Sashe 20
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe idanu prime minister yayi a hankali batare daya buɗe su ba, shi kanshi baiso yanayin damuwar da yake a ciki ya bayyana ba, ko dan saboda al'ummar da suka taru domin shi.
"Idan akwai abun da kake buƙata ka faɗa mana muyi maka shi," acewar his excellency deen ya fada cikin nuna damuwarshi.
Daƙyar ya bude idanunshi wadanda suka kaɗa jawur da su
Muryar shi ƙasa ƙasa ya furta"lafiyata lou, dan Allah ku kwantar da hankalin ku, kada halin da nake a ciki Ya dame ku"
"Taya zamu iya kwantar da hankalin mu bayan kana a cikin damuwa? pls kayi kokari ka danne zuciyarka ko mun samu a kammala taron nan lafiya, duba fa ka gani gaba ɗaya mun taru ne saboda kai" fuskar Abdul razak A yamutse yayi maganar.
Sai lokacin Hajiya malikat dake a hakimce gefen su tayi ma Gimbiya mujeedat raɗa a kunnanta"ki ja shi ku ke6e ki ji meke damun shi, saboda ke kadaice zaki iya shawo kan shi"
Gimbiya mujeedat taji dadin shawarar malikat.
Duban ƴan uwan nashi tayi"idan ba damuwa inason zanyi magana da shi"
Ta faɗa tare da miƙewa ta ruƙo hannun Prime minister, da sauri jami'an sirrin dake a cikin filin suna shawagi suka take masu baya don basu tsaro, wata corridor suka nufa an ƙawata ko'ina na wurin abakin ƙofar shiga ɗaya daga cikin resting rooms din dakin taron jami'an suka dakata abakin kofar su kuma suka shiga daga ciki.
Duk abun da ke faruwa akan idon chief Owais, ya riga dayasan meke damun uncle din nashi, shi kanshi zuciyarshi ta karaya,
"Babban mutum me kake tunanine"? Muryar Justice ce ta katse mashi zancen zucin nashi
"Tun da muka zauna na lura baka fara'a meke damun ka ne"?
Yamutsa fuska chief owais yayi"bakomai"
"Ko ruwa baka sha ba, Kuma nasan kana Jin yunwa"
Ya fada tare da janyo glass mai ɗauke da juice Ya tura mashi agabanshi, Ya haɗo mashi da suya,
Ba dan yana jin yunwa ba, ya ɗauki glass din ya kur6i lemun wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar shi
"Zaki gafa mutuniyar ka," ɗagowa zaki yayi tare da kallon direction din da justice ya ke nuna mashi, hajiya laurat ya hango.
"ita kaɗai ce makullin da zata buɗe maka kofar haɗuwa da pretty ɗin ka" murmushin gefen fuska ya saki.
"Kana ganin zatayi mana hanya? Ni fa ban ta6a kula ta ba, ko magana bata haɗani da ita"
Cike da kwarin gwiwa Captain Yaseer dake a gefen shi yace"ay dolen ta ne tayi mana abun da muke so,"
"Kwara dai mubi ta lalama, don wlh matarcan da kake gani ba karamar kwaruwa bace, ƙanwar fa Alhaji musa wadata, hmmm baka san shi bane, wlh mutumin nan ba karamin jan wuya bane" acewar justice
Ta6e baki Yaseer yayi"ni ina ruwana da wani alhaji musa, ina magana akan kanwarsa ne,"
"Da yaushe ne zaku yi magana da ita? In ba damuwa ku bani dama ni na tunkareta bayan an gama dinner din" acewar ziyad
"Ni nasan ta yarda zanyi mata magana"
Captain yace"ay dama kai zaka fi iyawa da ita, don wlh ta ce zatayi min ji dakai, tsaf zan dauke ƴar mutane da mari abainar jama'a" gaba ɗaya suka sanya dariya banda chief wanda hankalin shi ba akansu yake ba
"Wlh da kuwa ka kare rayuwarka a gidan kurkukun ƙaddara, don kuwa ta6a matar can ba abune mai sauƙi ba, kai ko shi daddy sharafuddeen ba iyawa zaiyi da itaba, saboda mugun jin kaine dasu ga tarin dukiya da Allah yayi masu" justice ne ya faɗa
Ta6e baki yaseer yayi ba tare daya ƙara furta kalma ba
Idan muka koma 6angaren Hajiya turai, dake atsaye kamar wadda tarasa galihu fargaba Ya hana ta tunkari su Hajiya laurat, baiwar Allah tayi tsaye ita kadai, Sai faman yan waige waige take yi tana neman jazz tasan shi kadai ne zai share mata hawayen ta
Kamar daga sama taji anyi hugging ɗinta ta baya, lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya jin sautin dariyar Hajjaty da sauri ta juyo suka fuskanci juna, tun shigowarta Alhazawan nan Na canada suke bin ta da kallo, musamman abokin baba obie dama yajima da dakon soyayyarta a zuciyarsa.
Ita kaɗai ce a filin taron ta sanya Sari na indiyawa, launin red colour, masu ƙyalƙyali, fuskarnan tasha over make up, ga wasu highhills ƴan uban su dake a kafarta, hannunta ɗaya ruƙe da ƴar purse dinta
Wani irin farin cikine ya lullu6e mom turai har batasan sa'adda ta kara huggin dinta ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"I'm glad to see you hajjaty, kinga yadda ki ka yi kyau?" ta faɗa tare da dago da kanta tana kallon ta
Su hajiya muhibbat dake kallonsu ransu ya 6aci sai faman buga tsoki suke yi, sunji haushin zuwan hajjaty ɗakin taron saboda yadda taja hankulan dattawan dake awurin, har takaiga sun rasa sukunin su
Ruƙo hannun juna sukayi sai faman sakin mirmushi takeyi kamar wadda akayiwa Albishir da gidan Aljanna
"Me kike yi atsaye ke kadai? Sannan naga idanuwan ki sun ciko da kwalla fada min meya faru" cikin kulawa hajjaty keyi mata magana
Cikin sanyin murya tace"bakomai, kawai banjin dadin zama nikadai," nan take hajjaty ta fahimci abunda ke damunta
Bin ɗakin taron tayi da kallo karaf idanunta suka sauka kansu Her excellency muhibbat
Wani irin mugun kallon harara suke jifarsu dashi.
Ko ta kansu hajjaty bata bi ba, ta ruƙo hannun Mom turai suka samu wuri kan kujeru suka zauna suna ƙara gaisawa, pravin ne yayi magana da masu raba abinci suka kawo masu shaƙe da table, sai rawar kai yakeyi akan hajjaty don yaga hajiya saratu bata a hall din, ƙarfin hali hada zama wurin su.
"Lallai mutumin can, wato don yaga hajiya saratu batanan shine ya zauna yana goga kafaɗa da waccan kilakin" rai a6ace laurat tayi maganar
Muhibbat tace"zata ci ubanta ne wlh, ni dama tun fil azal na tsani matar can, ay tun farko kuskuran da hajiya saratu tayi na auran dangin masu bautar shanu ta kawo su cikin family dinta, wlh mutanan can basu da amana, sun iya munafunci da kisisina, ga kwaɗayin abun duniya, nidai fatana Allah yasa bada wata muguwar manufar suke zaune a family din nan ba"
Guntun tsoki her excellency Jamila taja tace"takaici ma ya hana inyi magana, dalla jibi yadda ta ca6a ado ko kyau babu, mace kamar Aljanna, ita ala dole sai ta fi mu haɗuwa, kowa ya sanya abaya sai ita isassa mai walkin sa taje ta sanya sari, su kuma wadancan dattawan dake ta satar kallon ta bansan uban me suka gani a jikin ta ba.
Hajiya madina na dariya tace"ba dole su kalle taba, mace tana tafiya mazaunai suna jujjuyawa kamar an jera marmarar sakwara" dariya suka saki gaba ɗayan su.
Adai dai lokacin Hajiya saratu ta shigo hall din hannunta ruƙe dana zahra, nan fa hankali ya dawo kansu, zarah duk tasha jinin jikinta ganin zaratan samari da ƴan mata maƙil da hall din, duk da itama ba abaya ba, abaya din dake a jikinta irin na can ƙasan closet ne wadanda ake ji dasu ta dauko ta sanya launin skin pink, ta yi rolling veil akanta ga glass data manna, duk tabi ta ruɗe ganin yadda wasu ke kallonta, bakomai ne yasa suke kallon nata ba face ganin fuskar bare, koda shigowarsu pravin yayi saurin mikewa daga teburin su hajjaty gudun kada Hajiya saratu ta gan shi, lalla6awa yayi ya koma wurin su baba obie ya zauna.
Sai da ta fara zuwa da zahra wurin su hajiya laurat ta gaishe su cikin girmamawa, da fara'a suka amsa mata taci albarkaci Hajiya saratu da kuwa ko kallo bata ishe su ba
"Wacece wannan ko itace surukar taki"? Hajiya jamila ce ta tambaya
Murmushi hajiya saratu tasaki hannunta ɗaya dafe da shoulder din zahra tace"kwarai kuwa, to Ya kuka gan ta"?
"Masha Allah, kyakkyawa da ita son kowa kin wanda ya rasa, malama zahra sannu da zuwa" muryarta ƙasa ƙasa ta amsa masu.
Jan hannunta hajiya saratu tayi"mu shiga ciki" tafiya su ka yi cikin hall din sai faman yan waige waige zahra ta ke yi, fargabanta bata san inda hajiya saratu zata kaita ba.
Su twins ta hango kowan nan su ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya kan kujeru, tare da Dr Nawaz, wurin su hajiya saratu ta nufa da zahara wadda tuni gabanta ya soma dakan uku uku, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ganin suna tunkararsu
"Barkan ku da hutawa" a tare suka dago suna kallon ta
"Mom..." zaid ne ya kira sunanta bai karasa ba yai tozali da zahra,
Kallo ɗaya zayn yai mata ya kau da idonshi yaci gaba da danna wayar hannun shi, har kwara dr nawaz da dan fara a face din shi
"Yawwa ajiya na kawo maku, zahra ki zauna a wurin su, dan Allah ku kula mun da ita" amsa mata zaid yai da toh tare da nuna ma zahra kujera"have a seat," jikinta na kerma kerma ta zauna duk tasha jinin jikinta, sam ba ta so hajiya saratu ta kawota cikin maza ba, Ina laifin wurin ƴan matasan matan family din duk da tasan ba lallai ta samu shiga a wurin su ba.
Cikin kulawa hajiya saratu tace"Idan kina buƙatar wani abu, ki faɗa masu zasu sa akawo maki, pls ki saki jikin ki, Idan aka kammala taron zanyi magana dake kafin ki tafi gida' amsa mata tayi da toh
Bayan tafiyar hajiya saratu, zaid Ya soma jan ta da fira.
"Kamar naso na gane ki" murmushi ta ɗanyi tare da cewa"ina ɗaya daga cikin interior designers din da suka yi aiki lokacin birthday din ku dana baba obie"
"Oh yes, I remember now, What's your name"?
"Zahra"
"You look absolutely beautiful today" still face din ta da murnushi tace"thank u"
Dr nawaz ya dube ta daga ƙasa har sama farat ɗaya ya gane ba ƴar masu kuɗi bace sai dai akwai kyau ko dan saboda wannan zai ɗan daraja ta.
"Bimillah malama zahra" ya fada tare da miƙa mata glass na ruwa me sanyi