Yajiyo muryar khadeeja tana fadin"Ya salsabeel Ka buɗe min kofa na kama 6arawon dake cinye mana sauran abincin mu, gashi nan a hannuna, Ya salsabeel ka buɗe zai gudu'

Afirgice Ya farka har yana tuntube garin sauri, koda Ya buɗe ƙofar Miƙa mashi 6eran tayi

"Gashi ka kashe shi ko ka cire mashi hannayensa"
Chapter 13 · 0% Book details