← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 238

Sashe 31

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sorry ban gabatar maka da kaina ba, Ni sunana Prime minister Hateem Obinna, kai fa"? Ya faɗa yana duban shi har lokacin danish bai daina jefa mashi kallon ba, babu alamun zai tanka mashi kamar akwai wani abu daya ja hankalin da yasa shi kallon nasa.

"Ka yi shiru baka ce komai ba," kamar kurma haka danish yayi mashi.

Dafe kai Hateem yayi muryarshi da kasala ya furta"please ka yi min magana, ba ka son yadda na ƙagu da son ganin ka samu lafiya ba, na damu da kai kamar yunwar ciki na, dan Allah ka saki jiki dani, kada ka azabtar dani da kaunar ka...." fuskar shi a yamutse yake yi mashi magana.

"Ina fata babu inda ke yi maka ciwo yanzu"? Ya jefa mashi tambayar, lumshe mashi idanu danish yayi alamar eh.

"Ya Ilahi, ba zaka yi min magana ba, sai dai ka yi min nuni da ido, ni bana so ka daure ka yi min magana, Inason jin muryarka ko hankalina ya kwanta, namanta ban faɗa maka ba, gobe da asuba zan bar ƙasar ba lallai mu sake haɗuwa ba, shiyasa nakeso ka bani haɗin kai mu more lokacin nan da muka samu...." cikin sanyin murya ya ƙare maganar.

Har lokacin kallonsa danish ya ke yi, abun ya ɗaure mashi kai, Ya rasa gane ma'anar kallon nan.

"Ko dai kana mamakin kamannina dakai ne"? shiru yayi mashi.

"Wayyo Allah na, to ko dai baka jin harshen hausa ne inyi maka da turanci ko larabci ko french wanne yare kafi ji a cikin wadannan"? A ƙagare da son jin amsar shi ya faɗa yana kallon la66ansa burin shi ya motsa su don yayi magana.

Ƙiri ƙiri danish yana neman ya zautar da prime minister, zuciyarshi a jagule yace"nayi maka uziri tun da ba ka jima da farkawa ba, may be har yanzu baka gama dawowa normal ba, a hakan ma na samu kwanciyar hankali, ganin ka da nakeyi ba karamin faranta raina yayi ba" ya fada yana ɗan murmushi sama sama.

"Nasan kana jin yunwa bari nayi magana akawo mana abinci" wayarsa ya zaro daga aljihunsa har time din yana lura da kallon da danish ke jefa mashi har ya fara jin shakkar ko dai ifritan dake jikinsa ne suka motsa, dauriya ce kawai irin ta Hateem

"Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya faɗa tare da miƙe ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya miƙa ma Hateem wayar, Cike da zumuɗi ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi

Har saida gabanshi ya ɗan faɗi ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka damƙi waya.

da sauri ya dago suka haɗa ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske.

Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya.

"Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba.

Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne.

Bugu uku Chief yayi picking call din

"Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"?

"Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun ɗazu yaƙi yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"?

muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar.

Da buɗar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki.

"Babu, Mu kaɗaine"!

"Uncle ka sanya sojoji su yi maku ƙawanya saboda yaron ba shi ɗaya bane, bana so asamu matsala"

"In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar

Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais.

"Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka ɗauka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ƙara haƙuri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran.

Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ruƙe da faffaɗan faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu buƙaci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci.

Ya ɗanyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba.

Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu faɗo ƙasa.

"Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"?

Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfiɗar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi.

ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message.

_I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_

Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata"

Tuni ƙamshin soye soyen da aka kawo masu ya buɗe hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba.

Farantin farko yana dauke da banƙararrun kaji anyi masu jar suya sai maiƙo sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, ɗayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun haɗo masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu buƙata......

'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman haɗiyar yawu.

Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us.

Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,.

Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya ɗan buɗe kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya haɗiye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya ɗebo sakwarar ya miƙa mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba...

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya faɗo masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane.

Buɗe baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su...

Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne ɗauke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna...

Bayan sun gama da plate din sakwarar, Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna.

Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan coconut milk da fresh juice.
Chapter 31 · 0% Book details