← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 238

Sashe 234

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa..

"Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..."

Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin.

Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi.

Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...."

Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma.

Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!'

Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta.

Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?"

Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!"

Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..."

Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?"

"Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..."

Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru.

Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.."

Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya.

Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe.

Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita.

Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!"

Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa..

Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."!

Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita..

Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!"

Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla.

Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya ɗauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ƙaryar na mutu bayan ina a raye...."

Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ƙwaƙwalwarsu ke ƙoƙarin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki.

Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya jiƙe sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi.

Pretending ya yi duk don ya ƙara dagula masu lissafin ƙwaƙwalwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!"

Ya faɗa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce.

"Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..."

Ta faɗa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruɗani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu ɗaya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ƙwayar idanun ta.

In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faɗa yana girgiza kansa.

Bai ƙare maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruɗani! gaba daya mun ruɗe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faɗa fuskarsa sharkaf da hawaye.

Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi.

"Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ƙaryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..."

La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! Ƙarya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faɗa yana nunata da yatsansa dake kerma..

"Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ruƙiya zaku tabbatar da abunda nake faɗa maku..."

Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ƙululun bakin ciki da ya tokare maƙogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiɗani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasiƙi ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...."

bata ƙare maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruɗar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu ɗauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu.

Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ƙame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa.

Damƙar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faɗin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haɗa uba da yayansa, ni nasan maƙiya ne suka turo ki don ki yi mini ƙazafi..."

Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata ɗauki.

"A'uzu billahi minasshaiɗanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma baƙar munahika"

Ya faɗa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu.

Tana kuka haɗi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana miƙa masu hannu,

"Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ƙara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaɗai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla, tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta daga mugun ruƙon da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita.
Chapter 234 · 0% Book details