← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 238

Sashe 191

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batool ta tausaya mata sosai, ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su...

Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buɗe ta.

Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buɗe kofar daga can inda yake.

Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa ɗauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su.

Suna shiga ɗakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faɗo kan floor, cikin sauri ta dauƙi hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta"

Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruɗu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta.

Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer"

"To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"?

Da mamaki Unaisah ta ƙara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba.

"Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar..

"Zan faɗa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba..

Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya ɗaure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ruƙe fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call.

"Kin tabbata shine"?

"Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.."

lamarin ya ɗaure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta.

Kafin wani ya ƙara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne.

Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faɗa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke"

kafin Ummi ta shigo ɗakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu.

Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta.

Morning🌄

Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi.

"Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faɗa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faɗa, sai uban kasusuwan wuya..

In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.."

Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi..

"Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ƙare maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haɗiye shi.

"Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daɗi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faɗa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba,

Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"?

Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su.

A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba ɗaya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy.

"Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaɗan.

mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su.

Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru"

Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira.

zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buɗo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta ɗauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya.

Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta..

"Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya.

"I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita"

On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School.

basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?"

yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma yaƙi kulani ay da tuni mun yi maki ƙani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari.

tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki"

murmushin yaƙe tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faɗa maki yana da au..." bata ƙare maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call ɗin tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata ɗauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuɗi, kafin ta ƙarasa Ummi da Batool suka bi bayanta da ɗan gudun su.
Chapter 191 · 0% Book details