← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 238

Sashe 178

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ƙari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ?

girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..."

ta ɗan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da ɗan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba.

Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa ✍️

Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel.

Gaba ɗaya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matuƙar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa.

Ƙafafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su.

har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa..

Kallo ɗaya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruɗar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi.

A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi.

Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan.

abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj.

bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci.

A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta ɗaga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata ɗanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske.

yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar"

mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta.

Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana..

Ko gama wayar basuyi ba ya mika ma Chief saboda wani yanayi dayake ji atare da shi, Zuciyarshi Ta kasa samun sukuni tun kafin su bar garin Ya fara jin matsananciyar kewar Unaisah.

Tafiya yankin azaba sun ɗauki tsawon awanni akan hanya, da misalin sha biyun dare, suka qaraso cikin Dajin da suka haɗa katafaren sansaninsu, dajin yana a kusa da evil forest, katafaren Military base ne mai girman gaske ga wasu Irin Dakarun Sojaji masu ƙira irin ta zakuna kowan nan su yana asanye da army combat uniform dinsa, Cikin takun majiya karfi suke sintiri a cikin sansanin tamkar da rana saboda hasken electricity din dake a ko'ina na sansanin.

Bayan sun fito daga cikin motocin su, duk inda suka gifta cikin girmamawa sojojin ke sara masu tare da yi masu maraba da zuwa, a haka har suka shiga inda masaukinsu yake domin su dan hutu na wucen gadi.

THE DAY👹👺

Asubahin fari suka farka daga bacci, musulman dake acikin sukayi sallah awani ke6a66en wuri dake a cikin sansanin, bayan sun yi kalacin su, gaba ɗaya sojojin suka hallara a filin dambe, suka fara motsa jikin su har dambe sai da su ka yi a tsakaninsu wanda ya kasance kamar gasa ce su ke yi, Danish ya zama zakaran gwajin dafi a wurin an kasa samun wanda zai kayar dashi dayawa sun kara samun kwarin gwuiwa da ganin irin kwazon shi, bayan sun gama damben suka ɗan huta har wuraren ƙarfe shida na marece kafin daga bisani suka fara shirin shiga evil forest.

A helipad din dake a wani sashe na cikin Sansanin Wasu dankara dankaran Jiragen yaƙi ne a jere masu saukar ungulu da aka tanadar masu, ko da ido ka kalle su sai gabanka ya fadi, already fighter Pilots ɗin da zasu Yi jigilar daukarsu tuni sun shige cikin helicopters din.

Bayan komai ya daidaita, har dakarun sojojin sun gama shiga cikin jiragen, Kafin wani Lokaci jiragen suka lula sama, yayin da trucks ɗin makamai dake tafiya akasa suke bin su.

*FATAN NASARA*

____________________________________✍️

*🔥GIDAN KURKUKUN ƘADDARA🔥☠️*

Farkawarta kenan daga bacci, A hankali ta buɗe idanunta tare da kallon rufin gadon, Har na tsawon mintuna, har rama ta qara saboda azabar rashin lafiyar da tayi.

ta wutsiyarta idanunta ta hangi mutun kwance gefenta, da sauri ta wurga idanunta akanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin tsohuwa khala, da alama tayi nisa acikin baccin ta, ta ɗan yi mamaki don tunda ta tsinci kanta a dakin khala bata ta6a kwana kan gadon ba, a saman kujera take yin baccin ta a zaune kamar dogari.

Kasa kauda ido tayi daga kallonta, wani irin kaunar dattijuwar take ji acikin zuciyarta, batasan sa'adda ta matsa kusa da ita ba takai hannu ta shafa gefen fuskarta mai tarin tamoji tamoji, ta manna mata sumbata kan goshin ta ta danyi murmushi har chin dimple dinta Ya motsa.

"Bayan ɗan uwana gabriella, bani da abu mafi soyuwa daya wuce ke, Inasonki Khalana.." kamar daga sama ta tsinkayi muryar Khala acikin kunnanta"Nima Ina sonki Jikata" zare brown eyes dinta tayi fuskarta dauke da annurin farin ciki ta furta"Khala, Idonki biyu"? Ta fada akagare da son jin amsarta..

A hankali Khala ta buɗe idanunta akan fuskar Gabriellah.

"Ya jikin naki Jikata"? still da murmushi kan fuskarta tace"Naji sauki, yanzu babu inda keyi mani ciwo"

Tattausan murmushi khala ta sakar mata"haka nake sonji, Na lura kamar Kina farin ciki Yau, saboda tunda nake dake banta6a ganin murmushin ki ba..." yar dariya Gabriel tayi

"khala, kece silar farin cikina, da na yanke kauna da rayuwar duniyar nan, amma silar haduwana dake da kuma alkawarin da kika daukarmin na haɗani da ɗan uwana Yasa naji Ina son na rayu, Ina son na zama jajirtacciya jaruma kamar ke, kuma ina son na ɗauki fansar abunda akayi mana" tunda tafara magana khala ke binta da kallo, arayuwarta tana Son ya'ya musamman idan tagan su cikin nishadi da walwala shiyasa aduk lokacin data ga ana azabtar da rayuwar su take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin da takaici.

"Amma khalana, Idan muka yi nasarar ku6uta daga kurkukun nan, atare zamu rayu ko"? Murmushi khala tayi"Idan na fita bansan inda zanje ba, bani da kowa, ko kina da inda zaki ajiye ni"?

Shiru gabriella tayi tare da ta6e bakinta kamar zatay shagwa6a tace"nima bani da kowa, amma dani da ɗan uwana Gabriel, zamuyi aiki tukuru, donmu gina gidan da zamu zauna, nayi maki alkawarin zamu baki kyakkyawar kulawai..."

cike da nishadi khala ke sauraronta..

Kwatsam suna tsaka da yin fira, ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka jiyo masu wani irin sautin Bugun ganguna dumdum kamar dodon kunnan su zai fashe, tsabar sautin bugun gangar Ginin Har girgiza yakeyi, hatta gadon da suke kwance akai ya kama girgiza.

gaba daya Gabriella tabi ta ruɗe, baiwar Allah dama ba lafiyar kwalwa gare ta ba, da sauri ta toshe kunnuwanta da tafukan hannayenta.

Tsohuwa Khala kuwa tashin Hankali da farga Ya hana ta motsa sai faman zare idanunta takeyi.

Lokaci ɗaya suka daina Jin bugun gangar, sai kuma suka fara jiyo ɗaddaɗar Busar sarewa tana tashi

lokaci ɗaya yanayin fuskar Khala Ya sauya, aruɗe ta furta"ELDERS"

Cikin ruɗu Gabriellah ta kalle ta cike da rashin fahimtar me take nufi..

Damƙo hannunta tayi acikin nata"akwai abunda na manta ban fada maki ba, daren yau dare ne mai hadarin gaske, bugun gangar da kika ji alama ce dake nuna ƙarasowar ELDERS.

"abunda nakeso dake ki 6oye karkashin gadon nan, kada ki kuskura ko tari kiyi idan ba haka ba zaki jefa rayuwar ki cikin haɗari ne.."

Hankalin Gabriella ba karamin tayi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"Dan uwana fa? kada su kashe min shi..."

katse ta khala tayi"babu abunda zai same shi, kiyi abunda nace maki kawai"
Chapter 178 · 0% Book details