← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 238

Sashe 164

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaki iya tuna tayaya akai kuka tsinci kanku a gidan kurkukun ƙaddara?" Girgiza kai ta yi har lokacin bata raba jikinta daga na khala ba.

"Bazan iya tuna komai ba, ɗan uwana kadai na sani, pls ki taimaka min in gan shi..." Shiru tsohuwa khala ta yi saboda tasan me zai biyo baya in har ta faɗa mata cewa baya a cikin kurkukun, cos ta ga sunan shi cikin list na escaped prisoners, ta lura da yadda take mugun son shi in har ta faɗa mata, zuciyarta zata karaya ne kuma zata ga kamar ya manta da ita ne shiyasa ya tafi ya barta batare da ya taimaki rayuwarta ba"

Ɗagowa tayi da kanta, "kinyi shiru baki bani amsa ba, bana so na rasa ɗan uwana, nasan yana cikin wahala kuma yana nemana, pls ki ɗauko shi ya dawo nan mu rayu atare"

Dafa kafadarta khala tayi, "Zan iya jefa rayuwarmu da tashi cikin haɗari, abunda yasa nake 6oyenki saboda a yanzu haka dattijuwar da ta kusa kashe ki, nemanki take ruwa ajallo, amma in har Allah yayi mana tsawancin kwana gaba na yi maki alƙawarin zan hadaki da ɗan uwanki..."

cikin karyayyar murya ta ce, "ya mutu ko"? Girgiza kai tsohuwa khala ta yi, "A'a yana raye, "

"Ta ya kika san yana a raye"?

"Zan nuna maki"

Ɗaga mata kai ta yi alamar toh, saukowa suka yi daga kan gadon, ta ɗauki sandar ta, ta nufi gurin furannin dake a ɗakin, Gabriella tana a biye da bayanta, da sandar ta nuna mata fure kore shar da shi a cikin wata tukunyar shi mai kyan gaske.

"Ɗan uwanki yana a cikin ƙoshin lafiya, kin gan shi nan" aruɗe ta dubi khala, "tayaya hakan zai yiwu! Mutun ya zama fure??"

Dariya khala tayi, "It's a magic trick kema idan naso sai in mayar dake fure, Ko kina da ja ne?" Ta faɗa da zolaya, da sauri ta girgiza kai,

Zuƙunnawa tayi a gaban furen ta ƙura ido tana kallon shi, cikin sanyin murya ta furta sunan shi abun mamaki sai ta ga furen ya motsa ganyayyakinsa kamar iska ta kaɗa shi.

Murmushi ta saki,"Da gaske kaine?" again ya ƙara motsa ganyen shi, wani daɗine ya lullu6eta har ta buɗe baki zata ƙara magana kwatsam ba zato ba tsammani taji kamar an jeho mata wuƙa a kirjin ta,

dafe shi ta yi da hannun ta, radadi ya hana ta motsa, nan take ta fara yin aman jini,

Hankalin Khala kwata kwata baya akanta batasan meke faruwa da ita ba, saboda tayi zurfi acikin tunanin ta, sai kokari Gabriella take ta ruƙo rigarta amman ta kasa saboda kermar da yatsunta ke yi....🥺

__________________________________✍️

*BENAZIR💔*

Suna a zaune kan darduma su biyu ita da Zeenatu, sun haɗa baki suna karatun kur'ani da suka buɗe akan qur'an stand

Wayar tace ta fara ringing, bayan takai aya ta dakata da yin karatun ta miƙe da sauri ta nufi wayar dake ajiye saman gadonta

"Aunty Benazir, Azeezaty ne?" Zeenat ta tambaya tana kallon ta

Bata ba ta amsa ba, har saida ta dauki wayar, ta dubi sunan me kiranta, tayi mamakin ganin sunan Uncle ya bayyana yau wata rana Alhaji musa ya kira ta, a ranta ta furta Allah yasa alkhairi ne.

Ɗaga kiran ta yi ta kara wayar a kunnanta, tana kokarin yi mashi sallama ya katse ta da cewa, "Ki same ni a garden yanzu" amsa mashi ta yi da toh.

Aje wayar tayi gaban mirror, ta juya suka haɗa ido da Zeenatu ta ƙura mata ido tana kallon ta.

"Daddynki ne ya kira ni, ki cigaba da yin karatun yanzu zan dawo" tace toh"

Bayan fitar Benazir, cike da zumuɗi ta miƙe, ta ɗauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura.

Lokacin da Benazir ta ƙaraso Garden ɗin tunkan ta ƙarasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi.

bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!"

Yana Jin muryarta da sauri ya ɗago ya kalle ta, zumbur ya miƙe tare da ambaton sunan ta "Benazir!"

Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba..

Gaba ɗaya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruɗe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta.

Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce,"

Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi.
Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi.

"Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faɗa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ruƙo hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare.

Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buɗe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka Ƙurama juna ido kamar yau suka fara haɗuwa, sunyi kewar junan su sosai.

"Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?"

Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan shaƙuwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita..

"Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba?

"Ka manta wayata tana a hannunka?"

"Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ƙasar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?"

Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ƙasa, tasan bata kyauta mashi ba..

"Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ƙaunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta.

Da ƙyar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ƙureta jikin murfin motar .

Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin haɗe bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi.

"Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi haƙuri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka kaɗa nan da nan suka fara yin ja...

"Kin haɗu da mijin naki?"

Ɗaga mashi kai ta yi alamar eh,

Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce ƙarara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita..

"Tayaya akai ka gano inda nake?"

Da ƙyar ya furta, "Uncle ɗinki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan.

A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..."

ƙiris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke faɗi mata, tayi mamakin zurfin cikin shi...

Ruƙo hannayenta ya yi acikin nashi.

"Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da ƙaunarki, shiyasa koda kika faɗamin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki faɗa ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar ƙasar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika faɗamin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima ƙaruwa...."

dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya haɗa komai da mace zata buƙata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban ƴarta.

Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina saƙon ya sake ni?"

Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta ɗan ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata...
Chapter 164 · 0% Book details