Sashe 49
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salsabeel Yana atsaye gaban motocin da za su shiga,, Jami'in da zaiyi driving din su Har Ya hallara a mazaunin driver, da gudun gaske khadeeja ta fito hannun ta ruke da takalmanta, har tana bangaje Su Yasmin, kamar a filin Yaki, gaba daya hankalin Jami'an dake tsaron gidan sai da ya dawo kanta, wani burgujejen wando tasanya yadda kasan kafafuwan agwagwa, ga wata yar yaloluwar riga mai hannu daya, Ta dambara jan baki akan la66anta har saman kumatuntu, mascara din data sanyawa eye lashes dinta ya zazzago har kasan idanunta, babu wanda bai firgita da ganin ta ba, Jami'an sai faman kunshe dariya suke yi a bakunansu, ko mayafi babu akanta sai wannan guntun gashin kan nata mai ɗan yawa data fake shi da ribbom Ya karkarce gefe ɗaya.
Ko ta kansu bata bi, Tana isa bakin motar, ta jefa takalmanta cikin car window, kafin ta daddage ta kama glass din Ta zura kanta aciki ta soma kiciniyar kutsawa ta karfi, dafe kai salsabeel yay da hannu ɗaya tamkar zai fashe da kuka, ya ma rasa me zaiyi, su rubina duk sun bude bakunansu asake suna kallon ta.
A hanzarce Ya cafko kafafuwanta, Ya zarota daga tagar, tana ta faman haki ta dube shi idanuwan nan nata kamar na babie sai kyaf kyafta su takeyi
_"Ya salsabeel baka ce nayi kyau ba" Cikin sanyi murya yace"kyawun ne ya ruɗe ni shiyasa nakasa magana" ya fada tare da bude mata murfin motar, ta shiga ciki ta zauna, Bayan kowan nan su Ya shiga, A jere suka fuce daga gidan kai tsaye suka haura kan titi_
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*
Mu Haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya
*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MAY LIKE THESE POSTS
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
SUBSCRIBE USNovels Elite
Home
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 19 Complete
by
Novels Elite Admin
June 15, 2024
Novels Elite English
_*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_
سجن القد💋🔥💞
~Takun Ƙarshe🔥~
Dedicated to Aunty Kubra💋💞
قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘
An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘
Daga alƙalamin Boss Bature💋✊
____________________________________✍️
ANEELERH
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga dakin abie, yana daga zaune gefen gadon shi sanye da farar jallabiya, idanunsa a manne da farin glass, yayin da hannun shi ke a ruƙe da kur'anin da yake karantawa, sai da yakai aya kafin ya ɗan ɗago yana dubanta tare da amsa mata sallamar da ta yi
A tsanake ta shiga ta zauna daga kasan gadon kusa da kafafuwan shi, cikin girmamawa ta gaishe da shi
Fuskar shi dauke da murnushi yace"oum junaid, kin tashi lafiya" sunnar da kanta kasa tayi fuskarta da murmushi tace"lafiyalou abie"
"Ina jikallan nawa? Maimakon ki tafo min da shi? ko dai rowar ɗan za'ay min ne" cike da jin kunyarshi tace"a'a abie, ni na isa in hana ka jikanka"
Murmushi yayi kafin ya Miƙa hannu ya ɗauko wayarsa dake ajiye kan side drawer ya miƙa mata
"Kar6i nan, Ki duba sakon da aka turo miki" da sauri ta sanya hannu ta kar6a, kafin ta ɗaura idanunta kan screen ta soma karanta sakon
_Assalamu Alaikum, barka da rana abie an wuni lafiya, ya iyali, ƙawar Aneelerh ce benazir matar tajudeen, Ina son yin magana da ita sai dai bani da contact dinta, dan Allah a hadani da ita, nagode sosai, ku huta lafiya__
Lokacin da ta kai ƙarshen Sakon Idanunta azare, baki a buɗe da tsantsar mamaki take kallon screen din wayar, sam takasa gasgata abun da aka rubuta mata, Muryarta ƙasa ƙasa take maimaita sunan Benazir Benazir!
Abie dake ta kallon ta, ganin tayi kasaƙe babu alamun zata motsa ne yasa shi yin gyran murya, kamar wadda aka zungura da sanda a ɗan firgice ta dube shi tana faman zare idanu
"Lafiya? Ko bakisan ta ba ne"?
Muryarta a harmutse tace"abie, na kasa yarda ne da abun da gani, wannan sakon da aka turo min daga benazir ne aminiyar nan tawa, matar da yau tsawon shekara goma sha wani abu da 6atan ta...." kafin ta ƙare maganar abie yace"kina nufin Benazir yar gidan Alhaji ubaid? Wannan ƙawar taki ta ƙuruciya" jinjina mashi kai tai alamar eh.
"To ki kira layinta mana sai ki ji idan itace da gaske" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta miƙe ta fuce daga ɗakin a falo ta tsaya kafin ta danna call, jikin ta har kerma yakeyi tsabar zumudin taji idan banezir ce take neman ta. ......
*DAULAR ALHAJI MUSA*
Gaba ɗayan su sun Hallara a kan dining chairs, Tani da lami ne suke dawainiyar yin serving din su, an shake masu table da lafiyayyan abincin breakfast.
Tun da suka zauna babu mai magana acikin su, zeenatu da benazir abayane a jikin su, sun daure kansu da head scarp, yayin da Hajiya sarah ta sanya fitted gown ta atampa, kayan sun bi shape din jikinta, sam babu ɗankwali akanta sai zallar gashin kanta da ya sauko har kan kafadarta, mom layla ma atampar ce ta sanya, Alhaji Ubaid da shureim jallabiya ne a jikin su, Alhaji musa ne kadai ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda launin blue sky, kayan sun zauna mashi abunka ga namijin duniya, yayi kyau sai dai babu annuri akan fuskarshi kamar kullum Ya haɗe rai kai kace bai ta6a murmushi ba, tsabar yadda ya ɗaure fuskarshi yana faman shan kamshi kamar wanda iska ke yi ma wari.
Abinci yake ci kamar baisan tauna shi, hajiya layla dake kallon shi ji take kamar ta shaƙe shi saboda haushin shi da take ji.
Dr shureim dake cin abinci a tsanake ranshi ne ya bashi cewar Ana kallon shi a hankali ya dago da idanunsa kai tsaye suka shiga cikin na zeenatu, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido ɗaya, da ɗan mamaki akan fuskarshi Ya zaro mata ido da sauri ta sunnar dakai kasa tana cigaba da sakin murmushi, girgiza kanshi yayi kafin ya maida hankalinsa akan abunda Yake yi.
Gaba ɗaya Hankalin benazir baya atare da su, ta tasa plate din abinci agaba ta kasa ci saboda tunanin Yarinyar da ta kira ta a daren shekaran jira, tun washe garin jiya take ta kiran layin baya shiga hankalin ta yaƙi kwanciya.
"Benazir Lafiyar ki kuwa? ko wani abu na damunki ne? Tun dazu na lura dake kin kasa cin komai" cikin kulawa mom sarah tayi mata magana.
Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace"ba abunda ke damuna mommy, lafiyana qalou"
"Okey, ki fara cin abincin kada ya huce, ba lallai yai maki dadi ba"
Amsa mata tayi da toh
Spoon ta ɗauka ta soma cin abincin zuciyarta cike fal da tunanin Unaisah
Wayar dr shureim ce ta soma ringing daga cikin aljihunsa, Hannu ya zura ya curo ta yana duban me kiran nasa.
"Ka tsaya ka kammala cin abincin, Inya so daga baya sai ka yi picking call din"
Muryar Alhaji ubaid ce ta katse masa hanzarinta.
"Daddy, kira ne mai mahimmanci,"
"Shikenan je ka daga" mikewa yai a hanzarce yabar dining din
Tafiyarsa keda wuya Hajiya layla ta dubi Alhaji Ubaida dake a zaune gefenta tace"ya maganar da mukayi dakai jiya"?
Murmushi yadan saki Yana duban fuskar Alhaji musa Yace"ay na fada maki, Ki ƙara hakuri"
girgiza kai tayi"bazai yiwu ba, ni bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba! Wannan ay abun kunyane ace muna zaune gidan kaninka....." maganar na dira kan kunnan Alhaji Musa Ya ajiye spoon din hannunsa, fuskarsa a murtuƙe Ya ke duban Hajiya layla, yasan tayi maganar ne don Yaji ta.
Gaba daya hankulansu mom sarah ya dawo kanta.
"dan Allah ki yi shiru ya isa haka! Muje ɗaki mu yi magana" galla masa harara tayi"wallahi babu inda zanje, ko na bika bai wuci ka bani hakuri ba, Ni nagaji da zama acikin gidan nan, gaba ɗaya a takure nake, Kai ko gudun surutun mutane ba ka yi? tsawon kwanaki kana zaune agidan kaninka tare da Iyalinka"?
Hankali atashe mom sarah tace"dan Allah kiyi hakuri, mu kammala cin abincin sai muyi magana...." kafin ta ƙare maganar Alhaji musa Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tuni taja baki tayi shiru.
Jikin zeenatu harya fara yin kerma saboda batason tashin hankali arayuwarta, abun kaɗan ke rikitata, ita dai benazir ba ta ce komai ba ta zuba ido tana kallom mommyn nasu dake ta faman tada jijiyoyin wuya.
A gadarance Alhaji Musa Yace"Bana son haniya"
Harara ta watsa mashi"ay idan baka fita harkar mijina ba, hayaniya yanzu ka fara jin ta, wallahi bakaso zaman lafiya ba, akan me zaka dinga juya mutane son ranka sai kace wasu bayin ka, komai sai dai ka bada umarni abi, to wlh bazan lamunta ba! Hakuri na Ya ƙare, idan shi ka rufe masa baki to ni baka isa kayi galaba akaina ba!" ta fada tare dakai hannu ta bugi gaban table da karfi, kafin ta yunkura ta mike tare da kallon Alhaji ubaid.
"Ni zan tafi, tun da naga kai baka da niyar barin gidan," mayar da dubanta tayi ga benazir"tashi mu tafi" jiki asanyaye benazir ta miƙe, nan take zeenatu ta fashe da kuka tana fadin"Inna lillahi mom layla dan Allah kada ku tafi, wallahi banso, mommy kada ki bari su tafi, daddy kace masu su su yi haƙuri su zauna, ko kuma su tafi da ni" Hankalin Tani dana lami ba karamin tashi yayi ba, ganin rikicin dake shirin 6allewa.
Wani irin tausayin ta ne ya kama benazir sam batason ta rabu da yarinyar sai dai ba yadda zatai dole tabi umarnin mahaifiyarta.
Da sauri Alhaji Ubaid Ya mike muryarshi da 6acin rai Yace"haba layla menene haka? Yanzu abun ki kai kin kyauta? Mutane suna zaman su lafiya kin tarwatsa masu farin cikin su"
Dakatar da shi Alhaji musa yai, Cike da isa Ya mike tare da kallon fuskar Hajiya layla dake huci.