← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 238

Sashe 2

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baka jin sautin komai a falon tamkar babu mutane acikinsa, alhalin nan kuwa Suna zaune kowa Ya hakimce abun sa, tsabar miskilanci ne Yasa basa iya buɗe baki su tanka ma Junan su, Kowannan su da abunda Ya ɗauke mashi hankali, fitowa Dr jazz yayi daga bedroom dinsa ya kimtsa kanshi cikin shadda launin blue sky abunka ga farar fata ta ƙara fiddo mashi da hasken shi, ga wani daddaɗan ƙamshin turarensa dake fesowa, Ya gyara sumar kanshi hannun shi ɗaya ruƙe da key din motarsa, wani irin annurin farin cikine akan kyakkyawar fuskarshi ga dukkan alamu akwai wani abu daya faranta mashi rai.

kafin Ya ƙarasa cikin falon, Idanunsa suka hango ma sa Matasan Samarin Family din dake zaune saman sofas Har sai da gabanshi Ya faɗi da idanunsa suka yi mashi tozali da su, Baisan da zuwansu ba, aranshi ya ayyana to fa ashe yau muna da manyan baƙi a gidan na mu ba, meyasa Ibad bai faɗa min sunzo gidan nan ba? Ya ƙarasa zancen zucin nashi cike da jin fagabar tunkararsu, Ya kasa motsa ƙafafuwanshi Ya tsaya atsaye kamar wanda aka yi mashi Iyaka da shiga falon, ɗaya bayan ɗaya ya soma bin su da kallo, Zaki Yana a azaune saman 2 seater Yayin da Apple Laptop dinsa ke akan Table din gabansa, Gaba ɗaya ya tattara hankalin shi akanta yayin da yake operating dinta atsanake, Short ne a jikin shi tare da Denim shirt tabi shape dinsa, Kau da idanunsa yai daga kan Zaki Ya mayar da su kan Wani Matashin saurayi fari Sol, fatarshi ko ƙwarzane babu, Ga wata nannaɗaɗɗiyar sumar kai dark brown, kai daga ganinsa wani shege ne mai ji da naira, Allah yayi shi da kyau mai jan Hankali, Jallabiya ce a jikin shi launin grey, ta zauna mashi sosai, bakowa bane wannan face Captain YASEER ɗan gidan His Excellency Abdul Razak da Her Excellency Muhibbat shuwa arab ne kamannin shi sak dana su Chief Owais, banbancin su launin fatane dana Ido, hannun shi ruƙe da Expensive phone dinsa da yake daddanawa da zira ziran yatsun hannunsa, yayin da Justice Nadeem ɗan gidan His excellency Deen Yake a kishingide kan doguwar Sofa, Ya zagayo da hannun shi ɗaya saman forehead dinsa, idanunsa suna a lumshe tamkar mai yin bacci.

Ziyad ne kaɗai yake a zaune saman lallausan Carpet din dake a shimfiɗe tsakiyar Sofa set din falon, faffaɗan farantin da aka kawo masu fresh fruit acikinsa ya tasa a gaba yana shan kayan marmari, duk acikin su Ziyad yafi su sauƙin kai kasancewarshi ɗan jarida da son labari, A yanzu haka da yake a zaune cikinsu A takure yake jin kanshi sunƙi sakar mashi fuska su yi fira kowa Ya kama harkar gabanshi shiyasa ya sauko kan carpet yaci gaba da shan kayan marmari.

Ƙamshin turarensu Ya gauraye Falon, Jazz dake kallon su ba ƙaramin burge shi su ke yi ba, ba tun yau ba Yana son Yaga jikokin Baba Obie sun haɗu suna sada zumunci aranshi sai yaji inama ace shima Jikan Baba obie ne da Allah ne kaɗai Yasan irin Farin cikin da zaiyi a duniyar nan.

Ganin basu lura da shigowarshi falon bane yasa shi yin saurin tafiya cikin sanɗa Ya nufi ƙofa Ya fuce daga ciki Yana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri Ya nufi Harabar Ajiye motocinsu, Ya buɗe motarshi Ya shiga daga Ciki, tare dayi mata key, zuciyarshi acike fal da tunaninta, fatan shi Allah yasa wannan karan ta kula shi.

Yana driving fuskarshi dauke da annurin farin ciki, A haka Ya nufi Gidan baba obie.

Ganin shirun nasu bamai ƙarewa bane, Yasa shi miƙewa, Ya nufi Zaki Ya sanya hannu ya ɗauke laptop din da yake dannawa, Ya juya Ya nufi Captain Yaseer Ya kar6e wayarshi, kafin Ya tunkari justice Nadeem Ya sanya hannu Ya kamo Hancinshi Yaja Shi da karfi har sai da Justice Nadeem Ya buɗe idanunshi dake dauke da bacci Fuskarshi adaure yake kallon Ziyad.

Harara Ziyad Ya watsa masu Ranshi a6ace yace"wai meke damunku ne? Kullum muka haɗu kamar wasu kurame babu mai magana kowa ya kama harkar gabansa? Haka ake zumunci? Ni banga amfanin kirana wurin nan donmu haɗu ba.... " gaba ɗaya sun ɗaura idanunsu kan fuskarshi babu alamun zasu tanka mashi.

Guntun tsoki Yaja"kun wani zuba mun idanu kuna kallona wato ni ga shashasha"

Yamutsa fuska Zaki yayi tare da miƙa mashi hannu yace"Bani laptop dina ziyad"

"Ta ƙarfi ce zoka kwata" A faɗace Ya faɗa Yana haɗe mashi fuska.

Murmushi gefen fuska Zaki Ya sakar mashi.

"Meye damuwarka"? Ya tambaya yana faman lumshe idanunsa.

"Damuwata shine ku bani aron hankalin ku muyi fira kan abunda ya shafi rayuwarmu, daga gobe fa shikenan kowannanku zai koma inda Yake rayuwarsa, yawanci ba akasar nan kuke zaune ba why ba zamu kula juna yadda ya dace ba? Bamu da tabbacin ko zamu sake haduwa da junanmu"

Yanayin yadda yayi masu maganar Ya ta6a zuciyoyinsu,

In a calm voice Zaki Ya furta"In sha Allah zamu sake haɗuwa, Yanzu dai ka yi haƙuri, Ka zauna mu yi fira"

Ta6e baki Ziyad yayi, kafin Ya koma Ya zauna, Batare daya miƙa masu Kayansu daya kar6a ba.

"Bro, Ni bansan ta yadda zan fara firar bane, ko zaka taimaka mana da abun da zamu tattauna akai"? Captain ne Ya faɗa Tamkar baison furta maganar, justice Nadeem dake a kishingiɗe tuni Ya gyara zama saman Sofa Yana duban su

"Me zai hana Mu yi magana dangane da matayen da muke da burin aure"? Acewar ziyad.

kallon Harara Captain Ya watsa mashi"mu yi magana kan abu mai mahimmanci, Idan ba haka ba zan ja baki na nayi shiru"!

"Aure shi yafi komai mahimmanci domin kuwa Sunna ce mai karfi ta Manzon Allah SAW, Allah Ya bamu komai da zamu buƙata, Kowannanmu Yana da aikin yi, Aure shi ya rage mana yakamata ku yi tunani yanzu fa lokaci ne da zamu more rayuwarmu, mu ma yi aure mu hayayyafa kamar yadda Iyayen mu suka yi.... " Ziyad ne ya kora masu jawabi.

"Look, Ni aure baya a gabana yanzu, har yau banga macen data kwanta min arai na ba, tun lokacin dana rasa wadda nake da burin aure naji matan ma sun fitarmin araina"

Justice Nadeem dake kallon Captain Ya saki murmushi tare da cewa"Ai ba ita kadai bace mace a family dinmu ba, Kai ma kaso ka wahalar da kanka, Ai ni tun lokacin dana fahimci macace mai izza da ji da kai, na sanyama zuciyata salama, saboda bana son macen da namiji bai isa yayi iko da ita ba, ba zata yi dadin zaman aure ba, kwara wadda zaka Iya juyawa son ranka ba wadda zaka dinga jin fargaban tunkararta ba"

Ziyad yace"ka faɗi gaskiya mutumina, ita fa gaba ɗaya namiji ma baya agabanta, bata da burin yin aure, kai ma mai yaja maka yin dakon soyayyarta? Bayan Ga matasan ƴan mata nan masu jini a jika a family namu.... " kafin Ziyad ya ƙare maganar, Zaki yai gyaran murya tare da cewa"wai kuna Nufin Nazli"? Ɗaga mashi gira Nadeem yai, matashin murmushi ya saki kafin yace"Kuna nufin bakusan alaƙar dake a tsakaninta da chief Owais namu ba"? Atare suka haɗa baki wurin furta meke nan"?

Jim ya ɗanyi kafin Ya furta"Uncle Hateem, Ya riga daya mallaka mashi ita, bata da wani miji daya wuce shi a duniyar nan, tun kafin tazo duniya, wannan alƙawarine dake atsakanin Uncle sharafudeen da uncle Hateem, zasu haɗa auran ƴa'ƴansu... " da mamaki suke kallon shi

Ziyad yace"amma ni banta6a ganin alamun suna kula junansu da sunan soyayya ba, Ko ranar Birthday din grandfa da suka haɗu ko kallo ba su wa junansu ba"

"Dama taya za'ai su kula juna?bayan kowannansu Yana ji da kanshi daga ita har shi Owais din, duk abunda take taƙama da shi shima Yana da shi, gaskiya Uncle sharafudeen da Hateem basu yi tunani mai kyau ba, bayan sanin cewa Izza A jinin su take, tayaya Nazli zata yi mashi biyayya amatsayin matarshi? Justice Nadeem ne yayi maganar.

Captain da ke sauraransa fuskarshi babu annuri babu walwala ya furta"da ace nasan da zancen nan da tuntuni na cireta araina, dama ni ba Iyawa zanyi da ita ba, owais din shi yafi dacewa da ita, suje can su ƙarata," Ya faɗa tare da jingine kanshi jikin Sofa.

Shiru suka yi na ɗan wani lokaci, babu wanda Ya furta magana sai daga bisani Justice nadeem Ya furta"Zaki Ina budurwarka ta Canada Kyakkyawar balarabiyar nan"

Da zolaya ya faɗa yana duban shi.

Kallo ya jefa mashi mai kama da harara kafin Ya furta"ta koma gidan su"

Zaro ido justice Nadeem yayi"me? Kana nufin tabar gidanka"

Ɗaga mashi gira yai alamar eh,

"But why"?

Bai cika son tada maganarta ba, saboda hakan Yana fama mashi raunin dake a zuciyarshi.

Cikin sanyin murya ya furta"bansan meyasa ba, rana ɗaya ta haukace min ta soma kokarin juya min ba, badan naso ba nabarta ta dawo Nigeria"

Justice Yace"banji dadi ba, me zai hana ka nemi gidansu inyaso saika gabatar da kanka wurin Iyayenta"?

Murmushin takaicin Zaki yayi"tana da aure har da ƴarta, ban ta6a fada maka bane"

Jin wannan maganar Yasa Captain ware manyan idanunshi, hatta Ziyad dake sauraransu saida Ya zaro ido da alamun mamakin kalaman Zaki

A ruɗe justice Nadeem ya maimaita maganarshi"tana da aure har da ƴa? Amma ta zauna a gidanka tsawon shekaru tamkar ma'aurata? Kafin Ya ƙare maganar Captain Yace"tayaya hakan zai yiwu? Nima fa nasan Matar duk lokacin da zanje canada a gidan ka nake taras da ita, nayi tsammanin Ƴar aikin ka ce, shiyasa ban ta6a kawo ma raina wani abu ba,"

Girgiza kai Zaki yayi"ba ƴar aikina bace, Taimakon ta nayi, na ruƙe ta agidana saboda ta nuna min bata da kowa bayan mun fara shaƙuwa take bani labarinta, Hankalina Ya tashi jin cewa tana da aure, amma agidana mijinta ya tura mata da sakon saki, ganin hakan yasa muka cigaba da yin rayuwarmu, naso ta amince min in aure ta saboda bani da burin daya wuce na mallake ta, nasan tana sona sai dai tafi ƙaunar takomama mijinta saboda ƴarta da tabar mashi"

Gaba ɗaya sun lura da canzawarshi, hakan Ya ƙara tabbatar masu da irin kaunar da yake yi mata.
Chapter 2 · 0% Book details