← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 238

Sashe 176

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing.

Madaidaicin table din gabansa na ɗauke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya.

Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa

"have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba.

Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi..

Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka ɗauka kasha naka ne"

yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.."

Ƙiris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ruɗe yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa.

"Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"!

Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..."

Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi.

"hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"?

ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi.

"Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Yaƙi ne?

"Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi

"Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine ɗa namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada.

Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala.

"Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya faɗa

Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko ɗaya, dan leken asiri nane ya fada min"

"why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"!

Ya fada rai abace

"Naji Ubana Obinna, zan dakatar da ɗan leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ruƙe hannayensa acikin nashi.

"Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice.

"pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...."

Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta.

Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba.

"Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda ɗan leƙen asirin nawa ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Yaƙi a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_

ya faɗa babu wasa akan fuskar shi, harya buɗe baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"na gama magana Owais," ya faɗa tare Ya duba agogon hannunsa

"I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce.

Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu ƙaddamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karan❓

Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi.

Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba.

Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace.

Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci ɗaya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint ɗin daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking ɗinta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana.

Gwiwowin ƙafafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta ɗebe shi gaba ɗaya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi.

Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking.

"My baby boy, how are you"?

Kokari yake ya buɗe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy."

yana faɗan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi.

Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne?

Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ƙara sanin inda kan shi Ya ke ba..

(TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA🤔❓)

__________________________________✍️

Yayin Da Chief Owais ke a garƙame Cikin ɗakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa Ƙarfe biyar na maraice dai dai ba ƙari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuɗe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan yaƙi sun shirya tsaf.

Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform.

Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a alƙawari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a ɗauki abun da mahimmanci ba ne.

Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka ɗaga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu"

ya faɗa idanun shi akan screen ɗin wayar shi dake ruƙe a hannun shi..
Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"?

"Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..."

Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa"

"Har layin daddyn nasa na kira baya shiga"

"To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta ɗaga"

"Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran

Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number..

Buɗe sakon yayi tare da karantawa

_Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_

(Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta mayaƙan, Na soke kai farmakin)

Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaɗa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa.

jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin Buɗe kofar main Falon, zumbur Ya miƙe Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu...

ɗaya bayan ɗaya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna..

Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"?
Chapter 176 · 0% Book details