Sashe 163
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da shaƙiyanci ta faɗa kafin ta sake ce ma giant ɗin,
"Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita ɗakin fiɗa ka tabbatar sun feɗe sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar.
"Bayan na kaita ɗakin fiɗar, ban ƙara komawa ba, saboda ba hurumina bane"
Bata tsaya taji ƙarshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya.
bata nufi ko'ina ba sai dakin fiɗa, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici ɗin dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta.
Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta.
Wani irin ƙululun baƙin ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani hayaƙin huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa..
A matuƙar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya ɗauke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo.
da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta.
_"Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunƙurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_
waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi
_bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata.
Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta faɗo dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta damƙi wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke faɗa mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell!
cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta ƙarasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta ɗauka gurin yin jinyarta ba, har ɗinki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji.
Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu.
Kamar zasu yi dambe ita da Khala, saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da ƙarfi kamar doki, da ƙyar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa ɗagowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin ɗan uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas.
Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar ƙarama dake sai baƙar zuciya kamar ta kafuran farko! Dame kike taƙama ne? Ina karfin naki yake uhm!"? Nishi ta dinga yi tana huci kamar zata iya ta6uka wani abu.
Sassauta murya Khala tayi, "Ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, kasancewata a gidan kurkukun ƙaddara, ba hakan yana nufin nima muguwa bace, kamar yadda kika zata, kinyi min mummunar fahimta, amma nayi maki uziri saboda bakisan komai dangane dani ba..."
ta faɗa tana kallon idanun Gabriella da suka kaɗa jawur.
Numfasawa tayi kafin ta ɗaura da cewa, "Da ace ni muguwa ce da ban taimaki rayuwarki ba, nasan yanzu tunaninki ya dawo, dama abunda na ke gudu kenan saboda nasan za'a rina, yanzu da ban zo ɗakin nan ba da tuni kin jima da kashe kanki saboda ɗamsil basira, idan kina tunanin mutuwa mafita ce a gareki toh ki daina, shi jarumi ba'a san shi da karaya ba, kada ki zama raguwa ki zama jaruma mai iya tankwara zuciyarta me kuma burin ɗaukar fansar zaluncin da aka yi mata.
Tana jan nishi da ƙyar ta furta, "Who are you? Where did you find me? and Why did you help me?"
"Sanin wacece ni baida amfani, iya abunda zan iya sanar dake shi ne ba a haife ni a gidan kurkukun ƙaddara ba, bada son raina na kasance a cikin shi ba, ta karfi da yaji aka kawo ni nan, bazan iya misalta maki ƙunci da raɗaɗin da na ji a lokacin dana buɗe idanuna na tsinci kaina a gidan kurkukun nan ba, na ga musiba da bala'e da idanuna, abunda ban ta6a zaton ko a mafarki zanga makamancin shi ba, zuciyata a karye take saboda anci amanata an yaudare ni, bayan haka an nuna min fin karfi ba yadda na iya,...." idanunta ne suka ciko tab da kwalla.
"Kamar yadda kika so kashe kan ki, nima nasha yin yunkurin yin hakan amma idan na tuna menene makomata? Sai inji na gaza! Mutuwa bazata hana su cigaba da aikata fasadi ba, saboda su ɗin 6atattu ne in har bamu haɗa hannu mun kawo ƙarshen su ba, babu abunda zai canza na daga zaluncin da suke aiwatarwa, bayan haka babban abunda yasa nake so na rayu shi ne ya'yana inason na sake ganin su ko da da numfashina na ƙarshe ne".
muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, Gabriella dake sauraran khala, itama hawayene kan fuskarta, tana da wuyar sha'ani a rayuwarta bata yarda da mutane amma karo na farko ta yarda da tsohuwa Khala, maganarta ta karya mata zuciya.
A hankali ta zame tafinta daga kan Gabriella, hakan ya bata damar miƙewa ta zauna da ƙyar tana duban fuskar khala da tausayawa
"Ke ɗan uwan ki ɗaya ne, ni kuma jikokina da suka salwanta agidan kurkukun ƙaddara yawa ne da su, inaji ina gani ban iya tsinana masu komai ba saboda an nuna min fin ƙarfi...." fashewa ta yi da kuka kamar ƙaramar yarinya.
Itama Gabriella din kukan ta fashe da shi saboda tausayin khala da ya mamaye zuciyarta ashe ita bata ga komai ba tayi mamakin haƙuri da juriyar tsohuwar da har ta iya kai tsawon lokacin nan bata haɗiyi zuciya ta mutu ba.
"Yau kimanin shekara ashirin cuf, rabon da in shaƙi iskar duniya saita gidan kurkukun ƙaddara, bani da burin da ya wace in tona masu asiri, kullum ne sai na roƙi Allah dare da rana ba fashi, duk da har yanzu ba wani sauyi, ban ta6a gajiyawa ba, saboda nasan Allah ne kadai zai iya cika min burina kuma yana sane dani, wani jinkirin Alkhairi ne kuma ina ji araina ƙarshen kurkukun nan ya zo" ta faɗa tana jan magina.
"Kin tambayeni Ina na tsinto ki?" A ranar bayan na fito daga fadar Elder naji ina sha'awar in kewaya kurkukun duk da bana so nayi tozali da abunda zai hanani kwanciyar hankali, har zan gifta na hango tsohuwa inno tare da giant din da ya ɗauko ki babu sutura a jikin ki raina ya 6aci ba kaɗan ba, nayi zaton ma kin mutu ne, kwatsam idanuna suka hango min yatsun ƙafarki na motsi, wani iko na Allah ni da bana shiga huruminsu bansan ya akai zuciyata ta azalzala min akan in taimaka maki ba, cikin sanɗa na bi bayan su, har suka aje ki a ɗakin fiɗa, tafiyar su ke da wuya, nayi 6adda kama ta hanyar amfani da sihiri na, na shiga cikin Gigantes Medici din batare da sanin su ba saboda hankalinsu ya karkata akan aikin fidar da sukeyi, kafin su zo kanki cikin abunda bai fi daƙiƙa talatin ba, na sace ki na kawoki ɗakina, na fara kokarin tsayar da bleeding din da kike yi kafin na dinke raunukan jikin ki...." tiryan tiryan khala ta zayyana mata komai, wani irin son tsohuwar ne ya kamata har batasan sa'ar da ta faɗa kan kirjinta ba, ta rungumeta cikin shesshekar ta furta, "Ki yi haƙuri nayi maki mummunar fahimta, ki yafe min"
Ɗan murmushi khala tayi kafin ta daura da cewa, "Tun kafin ki dawo hayyacinki na ji kina ambaton sunan ɗan uwanki Gabriel, na kwallafa rai a kan son sanin wanene shi? a cikin bookshelve ɗina ina da littafin register na fursinoni (Sijil al-sujna) a cikin littafin na buɗo ina bincikawa don inga wanene me suna Gabriel, ban sha wahala ba, saboda nayi nazari na gane cewa ku ɗin ba tsoffin prisoners bane cikin waɗanda aka kawo ne a ƙarshen shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, cikin sa'a na ga sunayen ku, a fahimtana ɗan uwanki ne ko?..." cikin sanyin murya tace, "twin brother ɗina ne."