← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 238

Sashe 197

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin mugunta hajiya saratu ta saki da alama ta manta da abunda hajiya laura ta fada mata"Idan kin koma ɗaki, Ki cire sareen nan, Yau nafi son naganki cikin uniform na ma'aikatan gidan nan fatan kin fahimce ni" jinjina mata kai tay"Toh"
"Yawwa zaki iya tafiya" har zata juya ta kuma kiranta
Da yatsa ta nuna tray din hannunta"meye a ciki"?
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"dambun nama ne"
"Samun wuri, Wato ke har kin riga masu gidan dandana girki ko? Ta fada tare da kai hannu ta buɗe plate din Ta duma hannu ta dibi dambun naman ta tura abaki tana tauna, bakinta a cunkushe tace"kafin in dawo kisa a shirya min Lunch dina, komai da aka dafa za'a zuba min.." ta fada tare da kara dumbuzar dambun naman ta tura abaki, kafin ta dauki Juice ta kur6a, duk hajjaty tana atsaye tana kallonta.

Tsoki taja"duk na bata hannuna da maiko ni da zanje airport tarbo mijina" cikin sanyin murya hajjaty tace"yakamata ki wanke" ta fada tare da nuna mata Sink din dake a kusa da in da suke.

harara ta galla mata"nifa komi zakiyi ba zaki taba burgeni ba.."

Ta fada tare da zaro hanky daga purse dinta ta mutsustsuke hannun dashi duk don kada hajjaty taji dadin ta bi shawarar ta, juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga falon.

Binta da kallo Hajjaty tayi har ta bace ma ganinta, murmushi ta saki ta danyi mamaki da ta ci abun hannunta musamman a kwanakin nan data lura kamar batason ko hanya su hada, tabbas ta bata mata rai amma har yau Allah bai sanya mata tsanarta ba, Ita dai tana so su dinga mutunci da juna.

Juyawa tayi jiki asanyaye ta nufi dakinta.

kaitsaye hajiya saratu ta nufi hamshakiyar motarta, a hanzarce Officern da zaiyi driving dinta yai hanzarin bude mata cardoor har ta zura kai zata shiga muryar Twins ta katse mata hanzarin ta"Mommy" gently ta juyo tare da kallonsu, yayin da suke fitowa daga Entry hall sun dauki wankan suit kamar a turai.

Murmushi ta sakar masu, Suna karasowa ta haɗa su duka tayi hugging dinsu gwanin ban sha'awa..

Bayan sun gaishe da ita ta amsa masu tare da cewa"my twins Ina zuwa haka? Yau dai ba aiki na sani ko za'a fita yawon bude ido ne" zaid yace"No, daddy ya fada mata time da jirginsu zai karaso shiyasa muka shirya don muje tarbo su"

"Kunyi tunani mai kyau, Nima yanzu haka airport din zanje, me zai hana mu shiga mota dina"

Bayan sun shiga suka sanyata tsakiya suna zaune a gefe da gefenta.

Sai da motarsu ta haura kan titi kafin ta dubi zayn"ya zahra? Two days ban tuntube ta ba, amma nasan kai kana waya da ita"

yamutsa fuska yai a dakile ya furta"may be tana lafiya" wani kallo ta wurga mashi"oh baka da tabbaci ma? Thats mean baka kiranta awaya"!

"No ba haka bane mommy, Kinsan yanayin aikina bakasafai nake samun lokacin yin waya ba" girgiza kai tay"banji dadi ba, yakamata kana bata kulawa zayn, nan bada jimawa ba zata zama matarka" daure fuska yai, zaid sai faman kunshe dariya yakeyi..

"Mommy hannunki kamshin nama yakeyi ko hancina ne" Ya fada tare da ruko hannunta Yakai saitin hancin shi yana shinshinawa.

"Kai Zayn Allah ya wadaran naka ya lalace, ka cika sa ido" ta fada tare da dago purse din hannunta, ta kwala mashi akai" dariya suka sanya gaba dayansu da alama dai suna acikin farin ciki.

__________Hajjaty___________

Bayan da ta dawo daki, zama tayi daga gefen gadonta, ta ajiye din akan table din gabanta, A tsanake ta fara cin dambun naman fuskarta dauke da murmushi wato abunda hajiya saratu tay yabata dariya, aranta ta ayyana in da ni muguwace kamar yadda kike fadi wlh da abinci kadai zan iya kashe ki saratu.

Wayarta ce ta soma ringing, tayi azan Pravin ne cike da zumudi ta janyo wayar daga kan pillow ganin ba pravin bane yasa murnar ta koma ciki amma taji dadi data ga kiran daga kayin marwa ne.

Picking call din tay tare da kara wayar a kunnnata.

"Ina wuni inna, ya jikin marwan"? Bata kare maganar ba, Muryar Marwa ta katse ta da cewa"Aunty Hajjaty Nice marwa dakai na"

Da mamaki ta furta"Wai dagaske Marwa kece? Allahu akhbar amma natayaki murna naji dadi da bakinki Ya bude Marwa Ya jikin naki"

"Da sauki, yatsun hannayena ma sun warke har abinci Ina ci dakaina" tsantsar farin ciki ne Ya cika hajjaty"Alhamdulillah Ya Allah mungode maka, Allah ya kara maki Lafiya marwa, Allah ya kara tsare ki daga sharrin Aljanu".

"Ameen aunty, nagode da kulawarki agare ni" shiru sukayi na dan wani lokaci kafin hajjaty tace"kinji kwana biyu ban kira na tambayi lafiyarki ba, wlh na shiga busy ne amma kina araina, bari na hada ki da su Abla ku gaisa" har ta yunkura zata mike Marwa tay saurin katse mata hanzarinta"Aunty akwai wani abu da nake son fada maki sirri ne" jin wannan maganar yasa hajjaty ta koma ta zauna ta nutsu tana sauraronta.

"Kiyi hakuri ki yafe min, Abunda ya faru dani hakkinki ne ke bibiyana, baki min komai ba, amma saboda kwadayin abun duniya na rufe ido na kar6i tayin aikin leken asiri da aka sani akanki" wani irin faduwar gaba hajjaty taji gaba daya tabi ta rude murya na rawa tace"ban.. bangane me kike nufi ba!"

Marwa bata boye mata komai ba ta sanar da ita zargin da hajiya saratu takeyi akanta da kuma aikin data bata don tayi mata leƙen asiri don ta gano me take kullawa.

"Marwa Dama kece kike tsoratar dani"?

Cikin shesshekar kuka marwa tace"wallahi nice, nayi danasani hajjaty, baki min laifin komai ba hasalima kin kaunace a lokacin da wasu ke kyamatata, da zuciya daya kikai jinyata, na dade banga mace mai kyakkyawar zuciya irinki ba, kina da hakuri ga son taimako...."

kasa karasa maganar tay saboda kukan daya kwace mata.

Zafafan hawayene suka wanke fuskar hajjaty tabbas hankalinta ya tashi da jin abun da hajiya saratu tasa ay mata ashe tsanar da tay mata har takai ta sa adinga bibiyarta? Laifin me tay mata?
Numfasawa tay kafin ta furta"marwa ki daina kuka, wlh na yafe maki, har ita hajiya saratun, Allah ya yafe mana baki daya, kuma naji dadi da kika gane kuskurenki"

Bayan Marwa ta tsagaitawa da yin kukan tace"bawai iya wannan ne abun da na kira in fada maki ba..."

A kagare hajjaty tace Ina sauraron ki marwa.

"Bansan ya zaki ɗauki abun ba, amma kiyi hakuri ban fada maki don in tada maki hankali ba face sai don In ceto rayuwarki saboda Kyautatamin da kika yi, Da farko nayi danasanin aikin da hajiya saratu ta sakani amma daga baya Naji dadi saboda silar aikin Allah ya nuna min wani mugun abu dake rayuwa agidan nan" Yawu hajjaty ta hadiya kutt zuciyarta cike fal da fargaba ta furta"marwa menene? Fada min dan Allah!

Numfasawa marwa tay kafin ta daura da cewa"Aunty PRAVIN shine silar ciwo na, Saboda Ya gano nice nake yi maku leken asiri shine Ya daura mini cutar kuturta Ya toshe min bakina"

bata kare maganar ba sakamakon tsawar da hajjaty ta daka mata"Ya isa marwa! Bana son karya ki rasa wa zaki wa kazafi sai pravin? Taya pravin zai iya daura maki ciwo? Sai kace dai Aljani"!

"Saboda shi din mugun matsafine, kece bakisan wanene Pravin ba, tun farkon fara aikina gidan nasan munanan dabi'unsa, Ya saba Bibiyar mu yana laluban jikinmu dayi mana barazana akan in muka tona masa asiri zaisa a koremu daga aiki....."

wani irin faduwar gaba hajjaty taji daram dararam kamar ana mata luguden ta6are a kirjinta, Jikinta sai kerma yake kaf kaf idanunta azazzare cike da tashin hankali wlh ji take kamar a farmaki sam takasa yarda da maganar marwa taya ma wai pravin dinta zay aikata hakan?

"Naji kin shiru, dama nasan ba lallai ki fahimce ni ba, amma ki sani wlh rantsuwar dan musulmi ba kazafi nayi masa ba, Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan"
Chapter 197 · 0% Book details