← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 238

Sashe 67

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa dattijuwar tayi fuskarta babu fara'a ta sanya ƙafa ta naushi cikin gabriela tsabar rashin imani duk da ta sumar da ita hakan bai mata ba...

Fucewa tayi daga toilet din, ta ba giant umarnin ya dauko gabriellah, yan uwanta na kallo ya fito da ita zindir babu kaya ya ratayata kan kafadarsa suka fice daga dakin, kamar jira suke su tafi gaba daya suka rushe da kuka mai cin rai, haƙiƙa sunji zafin abunda Ya faru da gabriela saboda suna sonta, tana taimakon rayuwarsu wurin kwantar masu da hankali idan damuwa ta addabe su sai gashi yau sun gaza taimakonta sunaji suna gani anci zarafinta an wulakanta rayuwarta.

Allah kadai Yasan Ina zasu kaita? Zata rayu ko ta mutu?

________________________Gabriel💔

A firgice Ya farka daga bacci, hannunsa dafe da saitin zuciyarsa dake harbawa da karfi da karfi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da gumi.

La66ansa na kerma ya soma ambaton inna lillahi wa inna ilaihirraji'un.

zuciyarsa ce batay masa dadi, kuma yana ji aransa wani mugun abunne ya faru da yar uwarsa dake acan gidan kurkukun ƙaddara, saukowa yai daga kan gadon su, yakai hannu ya kunna switch din dakin haske ya gauraya ko'ina, idanunsa sun cika da kwalla, gaba daya ya rasa meke masa daɗi.

A hankali yake yin tafiya kamar wanda aka zarewa laka sam babu karsashi a jikinsa, toilet ya shiga bayan ya fito ya nufi closet dinsu ya canza kayan jikinsa da jallabiya, kafin ya tsaya kan darduma ya fara jera nafilfili saboda yai mata addu'a.

Bayan ya kammala jiki asanyaye ya ɗaga hannayensa sama ya fara addu'o'i hawaye na wanke fuskarsa

Shesshekar kukansa ce ta farkar da naufal, tunkafin ya bude idanunsa kunnansa suka soma jiyo muryar sajeed Yana fadin"Ya Allah kada ka bari acutar min da ita, Ya Allah ka kare min ita daga sharrin duk wani abun cutarwa...

Da wata irin kasala naufal ya sauko daga kan gadon yaje gefen prayer mat din Ya zuƙunna Yana dubansa.

"Sajeed meke damunka ne naga kana kuka"?

Idanunsa jawur ya kalle sa"Naufal bana jin dadin zuciyata, ina ji araina wani abu Yana faru da gabriela, kwata kwata banyi bacci mai dadi ba"

Dafa kafadarsa naufal yai cikin kulawa da nuna tausayawa yace"meyasa baka ta da ni munyi sallar atare ba"?

"Bana so na takura maka" girgiza kai naufal yayi"babu takura, nima yar uwata ce sajeed, zan iya hana idona bacci don muyi mata addu'a"

Kallonsa kawai yai ba tare daya ce masa wani abu ba.

"bro ba ka tunanin Danish zai Iya taimaka mana? Da alamun ruɗu sajeed ya furta"bangane me kake nufi ba"

Naufal yace"ina nufin me zai hana mu nemi taimakonsa akan ya ɗauko mana yar uwarmu, tun da yana da ƙarfin da zai iya yin hakan"

"tayaya zai iya zuwa gidan kurkukun ƙaddara Ya taimake ta? ni bazan Iya tunkararsa da maganar nan ba, saboda bana so ya sake shan wahala, Za su Iya cutar da shi idan Yaje......." Ya faɗa Yana faman matse kwalla, kafin wani Ya kuma furta kalma sautin motsin buɗe kofar dakin su Yaja hankulansu ga duban door room din, kusan a tare suka zabura suka mike tsaye suna kallon shi babu wanda Yayi zaton shi ne, saboda bai ta6a shigowa bedroom din su ba, watakil Yana ɗan zagaye gidanne Ya jiyo sautin muryoyin su shiyasa ya shigo dakin na su

Har suna baki wurin gaishe da shi cikin girmamawa.

Bai amsa masu gaisuwar ta su ba, gaba daya hankalinsa na akan fuskar sajeed, farar jallabiya ce a jikinsa ta kamasa.

"Meke faru ne"? Ya jefa masu tambayar, da sauri naufal Ya nuna sajeed da yatsa"shi ne ke kuka"

takawa yayi a hankali Ya karasa gaban sajeed yakai hannu ya dafa kafadarsa

"I'm sorry nayi maku la6e, ba hali na ba ne, na fito ina zagaye gidanne sai najiyo voices ɗinku kuna magana, bakomaine Yaja hankalina ba, face sautin kukan ka, fadamin meke damun ka" da wata irin sanyayyar murya mai haɗe da kasalar bacci ya furta maganar

Sajeed bai 6oye masa komai ba, dangane da Sister dinsa, ba zato ba tsammani yaji chief Yai huggin dinsa da hannu biyu kamar kaninsa, tuni yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa kamar an yaye mashi damuwar shi, a hankali chief ya daura hannu daya kan bayan sajeed Yana ɗan bubbuga masa bayan cikin sigar lallashi muryarsa kasa kasa kamar tameyin raɗa ya furta"ka cigaba da yi mata addu'a, Allah Yana atare da su, kuma Yana sane da duk wani hali da suke a ciki, in sha Allah komai yazo karshe, In har sister dinka nada tsawaicin kwana zata rayu ne kamar yadda kuma kuka rayu bayan wahalar da kuka fuskanta....." daɗaɗan kalamai chief ya cigaba da furta masa, ko a mafarki ba su ta6a tunanin chief zai shigo bedroom dinsu balle har ya rungumi ɗaya daga cikin su, sun kara ganin darajarsa da kimarsa a idanun su, sunyi mamakin hakan sosai, mutumin ya ƙara siye zuciyoyin su.

Sai da ya tabbatar Ya kwantar masa da hankali kafin ya raba jikin su daga na juna.

Fuskarsa da damuwa ya furta"time din sallar asuba yayi, ina jiranku a falo ku shirya mu tafi masallaci, ku sanar da sauran yan uwanku maza" amsa masa sukai da toh, gently ya juya har Ya kusa fita daga dakin muryar sajeed ta ratsa kunnansa.

"Nagode chief, kamar yadda ka faranta min rai, kaima Allah Ya faranta maka naka"

Ba tare daya juyo ya kallesa ba Ya furta"Ameen, but ku kira ni da sunana Owais, zanfi jin daɗi"

Murmushi suka saki atare suka hada baki wurin furta"Yaya Owais" jinjina kansa yai kafin Yasakai Ya fuce daga dakin, wayyo Allah dadi kamar jira suke Ya fita, da sauri Sajeed Ya ruko gaban rigarsa ya soma shinshina kamshin turaren chief.

"Naufal shinshina kaji" shinshinawa naufal yayi sai dadi suke ji

"Wallahi baka ji dadi ba daya rungune ni, sai naji kamar an wanke min damuwana, mutumin Yana da mutunci sosai komai nasa yana burgeni....." santin chief suka cigaba dayi.

Kafin daga bisani naufal yace"yana fa jiranmu zamu tafi masallaci, mu yi sauri mu shirya"

💘UNAISAH ANGEL💋

kiran sallar asubahin farko, wayarta ta fara ringing kamar zata fasa kunnuwan su, cikin duhu ta farka tare da laluba hannu ta damƙo wayar dake ajiye kan nightstand ta ɗago da ita ba tare da ta duba sunan mai kiranta ba tai picking

"Unaisah! Ina kika shiga inata jaraba kiran layinki bana samu" wata irin zabura tayi aɗan ruɗe saboda bata gane wacece ba.

"Nasan baki gane mai magana ba, Aunty pretty ce"

Ajiyar zuciya ta sauke muryarta da kasalar bacci ta ce "Yanzu na gane, Ina kwana kin tashi lafiya"

"Ki yi hakuri na katse maki baccin ki, na damu da son jin awani hali kike a ciki kwana biyu ba ki neme ni ba"

Muryarta adidashe Tace"ba komai, nima kina araina"

"Ban yarda ba, meyasa baki kara kirana ba? Ni ay fushi ma nake dake, kin manta dani" muryar benazir da alamun 6aci rai tay maganar.

"Ba haka bane wallahi ban manta dake ba, nayi rashin lafiya ne amma yanzu naji sauƙi, wayar ma bata a hannu na sai jiya na kar6e ta"

Tana jiyo sautin muryar aunty pretty tana zabga salati gaba daya ta ruɗe jin bata da lafiya

"Inna lillahi! Yanzu ya jikin naki? da sauki?

Murmushi unaisah tayi jin yadda ta ruɗe"ay na fada maki da sauƙi yanzu"

Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar ta

"Har naji sanyi araina, Allah ya ƙara maki lafiya, wallahi baki ji yadda naji ba saboda na damu dake, dan Allah Idan nan abuja kuke da zama, ki bani dama inzo gidan ku, dama yau nakeson fita anguwa"

waro idanu unaisah tayi da sauri tace"a'a ni ban ma ta6a zuwa abuja ba, a kano mu ke"

"Allah sarki, kinyi min nisa, in sha Allah wata rana zan kawo maku ziyara"

"Nagode da kulawarki a gare ni" sun jima suna waya kafin daga bisani su ka yi sallama, ta ajiye wayar tana faman sauke ajiyar zuciya, ita kanta tana son haɗuwa da matar sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, na farko batasan wacece ita ba? Idan har dagaske number da take amfani da ita ta sajeed ce me zai biyo baya?

da wannan tunanin ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken dakin nasu

a hankali ta sauke idonta kan Deeja dake bacci tana jan minshari kwatsam taga ta fara mirginawa zata faɗo ƙasa daga kan gado, cikin zafin nama ta yi hanzarin tallabota a hankali ta wurga ta kan mattress din

Murmushi ta dan saki kafin ta juya ta shiga toilet, har yau tana mamakin jinin daya dauke mata tun bayan da ta sha bakar wahala bai dawo ba, har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taji ance alamun girma ne ga mace, kuma idan tanayi boobies ɗin ta zasu kara cukowa sannan hips dinta zai ƙara faɗaɗa komai ma na jikinta zai canza ta zama cikakkiyar budurwa, a gaban sink ta tsaya tana lalubar wurin don taga idan za'a samu ko da alamunsa ne sai dai bata ga komai ba...." fuskarta ayamutse ta kalli mirror kamar zata fasa ihu haka take ji, ita da take son ta zama house wife idan har bata fara wadannan abubuwan ba ina ita ina iya zama matar aure? ta faɗa aranta, kafin ta sa hannu ta zame wuyan rigar baccin ta, ta soma leƙen kirjin ta, murmushi tayi ganin sun ƙara girma ba laifi, wani irin dadi ne Ya lullu6e ta, har yau bata bari danish ya gan su ba, saboda kullum in zata sanya kaya sai ta ɗaure su tamau don karsu fito.

jujjuyawa ta yi agaban mirror din tana kallon qugunta, ni dai na rasa me angel take ma zumudi, da alama batasan meye ake azaman auran ba.

Gaba ɗaya matasan gidan sun tafi masallaci, bayan sun kammala sallah shiekh imam ya zaunar da su don suyi karatun da yake biya masu kullum.
Chapter 67 · 0% Book details