← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 238

Sashe 6

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waro idanu waje natasha tayi da mamaki ta furta kina nufin Big Boss? Ya ziyarce ki? Ɗaga mata gira ummi tayi alamar eh.

"Amma ya akai ya iya shigowa gidan Jami'an Isod, bayan kin faɗamin acikin sharuddan da suka baki, babu shige babu fuce basu buƙatar wani naki yazo inda kike, har zuwa lokacin da kika kammala Yi masu aikin su" ta faɗa a kagare da son jin ƙarashen xancen.

Dariyar shaƙiyancin Ummi tasaki tamkar babu damuwa aranta"kinsan mutumin na dabanne, ni kaina bansan tayaya akai ya shigo gidan ba, Har tambayarshi nayi sai yace min idan na yarda dashi indaina tambayarsa.... " dariya natasha tayi cike da nishaɗi tace"Namijin Duniya, Nayi kewarshi ummi, kullum cikin begen ganinsa nake yi, yayi min nisa yanzu, ba kamar lokacin da nake yi mashi rainon babynsa Pretty ba, tun da Ya kar6i Yarinyar sai nayi dagaske nake ganin shi, ko wayana baya picking... " kafin Natasha ta ƙare maganar Ummi tayi hanzarin tarar numfashinta da cewa"wai ina yarinyar take ne? Na jima ina son na tambayeki ita, nayi missing dinta, tun ranar dana fara Yin tozali da ita naji kaunarta ta shiga raina, duk da bata jin magana amma tana da kyau"

Natasha tace"hmmm, Ummi Ya raba ni da ita, tsawon watanni, duk idan na tambayeshi ina baby Pretty na sai yace min ya mayar da ita wurin mamanta, har alfarma na nema awurin shi akan ya amince min inbiyo shi nigeria saboda ina son ganinta amma Ya hanani.... "muryarta na rawa ta ƙare maganar idanunta sun cicciko tab da kwalla.

"Ummi Inason yarinyar nan, Ina ƙaunarta, nayi fatan ace ni na haifeta ko dan saboda mu kasance atare har abada, mun shaƙu da juna, na saba da ita, Amma yayi min yankan ƙauna.... " tunda tafara magana ummi ta natsu tana kallon fuskar Natasha ta cikin screen din laptop tamkar suna awuri ɗaya.

"Ummi nasan zaki Iya taimaka mani, tunda Yana kaunarki, Yasha fadamin ke kadaice kike Iya sarrafashi son ranki, please kiyi amfani da damar da kika da ita, Ki lalla6a shi Ya dawo min da baby pretty" cikin sanyin Murya ta ƙare maganar, Ummi dake kallonta tuni tausayinta Ya kamata, bata ta6a ganin Natasha tana zubar da kwallarta akan wani ɗan adam ba sai akan babyn da take mutuwar so, tasan da irin kaunar da take yima yarinyar a lokacin baya.

Cikin kwantar da murya ummi ta furta"Am sorry, Kinsan bana son ganin hawayenki, zan Iya yin komai akanki, saboda halaccin ki agare ni, Kin wuce ƙawa a wurina sai dai ƴar uwa, saboda kin kaunace ni a lokacin da kowa yake guduna, abun da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, zanyi kokarin ganin na shawo kanshi don ya dawo maki da babyn ki"

Murmushin farin ciki natasha tasaki tana fadin"thank u ummi, nasan zaki iya yin komai saboda farin cikina, shiyasa nake ƙara kaunarki, ina nan ina shirye shiryen zuwa Nigeria saboda ke"

Martanin murmushin ummi ta mayar mata,

"Ina handsome boy din nan, namanta ban tambaye ki shi ba"

"Bashi da lafiya, Yana a kwance"

Yamutsa fuska Natasha tayi"najiye mashi ba dadi, Allah Ya bashi lafiya, har yau ban manta da fuskar shi ba"

Murmushi Ummi tayi mata" dama ke ay bakya mantawa da abu mai kyau, naga kin kirani da layinki Na england, hakan na nufin kin koma gidanki"?

Ɗaga mata gira tayi alamar eh. Jinjina kai ummi tayi, shiru sukayi na wani lokaci yayin da suke kallon juna batare da ƙyaftawa ba.

"Kin tsareni da ido Kina kallona, Kamar akwai wani abu da kikeson fadamin" acewar natasha ta faɗa tana ɗage mata gira.

Dariya Ummi tayi, Harta Buɗe baki da niyar furta magana, Sautin knocking ƙofar da akayine Yasa ta fasa yi mata maganar,

"Zan Kiraki Anjima Ki kula min da kan ki"

"Bangaji da jin muryarki ba ummi, amma shikenan zan jira zuwa anjiman inma kin manta baki kirani ba, Ni zan Kira ki, ki kula min da kanki and pls ki daina sanya damuwa aranki" a hankali ummi ta furta mata"toh, nagode da kulawarki agare ni" bayan sunyi sallama, Ta kashe video Call din, ta sauko tare da laptop din a hannunta, ta nufi desk ta ɗaurata, kafin ta shiga wurin closet dinta, mayafi ta daura akanta.

ɗaga Murya ta yi Wanene"?

Daga waje tajiyo Muryar Batool Tana fadin"aunty Ummi ni ce" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta jin muryar Batool.

"Ki shigo daga ciki," turo ƙofar batool tayi tare da shigowa ciki, tana bin dakin da kallo kafin ta ɗaura idanunta akan fuskar Ummi, Murmushi suka sakarma juna

"Nayi fushi Batool, sai yanzu zaki tuna dani? Nayi tsammanin kece mutun na farko da zaki zo gare ni idan kika ji shiru ban fito ba, amma sai naji shiru babu ke babu unaisah" tafaɗa tana haɗe mata fuska alamar ranta Ya 6aci.

"Aunty ummi am sorry, Kina araina, tun ɗazu nake taso in shigo wurin ki'

Miƙa mata hannu Ummi tayi da sauri Batool ta ƙarasa gabanta tare da faɗawa kan chest dinta, sosai Ummi tai hugging dinta.

"Nayi missing dinki My babe, kun barni a daki ni kaɗai inata kewarku, Ina unaisah ne"! Ta faɗa batare data raba jikinta daga na batool ba.

"Nima bansan inda take ba, ɗazu muka rabu"

"Okey,ina fata kina lafiya, " ɗago dakai Batool tayi"Lafiyata lou, amma ke kamar baki da lafiya"

Shafa gefen fuskarta ummi tayi"bana jin dadi, amma kada hakan Ya dame ki, ganinki da nayi ya faranta raina" ta ƙare maganar tare da ruƙo mayafin Pakistan din batool"kayan sunyi maki kyau sai naga kinyi min kama da wata Old friend ɗina da muka rabu da dadaɗewa, kamar ita ta haifeki, Itama doguwace fara, Mom dinta balarabiya ce"

Murmushi batool tayi"amma ni da Unaisah nake kama"

Girgiza kai Ummi tayi"No, baki kama da Unaisah kun dai yi yanayi da ita"

Kwa6e fuska Batool tayi saboda ita tafison ace tana kama da Unaisah, ummi ta fahimci hakan sai tayi saurin cewa"wasa nake maki, dama don in ga reaction dinki ne, gaskiya kuna kama da ita sosaima kamar twins" jin hakan yasa batool sakin dariyar farin ciki, ummi dake kallonta batayi mamakin hakan ba ta riga data fahimci tsantsar ƙaunar da suke ma junansu.

"Mu zauna ki tayani fira, Ko baki gaji da tsayuwa bane"

"Aunty ummi, nasan kina jin yunwa, ki tafo muje falo zan sama maki abunda zaki ci" wani irin kallon ƙauna ummi keyi mata ba ƙaramin dadi take ji ba idan Batool ta nuna damuwa akanta.

Ruƙo hannunta ummi tayi acikin nata atare suka fito daga dakin.

Sautin Muryoyinsu Naufal ne Yajawo Hankalin Ummi Ga kallon su, tun Dazu suna a falo, Tare da Boss Man, Sun tasa shi gaba sai surutu suke zuba mashi.

Jin takun Takalmansu Yasa su dagowa suka kalli su Ummi dake saukowa down stairs, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta Aunty Ummi.

Saukowa Jamimah da azeeza su ka yi daga kan sofan da suke zaune, da gudu suka nufe ta, Hannah da Parveen ma suke miƙe suka nufe, wani irin daɗi taji aranta,

Ɗaya bayan ɗaya ta soma rungumarsu a jikinta,

"Aunty Ummi, Yanzu kika tashi daga bacci"? Azeeza ce tayi mata tambayar

Girgiza mata kai tayi alamar a'a

Parveen tace"Ko dai baki lafiya" Harara Ummi ta jefa ma Parveen tare da cewa"kun damu dani ne? Meyasa ba ku zo bedroom ɗina kun duba ni ba? Shiru sukayi sai jamimah ce tai kokarin cewa"mantawa mu ka yi" Jan kumatunta Ummi tayi da hannu"Aku sarkin ɗumi, Na riga da nage baku kaunata, Shiyasa baku damu dani ba" ta faɗa haɗi da marairaice masu fuska,

"Wallahi aunty Ummi Muna ƙaunarki, kuma mun damu dake" Hannah ce tayi maganar

"Ni dai Inasonki aunty Ummi, kiyi hakuri idan mun 6ata maki rai," murmushi ummi tasakar ma Azeeza da tayi maganar.

Ruƙo hannunta Jemimah Tayi"Aunty ummi nima ina sonki"

"Naji na Yarda kuna sona, Yanzu mu shiga ciki," ta fada tare da Jan hannun Batool suka nufi ciki tare da su Hannah

Tunkafin Su ƙaraso, Boss man Yake Kallon Ummi, sam ya manta da ita.

"Barka da hutawa Yalla6ai, Fatan ka wuni Lafiya, Ya iyali"

A hankali Ya furta"Lafiyalou Ummi, Ina fata kema haka"? Ɗaga mashi gira tai alamar eh, ta faɗa tare da samun wuri saman Sofa ta zauna, suma sauran duk suka zauna.

hankalin Sajeed na akan screen din wayar Unaisah, Haris da javed suna zaune gefe da gefen shi tare da naufal sai kallon Game din da Yake bugawa suke yi, baijima da sauke shi akan wayar ba.

Gyaran Murya Ummi tayi masu atare suka dago suna kallon ta.

"Sannunku, ba hello ba Hi kun samu Waya kunata danna waya baku ita ne"

"Ta Unaisah ce," Acewar Sajeed

Da mamaki Ummi tace"Unaisah ke da waya iphone15pro? Amma ban ta6a ganinta ba"

"Dr Laurace ta bata Kyautarta, ɗaya daga cikin Likitocin da suka yi jinyarsu a america"

Boss man ne Ya bata amsa, Jinjina kai tayi.

"Ina ita Unaisah dinne"? Tayi tambayar tana kallon su

Boss Yace"Bansan meya tsayar da ita ba, tunɗazu da muka shigo tare da big guy Ya tafi da ita zai nuna mata kitchen din gidan nan ban ƙara ganin ta ba, ba mamaki ta tsaya taya masu aiki girkin dinner"

"Dan Allah ka nuna min kitchen din, Inaso In kar6o ma aunty Ummi abinci, Yunwa take ji" acewar Batool.

Murmushi boss man Yayi yana dubanta yace"kin damun da auntyn nan naki da alama, kada ki damu, bari na kira big guy awaya, idan suna a kitchen din zansa akawo mata abincin.... " kafin Ya ƙare maganar, Parveen tayi saurin cewa"Dan Allah Nima zanci" dariya sukayi gaba dayansu.

Ummi tace"foodie, Baki Gajiya da cin abinci, shiyasa kika fi sauran ƴan uwanki jiki"

Kwa6e fuska tai"ay bani kadai bace me cin abincin ba, Ki kalli kumatun jamimah sunyi manya manya da su" maganarta ta basu dariya.

Harara jemimah ta watsa mata"ay dai ban kaiki Cin abinci dayawa ba, Ni madara da bonbita nake sha, Sai dafaffan kwai da Fika fikin Kaza," boss dake kallonsu murmushine dauke akan fuskarshi, Firarsu ba karamin nishadi take sanya shi ba

Wayarshi Ya zaro daga aljihu Ya danna ma Big guy kira, Bugu uku Yayi Picking

Miƙewa yai da sauri Ya nufi cikin falon nesa da su ya tsaya saboda hayaniyarsu.
Chapter 6 · 0% Book details